* Labarin ƙarya ne, inji ƙanwar jarumar
AN shiga wani zazzafan ruɗani a kan wani labari da ya ɓulla a soshiyal midiya gaf da magaribar yau cewa wai fitacciyar jarumar Kannywood Ummi Zee-Zee ta rasu.
Sai dai ƙanwar jarumar, Hasina Ɗan-Chaina, wadda ke aure a Jos, ta ƙaryata labarin wanda ake ci gaba da yaɗawa a soshiyal midiya.
Bayan dukkan turka-turkar da aka yi kwanakin baya da Zee-Zee na maganar kashe kan ta da kuma maganar damfarar ta da ta ce an yi ne a yau kuma aka samu wata sanarwa a shafin ta na Instagram cewa wai Allah ya yi mata rasuwa.
Kamar yadda sanarwar ta nuna, wata ƙawar ta mai suna Khairat ta ɗora hoton Ummi, sannan ta yi rubutu a ƙasan hoton Zee-Zee, ta ce: “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Allah ya yi wa Ummi Ibrahim Zeezee rasuwa da misalin ƙarfe biyu na rana yau a nan unguwar Sarki da ke Kaduna State a gidan ƙawar ta. A taya mu da addu’a, Allah ya jiƙan ta da rahama, amin, daga ƙawar ta Khairat.”
Abun mamaki shi ne babu wanda zai iya tura saƙo a shafin wani sai mai shafin domin shi ne mai ‘password’ ɗin.
Ganin wannan aiken ya sa wakilin mujallar Fim ya yi ta ƙoƙarin kiran wayar jarumar, amma ba a ɗaga ba.
Duk da cewa wadda ta wallafa sanarwar ba ta faɗi a wane ɓangare ne Unguwar Sarkin aka yi rasuwar, wakilin mujallar da ke Kaduna ya garzaya ya shiga unguwar, ya zaga ko zai samu labarin an yi rasuwa a unguwar, amma bai ga wata alama ta rasuwa ba. Har tambayar mutane ya yi a unguwar, amma babu wanda ya ji labarin an yi rasuwa a duk unguwar.

Abin mamaki ne a ce jarumar fim kamar Zee-Zee ta rasu a cikin unguwa amma wai babu wanda ya ji labarin rasuwar ta a cikin unguwar. Kuma ba ma a gidan ta ba ko gidan ‘yan’uwan ta, a’a, a gidan ƙawar ta, abin dubawa ne.
Yayin da ta ƙaryata labarin, ƙanwar jarumar, Hasina Ɗan-China, ta yi martani a ƙasan rubutun inda ta ce, “Subhanallah! Allah ya kyauta. Wacece Khairat da ni ban san ta ba? Ku daina irin wannan, ‘is very very wrong’ ɗaga wa Musulmi hankali.”
Ta ƙara da cewa, “Ta rasu shi ne duk ‘family’ ta ba wanda ya sani uwar rubutu ko in ki ka bari ta mutu a gidan ki kuwa ke ma ki na cikin wani hali, ‘u should better stop doing all this’.”
Hasina ta ƙara da cewa, “Ku na wasa da Allah da ikon Sa, ya yi kyau. In ke ƙawar kirki ce ki ba ta shawaran kirki.”
Sai kuma ta ce, “Drop me ur contact or IG handle ni, ban san ki ba ana cikin watan azumi ku na wannan abun, wat is the meaning of this pls’?”
To amma akwai alamar ita kan ta Hasina ba ta iya kiran Zee-Zee su yi maganar.
Bayan wannan aiken rubutun a shafin jarumar, mutane sun yi caa a soshiyal midiya su na faɗin albarkacin bakin su.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan labarin, mutum sama da 300 sun tofa albarkacin bakin su game da lamarin. Kuma dukkan masu magana a ƙasan saƙon su na yi wa Khairat ɗin Allah wadai da irin wannan abu da ta yi.
Wasu kuma na cewa Zee-Zee ta haukace da gaske, yayin da wasu ke cewa ita ce da kan ta ta tura saƙon domin tada ƙura da jan hankali kawai.
Akwai kuma waɗanda su ka yarda ta mutu ɗin, su na faɗin Allah ya jiƙan ta.
Ba dai yau ba ne aka fara ƙaga wa ɗan fim mutuwa. Kusan kowane fitaccen jarumi an taɓa yi masa ƙaryar ya mutu. Kuma mutane daga wajen industirin ne ke ƙago labarin ƙanzon kurege su na yaɗawa.
Sai dai bambanci da wannan shi ne ɗan fim ba zai tura saƙo da kan shi a shafin sa ba ya ce ya mutu. Don haka ko dai da gaske Zee-Zee ce ta tura saƙon, ko wani ne ta yi amfani da wayar ta ya tura saƙon.
Gaskiyar za ta bayyana nan gaba kaɗan.









Muhammadtukur866@email.com
Babu abunda malaman nigeria zasu ce miki ga me da kisan kan ki da kika so yi sbd ba jin maganar su kuke ba. So nawa ne? Su ke muku wa’azi amman bakuji!