FITACCIYAR jarumar masana’antar finafinan kudancin ƙasar nan, wato Nollywood, Tonto Dikeh, ta bayyana cewa gidauniyar ta za ta ciyar da yara ‘ya’yan Musulmi guda 2,000 har tsawon kwana biyu saboda bikin Sallah.
Jarumar, wadda kuma mai taimakon jama’a ce, ta bayyana wannan labarin mai daɗi ne a wani rubutu da ta yi a Instagram a yau Juma’a.
Wannan ya nuna cewa ita mai tallafa wa dukkan yara ne a ƙasar nan, ba ‘ya’yan Musulmi kaɗai ba.
Mujallar Fim ta fassara abin da jarumar ta rubuta kamar haka: “Ni da kai na zan tafi in ciyar da yara ‘ya’yan Musulmi su 2,000 a yau da kuma gobe don taya su murnar Sallah.
“Manyan ayyuka guda huɗu sun mamaye gidauniyar mu domin mu na kasafin kuɗi ga wasu gidauniyoyin daban-daban da kuma kayan aiki da su ka kamata don ciyar da yaran Musulmi su 2,000.

“Ya zuwa yanzu dai mun samu isa ga yara 1,800 kuma in ka na Abuja kuma ka na da wasu al’ummar Musulmi da ka ke son ka ciyar, to don Allah ka tuntuɓe mu.”
Ta kuma tura hotunan da ta ɗauka tare da wasu daga cikin yaran da za ta ciyar.
Tonto Dikeh ta miƙa godiya ga al’ummar garuruwan Fatakwal da Legas da Kano da kuma ƙasar Kamaru da sauran jama’a saboda ƙwarin gwiwar da su ke ba ta da kuma saka hannu da su ka yi a cikin ayyukan ta.
Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) ta ruwaito cewa ‘yar wasan ta na gudanar da ‘Tonto Dikeh Foundation’, wadda gidauniya ce mai zaman kan ta.
An kafa gidauniyar a cikin shekarar 2000 da niyyar inganta rayuwar mata, ‘yan mata, matasa da ƙananan yara marasa galihu a Afrika, ba tare da nuna bambancin siyasa, addini ko ƙabilanci ba.
Jarumar ‘yar shekara 36 ta fito a ɗimbin finafinai, kamar su ‘Dirty Secret’, kuma bayan ta cimma gagarumar nasara a fagen wasan fim, sai ta shiga harkar waƙa.
Ta fito a wani bidiyon waƙa na kamfanin Amaco Investments, ita da Patience Ozokwor.
Dikeh ta fara waƙa ne da wata mai taken ‘Hi and “Itz Ova’.
A cikin Yuni, 2014, mawaƙin nan ɗan Nijeriya mai suna D’banj ya ɗauke ta a ƙarƙashin kamfanin sa mai suna DB Records, amma ta bar shi a cikin Maris 2015.
A cikin 2018 ta samu kwangilar yin talla a Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane (NAPTIP) a kan yekuwar hana irin wannan safarar.

![]()







