• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, May 15, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

‘Yan fim sun yi taro kan hana nuno shan sigari a finafinan Nijeriya

by DAGA ABBA MUHAMMAD
June 18, 2021
in Labarai
0
‘Yan fim sun yi taro kan hana nuno shan sigari a finafinan Nijeriya
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MASU harkar shirya fim a Nijeriya sun yi wani babban taro jiya a Legas kan yadda za a daina nuno shan taba ko tallar ta a finafinan da ake yi a ƙasar.

Wata ƙungiya mai suna KAPA ce ta shirya taron, wanda aka yi a wani otal mai suna De Rembrandt da ke unguwar Ikeja, kuma manyan masu shirya finafinai daga sassan Nijeriya daban-daban ne su ka halarta.

Taken taron dai shi ne “Stakeholders’ Summit on Smoking in Movies”.

Daga masana’antar shirya finafinai ta Kannywood, mutum biyu su ka samu halarta, wato Hajiya Fatima Ibrahim Lamaj da Alhaji Maikuɗi Cashman; a yayin da Lamaj ta wakilci shugabar Ƙungiyar Matan Kannywood (K-WAN), Hajiya Hauwa A. Bello, wadda ita Lamaj ɗin ce mataimakiyar ta, shi kuma Cashman ya wakilci shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai Ta Nijeriya (MOPPAN), Dakta Ahmad Sarari.

Da mujallar Fim ta tambayi Lamaj yadda taron ya gudana, sai ta ce, ”Wannan taro an yi shi ne kan shaye-shayen taba sigari da kuma illar da ita kan ta tabar ta ke yi wa masu shan ta. 

“Magana ta gaskiya, taron ya yi armashi sosai, saboda an nuna mana yadda taba sigari ke da illa ga ɗan’adam, kuma da yadda bai kamata mu na sanya ana shan taba a fim ba, domin duk fim ɗin da aka saka taba sigari a ciki Hukumar Tace Finafinai ba za ta tace shi ba.”

Hajiya Fatima Lamaj ta na gabatar da jawabi kan matsayar K-WAN a taron hana nuno shan taba cikin fim a Legas jiya

Ta ce ita kan ta ta nuna wa mahalartan taron wani fim da ta shirya kan illar shaye-shaye ga al’umma, wanda ya taɓo har da ita sigarin. Ta ce a fim ɗin an nuna yadda saboda shaye-shaye har wani mutum ya yi wa ƙaramar yarinya ‘yar makaranta fyaɗe. 

Lamaj ta ce mahalartan taron sun ce tunda shaye-shayen ne ya yi jagoranci ga aikata haka ɗin za a iya kauda kai, “amma kuma sai na sa ‘Cigaratte Is Dangerous To The Health’ kamar yadda ake rubutawa a finafinan ƙasashen waje.”

Ta bayyana cewa an sanar da su cewa duk mashiryin fim wanda ya karɓi tallar taba, zai biya diyyar naira miliyan biyar.

A cewar ta, “Ire-iren waɗannan batutuwa duk su aka tattauna a kai a wurin taron domin su ne maƙasudin shirya taron.”

Babbar furodusar, wadda kuma ita ce shugabar Ƙungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna, ta faɗa wa mujallar Fim cewa, “Ina kira ga mutanen mu da su bi dokokin gwamnati, don ba ka isa ka yaƙi gwamnati ba. Saboda akwai waɗansu da su ka yi magana a wurin a kan cewa ai ba gwamnati ke ba su kuɗi ba, sai aka ce masu, ‘Gwamnati ba ita ke ba ku kuɗi ku yi fim ba, amma gwamnati na da dama ta ce in ka yi fim da ka saɓa wa dokokin ta za ta iya cin tarar ka. Don haka dole ne mutum ya bi dokoki da ƙa’idojin gwamnati.’ 

“Don haka ina jan hankalin mutanen mu da su bi umarnin gwamnati; in aka ce ka yi, ka yi, in aka ce ka bari, ka bari.”

Fatima Lamaj da Maikuɗi Cashman tare da wasu daga cikin jiga-jigan masu shirya fim a Nijeriya a wurin taron
Fatima Lamaj da Maikuɗi Cashman tare da ɗaya daga cikin shugabannin Nollywood a wurin taron

Loading

Previous Post

Jam’iyyu 18 ke fafutikar neman kujerar gwamnan Anambra – INEC

Next Post

An ɗaura auren jaruma Naja’atu Muhammad da ɗan ƙwallo Abdullahi Shehu

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
An ɗaura auren jaruma Naja’atu Muhammad da ɗan ƙwallo Abdullahi Shehu

An ɗaura auren jaruma Naja'atu Muhammad da ɗan ƙwallo Abdullahi Shehu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!