ALHAMDU lillah! Kamar dai yadda mu ka ba ku labarin fitacciyar mawaƙiya Hajiya Magajiya Ɗambatta a shekarar da ta gabata na irin halin da ta ke ciki na ƙunci da ya sa ta har sai ta yi bara ta ke gudanar da rayuwa, wanda fitaccen ɗan jaridar nan Jaafar Jaafar ya nemo har inda ta ke a garin Makoɗa a cikin Jihar Kano.
Jaafar ya yi magana da ita tun a wancan lokacin bayan ya samu ganin ta, inda bayan dawowar sa daga wurin zabiyar, ya sanar wa da duniya halin da ta ke ciki, a nan take su ka aza gidauniyar nema mata taimako.

Jama’a da dama sun taimaka da kuɗi zunzurutu har N5,194,000, da waɗannan kuɗaɗe ne tun a lokacin aka yi alƙawarin saya mata fili a gina mata gida da kuma sauran ɗawainiyar yau da kullum.
An kashe N4,465,150, inda kuɗin da su ka yi saura N728,850.

Cikin yardar Allah wannan alƙawari ya cika, domin kuwa a jiya Talata, 2 ga Disamba, 2020 Jaafar ya sanar da batun kammala gidan da sauran abubuwan da aka yi da kuɗaɗen cikin harshen Turanci. Ga fassarar sanarwar tasa:
“A ƙarshe mun kammala aikin sayen fili da gina sabon gida da kayan ɗaki ga shahararriyar mawaƙiya Magajiya Ɗambatta.
“Tun fara shiga tsakani a Disambar bara, (2019) mun cika alƙawarin ciyar da ita, da sayen sutura, da ba ta alawus domin hana ta bara.

“Abin farin ciki ne cewa tun daga lokacin ta daina bara kuma ‘yar jagorar jikar ta yanzu ta shiga makaranta.
“Mun riga mun zaunar da Magajiya Ɗambatta a sabon gidan ta a inda ta ke so, Makoɗa. Sabon gidan ya na ɗan jifa ne kawai daga gidan dangin ta. Haka nan an haɗa gidan mai ɗakuna 3 da wutar lantarki, ruwa mai ɗauke da bututu da kuma matsugunar WC. Daga wata kusurwa ta farfajiyar, an shirya rumfar dabbobi da ta dace.
“A madadin mambobin tawagar: Musa Sufi, Ibrahim Sanyi-Sanyi, Dr Kabir Ɗambatta, ina matuƙar gode wa duk waɗanda su ka bada gudunmawa saboda wannan aikin.
“Wani babban abin lura shi ne jajircewar Musa Sufi, wanda ke yin zirga-zirga a kai a kai daga Kano zuwa Makoɗa don ganin halin da ta ke ciki da kuma cigaban aikin.

“Godiya ta musamman ga Malam Hassan Gama na ‘friends of the community’, ƙungiyoyi masu zaman kan su na riƙe kuɗin kuma su na bada bayani mai kyau game da su.
“Babbar godiyar mu kuma ga Arc. Bilyamin Kaila Umar wanda ya tsara kuma ya kula da aikin kyauta.
“Hajiya Magajiya dai ta tare a sabon gidan ta. Allah ya saka wa dukkan mutanen da su ka bada gudunmawa har wannan abu ya tabbata da gidan Aljanna.”
