• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Furucin ƙazafi: Matan Kannywood za su maka Naziru Ahmad a kotu

by DAGA IRO MAMNAN
February 14, 2022
in Labarai
0
Naziru Ahmad (Sarkin Waƙa)

Naziru Ahmad (Sarkin Waƙa)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƘUNGIYAR Matan Kannywood (Kannywood Women Association of Nigeria, K-WAN) ta ba fitaccen mawaƙi Naziru M. Ahmad wa’adin kwana uku da ya janye ƙazafin da ya yi wa mata ‘yan fim ko kuma su yi ƙarar sa a kotun Musulunci.

Wa’adin ya fara aiki ne daga yau Litinin, 14 ga Fabrairu, 2022.

Shugabar ƙungiyar, Hauwa A. Bello (Edita), ita ce ta bada wa’adin a cikin wata takardar sanarwa da ta aika wa mujallar Fim.

Naziru M. Ahmad, wanda ake wa laƙabi da Sarkin Waƙa, ya wallafa wani bidiyo a soshiyal midiya inda ya yi iƙirarin cewa ba a sanya jarumai mata a fim a masana’antar Kannywood sai sun bada kan su an yi zina da su.

Ya yi maganar ne domin bada martani ga waɗanda su ka yi fatali da iƙirarin da dattijuwar ‘yar wasa Hajiya Ladin Cima (Tambaya) ta yi inda ta ce ba a taɓa biyan ta sama da N5,000 ba idan ta yi fim.

Naziru ya zaɓe jarumai Ali Nuhu da Falalu Ɗorayi musamman a martanin sa, ya ce babu tsoron Allah a zuciyar ‘yan fim.

Hauwa A. Bello, Shugabar K-WAN

Maganar tasa ta janyo surutai sosai, kuma ta zama makami ga mutane masu adawa da harkar fim a yayin da kuma ta hayaƙa wasu ‘yan fim ɗin.

A takardar da ta rattaba wa hannu a yau, Hauwa Edita ta ce, “Duba da abin da ya faru wanda Naziru M. Ahmad ya yi wasu kalamai na cin zarafi ga mata masu sana’ar fim, mu na kira a gare shi da ya janye kalaman sa cikin kwana uku daga yau, in kuwa bai yi haka ba za mu kai shi kotun Musulunci bisa tuhumar ya yi mana ƙazafi.”

Tun da fari, kwana kaɗan kafin wannan sabon matakin da ƙungiyar ta ɗauka, sai da Hauwa Edita ta yi Allah-wadai da kalamin mawaƙin a wata sanarwa da ta raba wa manema labarai.

A sanarwar, ta ce, “A madadin shigabanci na ƙungiyar mata ta ‘Kannywood Women Association’ mu na tir da Allah-wadai da wasu kalamai da Naziru Sarkin Waƙa ya yi a kafar sadarwa kan wasu munanan halaye da ya danganta mata ‘yan fim da su, wanda wannan ƙazafi ne kuma ɓata suna ne da taɓa martabar wasu daga cikin ‘yan wannan masana’anta.

“Mu na kira ga Naziru ya nemi gafara don ya shiga haƙƙin mu.

“Allah ya ci gaba da kare wannan masana’anta. Allah ya kare mutuncin mu da martabar mu, amin.”

Loading

Tags: Ali NuhuFalalu DorayiHausa actressesHauwa A. BelloHauwa EditaK-WANKannywoodKannywood Women Associationkazafikotun MusulunciLadin Cima TambayaNaziru Ahmad Sarkin Waka
Previous Post

Za mu kawo sabon tsari mai kyau a harkar fim a Kaduna – Zaharaddin Sani Owner

Next Post

MOPPAN ta sulhunta matan Kannywood da Naziru Ahmad

Related Posts

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama
Labarai

Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama

August 2, 2026
Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11
Labarai

Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

August 1, 2026
Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano
Labarai

Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano

July 15, 2026
Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu
Labarai

Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu

July 14, 2026
A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti
Labarai

A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti

July 9, 2026
Next Post
Naziru M. Ahmad (a dama) a wajen taron a daren yau

MOPPAN ta sulhunta matan Kannywood da Naziru Ahmad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!