BAYAN ya shafe tsawon lokaci yana jinya sakamakon karayar ƙafa da ya samu, jarumi kuma furodusa Malam Ɗan’azumi Baba (‘Kamaye’) ya fara samun sauƙi, inda a yanzu ya fara iya tafiya da taimakon sandar ƙarfe.
Kamar yadda mujallar Fim ta ba ku labari, kimanin watanni biyu da suka gabata jarumin ya yi haɗari a lokacin da yake tafiya a kan mashin ɗin sa, hatsarin da ya yi sanadin samun karaya a ƙafar sa, musamman a wajen mahaɗar gwiwa.
Sai dai a yanzu halin da yake ciki ya fara sauyawa zuwa samun sauƙi, inda jarumin ya fara iya taka ƙafa tare da dogaro da sandar ƙarfe.
Da mujallar Fim ta tuntuɓe shi domin jin halin da yake ciki, sai Malam Ɗan’azumi Baba ya ce: “Alhamdulillah, ina godiya ga Allah da Yake ba ni sauƙi. A yanzu har na fara miƙewa ina takawa da ƙarfe.
“Da man rayuwa haka take; ɗan’adam ba ya wuce ƙaddarar sa. Ina fatan Allah Ya sa hakan ya zama mafi alheri a gare ni da rayuwa ta baki ɗaya.”

Haka nan, Kamaye ya bayyana godiyar sa ga dukkan mutanen da suka ziyarce shi domin duba halin da yake ciki, da waɗanda suka aika masa da saƙonnin jaje da fatan samun sauƙi.
Ya kuma gode wa dukkan masoyan sa da suka nuna damuwa tare da kasancewa tare da shi a lokacin da yake fuskantar wannan jarabawa.
![]()







