• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamna Ganduje ya ba darakta Ishaq muƙami

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
June 2, 2021
in Labarai
0
Gwamna Ganduje ya ba darakta Ishaq muƙami
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNAN Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya naɗa fitaccen darakta, jarumi kuma daga cikin dattawan Kannywood, Ishaq Sidi Ishaq, matsayin babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin fasaha.

A Turance, muƙamin shi ne ‘Senior Special Assistant, Creative Industries’. 

Mujallar Fim ta ruwaito cewa harkokin fasaha sun haɗa da shirya finafinai, waƙoƙi, rubuce-rubuce da sauran nau’o’i na ƙirƙira.

An bada sanarwar naɗin a cikin takarda mai ɗauke da sa hannun Bilkisu Shehu Maimota a madadin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano.

A takardar, mai ɗauke da kwanan wata 27 ga Mayu, 2021, an sanar da Ishaq cewa an naɗa shi muƙamin ne bisa cancanta, sadaukarwa, ƙwazo, son ƙasar sa da kuma nuna goyon baya da ya yi.

Gwamnatin ta ce, ”Mu na fatan za ka yi amfani da ƙwarewar ka wurin gudanar da wannan aiki da aka ɗora maka domin ciyar da fannin ƙirƙire-ƙirƙire a faɗin Kano.”

‘Yan’uwa da abokan arziki tare da Ishaq Sidi Ishaq (na 6 daga dama) a ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano

Har wa yau ta taya shi murna tare da addu’ar Allah ya taya shi riƙo.

A ƙarshe, takardar ta bayyana ranar 20 ga Mayu, 2021 a matsayin ranar da muƙamin ya fara aiki.

‘Yan’uwa da abokan arziki sun raka Ishaq zuwa ofishin sakataren gwamnati a jiya inda ya karɓi takardar naɗin nasa.

‘Yan fim da dama sun taya shi murna tare da yi masa fatan alheri a wannan sabon muƙami.

Da yawa su na sa ran wannan naɗin zai kawo wa Kannywood gagarumin cigaba domin Ishaq, wanda ƙwararren ɗan fim ne, zai yi duk iya mai yiwuwa wajen ganin ya jawo hankalin gwamnati domin tallafa wa masana’antar.

A saƙon godiya da ya tura wa jama’a a yau, Ishaq Sidi Ishaq ya ce: “Salam ‘yan’uwa, ina ƙara godiya da murnar da ku ke taya ni da ita, da addu’o’in ku. Allah ya saka muku da alkhairi, ameen. Na gode ƙwarai da gaske. Sai a ci gaba da sa mu a addu’a. Allah ya ba mu ikon kwatanta gaskiya tare da yin abubuwan da al’umma za su amfana. Na gode sosai.”

Naɗin na Ishaq irin wanda Gwamna Nasiru El-Rufa’i na Jihar Kaduna ya yi wa Hajiya Halima Idris ne.

Fitaccen jarumi Umar Gombe ya na taya Ishaq murnar naɗin sa yayin da su ke riƙe da takardar naɗin, a jiya

Loading

Tags: Creative industriesDr Abdullahi Umar GandujeIshaq Sidi IshaqKannywood
Previous Post

Tijjani Muhammad Musa ya zama shugaban marubutan Kano

Next Post

Gwamna Ganduje ya yabi dattawan Kannywood kan aikin su na faɗakarwa

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Gwamna Ganduje ya yabi dattawan Kannywood kan aikin su na faɗakarwa

Gwamna Ganduje ya yabi dattawan Kannywood kan aikin su na faɗakarwa

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!