• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Magajiya Ɗambatta ta tare a sabon gidan ta

by DAGA ABBA MUHAMMAD
December 2, 2020
in Labarai
0
Hajiya Magajiya Ɗambatta da 'yar jagorar ta a gaban tsohon gidan ta da kuma sabon gidan ta

Hajiya Magajiya Ɗambatta da 'yar jagorar ta a gaban tsohon gidan ta da kuma sabon gidan ta

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
ALHAMDU lillah! Kamar dai yadda mu ka ba ku labarin fitacciyar mawaƙiya Hajiya Magajiya Ɗambatta a shekarar da ta gabata na irin halin da ta ke ciki na ƙunci da ya sa ta har sai ta yi bara ta ke gudanar da rayuwa, wanda fitaccen ɗan jaridar nan Jaafar Jaafar ya nemo har inda ta ke a garin Makoɗa a cikin Jihar Kano.
 
Jaafar ya yi magana da ita tun a wancan lokacin bayan ya samu ganin ta, inda bayan dawowar sa daga wurin zabiyar, ya sanar wa da duniya halin da ta ke ciki, a nan take su ka aza gidauniyar nema mata taimako.
 
An buga dagin Arewa da sunan Magajiya Ɗambatta a jikin sabon gidan ta
Jama’a da dama sun taimaka da kuɗi zunzurutu har N5,194,000, da waɗannan kuɗaɗe ne tun a lokacin aka yi alƙawarin saya mata fili a gina mata gida da kuma sauran ɗawainiyar yau da kullum. 
 
An kashe N4,465,150, inda kuɗin da su ka yi saura N728,850.
 
Magajiya Ɗambatta a cikin ɗakin ta na sabon gida
 
Cikin yardar Allah wannan alƙawari ya cika, domin kuwa a jiya Talata, 2 ga Disamba, 2020 Jaafar ya sanar da batun kammala gidan da sauran abubuwan da aka yi da kuɗaɗen cikin harshen Turanci. Ga fassarar sanarwar tasa:
 
“A ƙarshe mun kammala aikin sayen fili da gina sabon gida da kayan ɗaki ga shahararriyar mawaƙiya Magajiya Ɗambatta.
 
“Tun fara shiga tsakani a  Disambar bara, (2019) mun cika alƙawarin ciyar da ita, da sayen sutura, da ba ta alawus domin hana ta bara.
 
Gwanin ban-sha’awa! Gidan Magajiya Ɗambatta sai ka ce gidan wani hakimi!
“Abin farin ciki ne cewa tun daga lokacin ta daina bara kuma ‘yar jagorar jikar ta yanzu ta shiga makaranta.
“Mun riga mun zaunar da Magajiya Ɗambatta a sabon gidan ta a inda ta ke so, Makoɗa. Sabon gidan ya na ɗan jifa ne kawai daga gidan dangin ta. Haka nan an haɗa gidan mai ɗakuna 3 da wutar lantarki, ruwa mai ɗauke da bututu da kuma matsugunar  WC. Daga wata kusurwa ta farfajiyar, an shirya rumfar dabbobi da ta dace.
 
“A madadin mambobin tawagar: Musa Sufi, Ibrahim Sanyi-Sanyi, Dr Kabir Ɗambatta, ina matuƙar gode wa duk waɗanda su ka bada gudunmawa saboda wannan aikin. 
 
“Wani babban abin lura shi ne jajircewar Musa Sufi, wanda ke yin zirga-zirga a kai a kai daga Kano zuwa Makoɗa don ganin halin da ta ke ciki da kuma cigaban aikin.
 
Magajiya Ɗambatta a cikin sabon gidan ta
 
“Godiya ta musamman ga Malam Hassan Gama na ‘friends of the community’, ƙungiyoyi masu zaman kan su na riƙe kuɗin kuma su na bada bayani mai kyau game da su.
 
“Babbar godiyar mu kuma ga Arc. Bilyamin Kaila Umar wanda ya tsara kuma ya kula da aikin kyauta.
 
“Hajiya Magajiya dai ta tare a sabon gidan ta. Allah ya saka wa dukkan mutanen da su ka bada gudunmawa har wannan abu ya tabbata da gidan Aljanna.”
 
Rumfar kiwon dabbobi a gidan Magajiya Ɗambatta

Loading

Previous Post

Bayan neman afuwa, kotu ta sakar wa Naziru Sarkin Waƙa mara

Next Post

Shugabancin INEC: Kungiyar ‘Tinubu Vanguard’ ta ce sake naɗa Yakubu daidai ne

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Farfesa Mahmud Yakubu

Shugabancin INEC: Kungiyar 'Tinubu Vanguard' ta ce sake naɗa Yakubu daidai ne

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!