• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamna Ganduje ya yabi dattawan Kannywood kan aikin su na faɗakarwa

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
June 3, 2021
in Labarai
0
Gwamna Ganduje ya yabi dattawan Kannywood kan aikin su na faɗakarwa
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNA Abdullahi Umar Ganduje ya yaba wa dattawan masana’antar shirya finafinai ta Kannywood bisa ƙoƙarin su na wayar wa da al’umma kai kan muhimmancin biyan haraji.

Ya faɗi hakan ne a lokacin da dattawan su ka kai masa ziyara a ƙarƙashin ƙungiyar su ta Kannywood Foundation a daren jiya Laraba, 2 ga Yuni, 2021 a fadar gwamnatin jihar da ke Kano.

A lokacin wannan ziyara ta musamman, ƙungiyar ta gabatar wa da gwamnan wani gajeren fim da ta shirya mai suna ‘Da Ruwan Ciki…’

Fim ɗin na nuna yadda ya kamata mutane su riƙa biyan haraji ga gwamnati da yadda za su iya sanin irin ayyukan da gwamnati ke yi da ƙuɗaɗen da su ke biya, musamman ayyukan da su ka shafe su kai-tsaye.

Da ya ke bayyana dalilin shirya fim ɗin a lokacin zaman, babban furodusa Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama ya ce, “An yi wannan fim ne domin a ci gaba da yin ayyuka na wayar wa da mutane kai kan abubuwan da su ka shafi haraji, da yadda jama’a ya kamata su bi wajen biyan haƙƙoƙin da ke kan su na haraji, da kuma harkokin tsaro. 

“Ya kamata a ce mutane sun ɗauki gaɓar gyara, wanda kuma gwamnati ita kaɗai ba za ta iya ba sai da haɗin kan jama’a.”

A nasa jawabin ne ɓangaren Dakta Ganduje ya yaba tare da bayyana jin daɗin sa bisa wannan hoɓɓasa da dattawan na Kannywood su ka yi na nusar da al’umma kan muhimmancin biyan haraji.

Hagu zuwa dama: Shu’aibu Yawale, Ɗan’azimi Baba, Gwamna Ganduje, Ahmad Sarari da Hamisu Iyan-Tama

Kazalika ya ce wannan aiki ya na matsayin wani tsani da zai taimaka wa jama’a su fahimci yadda ake gudanar da kuɗaɗen da gwamnati ta ke karɓa na haraji a faɗin jihar.

Bugu da ƙari, ya hori dattawan da su ƙara ƙaimi wajen shirya irin waɗannan finafinai da za su hasko wa jama’a wani abu da ya shige musu duhu game da gwamnati.

Ya bada misali da cewa, “Kamata ya yi ana shirya irin waɗannan finafinan, musamman ga masu babura masu ƙafa uku, wato Adaidaita Sahu, don sanin muhimmancin titunan da ake musu su na hawa domin yin kasuwanci ta hanyar bada kuɗin haraji.

Ya ce, “A kuma maida hankali wajen faɗakarwa kan tsaro, duk da ba za a iya nunawa ba amma ya kamata mutane su gane cewa yayin da su ke kwance su na barci, jami’an tsaro fa ba barci su ke ba.”

A ƙarshen jawabin sa, gwamnan ya yaba da sadaukarwar da ƙungiyar ta yi domin shirya wannan fim da kuma mallaka shi ga gwamnatin jihar kyauta ba tare da ta biya su ba.

Bayan kammala kallon fim ɗin, su ma kwamishinonin jihar da dama sun yaba da yadda aka tsara fim ɗin tare da bada shawarwari a wuraren da aka samu kurakurai a cikin sa.

Dattawan Kannywood da su ka halarci zaman nuna fim ɗin sun haɗa da Shu’aibu Yawale, Auwalu Isma’il Marshal, Ɗan’azimi Baba Ceɗiyar ‘Yangurasa (Kamaye), Hamisu Iyan-Tama, Dakta Ahmad Sarari, Bala Anas Babinlata, Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, Ali Sambo, Balarabe Tela da kuma Khalid Musa.

Gwamna da mataimakin sa da wasu kwamishinoni da maziyartan
Daga hagu: Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, da Kwamishinan Al’amuran Addini na Jihar Kano, Dakta Muhammad Tahir Adamu (Baba Impossible), da Alh. Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama

Loading

Tags: Dr Abdullahi Umar Gandujehamisu iyantamaKannywoodlabaran kannywood
Previous Post

Gwamna Ganduje ya ba darakta Ishaq muƙami

Next Post

Hukumar Tace Finafinai ce ke daƙile Kannywood – Salisu Officer

Related Posts

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta
Labarai

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta

June 23, 2025
Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima

June 22, 2025
Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau
Labarai

Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau

June 22, 2025
Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji

June 22, 2025
Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano
Labarai

Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano

June 20, 2025
Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza
Labarai

Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza

June 20, 2025
Next Post
Hukumar Tace Finafinai ce ke daƙile Kannywood – Salisu Officer

Hukumar Tace Finafinai ce ke daƙile Kannywood - Salisu Officer

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!