A JIYA Asabar, 27 ga Fabrairu, 2021 aka ɗaura auren matashin mawaƙin Kannywood, Mas’ud Idris, da kyakkyawar amaryar sa A’isha Abubakar.
An ɗaura auren da misalin ƙarfe 2:30 na rana a masallacin cikin layin gidan su amaryar da ke Bakin Boda, Unguwar Shanu, Kaduna, a bisa sadaki N70,000.
Mawaƙan da su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Ibrahim Al-Imash, Ɗanladiyo Mai Atamfa, Nafi’u Bigi, Auwalu Hannun Dama, Babangida Birniwa da Aliyu Janan.

Da ya ke angon soja ne, abokan sa sojoji sun haɗa wasan ƙwallon ƙafa a barikin sojoji da ke Jaji, Kaduna.
A yau Lahadi, 28 ga Fabrairu, aka ɗauki amaryar daga Kaduna zuwa Jihar Filato, daga can kuma za su wuce Jihar Abiya inda angon ya ke aikin sojan shi.
Allah ya su zaman lafiya, amin.








