• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Abin da ya hana Kannywood jagorancin harkar fim a duniya

by DAGA ZAHARADDEEN IBRAHIM KALLAH
January 6, 2022
in Tsokaci
0
Tijjani Asase kan kujera tare da jarumai da ma'aikata a wurin ɗaukar fim ɗin sa mai dogon zango na 'A Duniya'

Tijjani Asase kan kujera tare da jarumai da ma'aikata a wurin ɗaukar fim ɗin sa mai dogon zango na 'A Duniya'

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

KO shakka babu, finafinan Hausa sun taka rawa babba a tattalin arziƙin Nijeriya tare da samar wa matasa aikin yi. Duk da ɗimbin shekaru da mutanen Arewacin Nijeriya su ka kwashe wajen kallon finafinan Indiya, zuwan finafinan Hausa ya sauya masu alƙibla, inda su ka koma kallon finafinan Hausa. 

Marubuta da su ka samar da masana’antar sun yi wannan nasara ba da manyan kwamarori ko kayan aiki ba, illa da labarai masu tasiri da jan hankali.

Wannan zai nuna mana cewa da masana’antar Kannywood ta yi abin da ya kamata, zuwa yanzu babu tantama za ta iya jagorancin duniyar finafinai a faɗin duniya.

Wannan ba abin mamaki ba ne idan an yi la’akari da matsayin Afirka a duniya, musamman ta ɓangaren al’adu da yawan al’umma, wanda jigo ne na tattalin arziƙin duniya. 

Ali Nuhu da sauran jarumai a fostar fim ɗin sa mai dogon zango na ‘Alaqa’

Ƙasar Hausa na da ɗimbin labarai na ban-mamaki da duniya ba ta taɓa jin su ba. Waɗannan labarai, idan da masu ruwa da tsaki a Kannywood za su farga da su, su kuma san yadda za su amfana da su, da ba wannan maganar ake ba. 

Amma me ya sa masana’antar ta gaza fahimtar yadda za ta tafi da zamani a wajen cin wannan gajiya?

A yanzu haka idan ana maganar duniyar nishaɗi, wato ‘Entertainment Industry’, Nijeriya na sahun gaba. Taurari da mawaƙa na sashen kudancin ƙasar sun yi nisa tare da yin mahaukatan kuɗi, baya ga shahara a duniya. 

Duk da cewa Kannywood ta girmi takwarar ta ta Nollywood, amma ta gaza fito da kan ta a duniya kamar yadda ya kamata, bare ta ci moriyar arziƙin da ya ke damfare a harkar. 

Wasu daga cikin jagororin masana’antar na sane da cewa manyan kamfanonin shirya finafinai a duniya na ƙishirwar finafinai na ban-mamaki da al’ajabi da ya jiɓanci yankin Arewa. To amma sun gaza samun haɗin kai ne, ko kuma yunƙurin tabbatar da sabuwar tafiyar ne ya fi ƙarfin tunanin su?

A ranar Asabar, 25 ga Disamba, 2021 an gabatar da wani littafi mai suna ‘Ruwan Jakara’, wanda Nasiru S. Gwangwazo ya rubuta, a cikin bikin murnar auren sa da aka yi.

HAƙiƙa, rashin haɗin kai ba ya taɓa kawo cigaba, domin a lokacin da wasu ke ƙoƙarin kawo abin da zai amfani kowa, wasu na gefe tare da lalata wannan yunƙuri

Wannan taro ya samu halartar mutane da kai-tsaye za ka kira su da masu ruwa da tsaki a harkar rubutu da finafinai. Domin taron ya samu jagorancin Farfesa Abdalla Uba Adamu, sannan akwai shugaban Ƙungiyar Marubuta ta Njeriya (ANA), reshen Jihar Kano, Tijjani M. Musa, baya ga manyan marubuta kuma jagorori a harkar fim irin su Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, da Bala Anas Babinlata da Sunusi Shehu Daneji da Dakta Ahmad Muhammad Sarari da shugaban riƙo na haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kano, Umar Gombe, sai Adamu Muhammad (Kwabon Masoyi).

Sannan akwai shugaban Ƙungiyar Marubuta ta Jihar Jigawa, Hasheem Abdallah, da Bilkisu Yusuf Ali da Al-Amin Ciroma da Aminu Saira da Kabiru Y. Anka, sai mai gabatarwa a wurin, Salihu Alkanawy, da sauran su. 

Abin da ya ja hankali na a wannan taron shi ne jawabin Malam Sanusi Daneji a kan cewa Kannywood ta rasa ‘ya’ya masu tarbiyya da biyayya, wanda hakan ya taimaka wajen kawo koma-baya a harkar. Malam Sunusi, wanda shi ne ainihin mutumin da ya raɗa wa ƙungiyar fim ɗin Hausa suna da ‘Kanywood’, ya kwatanta ‘yan Kannywood da marubuta, inda ya ce a duk rashin fahimtar marubuta ko bambancin ra’ayi ba sa yarda hakan ya kawo masu rashin ganin girman manya da biyayya. A cewar sa, rashin wannan tarbiyyar ne ya kawo rashin cigaba a masana’antar fim. 

Haƙiƙa, wannan batun nashi ya sa na tuna baya a lokacin da marubuta da ‘yan fim su ka shiga rigima da gwamnatin Kano, a lokacin da Malam Abubakar Rabo Abdulkareem ke jagorancin Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano. A wani zama da mu ka taɓa yi da mutanen hukumar, mu na fitowa mu ka tarar da ‘yan fim ana ta ja-in-ja kafin a shiga ganawar da su ma za su yi. 

Allah ya jiƙan Sani Garba SK, wanda mu ka gan shi a gefe ya yi shiru. Da mu ka matsa wurin sa mu ke tambaya, “Anya SK ba ‘faction’ a tsakanin ku?” A lokacin ya yi murmushi ya ce, “Ai a ‘fakshe’ mu ka zo.” 

Wannan ya sa ban yi tantamar abin da Malam Sunusi ya faɗa ba da na tuna wannan al’amari. Haƙiƙa, rashin haɗin kai ba ya taɓa kawo cigaba, domin a lokacin da wasu ke ƙoƙarin kawo abin da zai amfani kowa, wasu na gefe tare da lalata wannan yunƙuri. 

Ina ganin wannan taro ya zo a lokacin da ake buƙatar sa, ba don komai ba sai ganin yadda duniya ta sa gaba na sabon tsarin kasuwanci, wanda dole marubuta da ‘yan fim su yi duba ga wannan ɓangare da idon basira.

Ya kamata marubuta da masu harkar finafinai su kafa wasu kwamitoci da za su zauna don fitar da wani sabon jadawali da zai yi jagoranci tare da haska yadda ake son harkar rubutu da fim ta kasance. 

Akwai mutanen da aka san su na da ƙwarewa a harkokin kasuwancin zamani, musamman a wannan ɓangare na duniyar nishaɗi. Idan ta kama, ana iya neman masu ƙwarewa (consultants) a faɗin duniya domin su nuna yadda za a buɗe wannan ƙofa. 

Zamanantar da waɗannan harkoki na adabi da fim shi ne mafita, tunda dai kasuwar ta na nan. Idan matasa sun daina karanta littafi saboda samuwar wayoyin ‘android’, to ta yaya za a ja hankalin su su dinga karance-karance ta wayoyin su? Idan an daina cinikin kaset ko sidi a bakin Bata, ta yaya cinikin zai hau mizanin tsarin kasuwancin yanar gizo ɗari bisa ɗari kamar yadda ake yin sa a manyan ƙasashen duniya?

Jarumai a fostar shiri mai dogon zango na ‘Ana Barin Halak’ na kamfanin 2-Effects pictures

Duk waɗannan amsoshi ba za su gagara ba idan mu ka buɗe ƙwaƙwalen mu. Ta yaya ƙasashen da mu ke kallo tare da sha’awa da ilimi da hangen nesa su ka kai wannan mataki?

* Zaharaddeen Ibrahim Kallah marubuci ne cikin harshen Turanci da Hausa, kuma sgi ne tsohon shugaban Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA), reshen Jihar Kano. Ana iya samun sa ta imel: zikallah@gmail.com

Loading

Tags: ANA.Censorship in NigeriaFinafinan Indiyahausa filmsHukumar Tace FinafinaiKannywoodMalam Abubakar RaboMOPPANNasiru S. GwangwazonollywoodSunusi Shehu DanejiZaharaddeen Ibrahim Kallah
Previous Post

‘Labari Na’: Tsakanin Aminu Saira, Nafisa, Nuhu Abdullahi da Kannywood

Next Post

Alhaji Bashir Othman Tofa (1947-2022)

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida)
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Alhaji Bashir Tofa

Alhaji Bashir Othman Tofa (1947-2022)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!