• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Abin da ya sa ba mu iya hana kwararowar sabbin jarumai a Kannywood – Alhassan Kwalle

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
March 27, 2021
in Tattaunawa
0
Abin da ya sa ba mu iya hana kwararowar sabbin jarumai a Kannywood – Alhassan Kwalle
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN Ƙungiyar Jaruman Kannywood ta Nijeriya (Hausa Actors Guild of Nigeria), reshen Jihar Kano, Malam Alhassan Aliyu Kwalle, ya bayyana cewa dole ce ta sa su ke ɗaukar sababbin jarumai bayan kuwa daina ɗaukar jaruman a masana’antar shi ne mafi a’ala.

A wata hirar musamman da ya yi da mujallar Fim, shugaban, wanda kuma fitaccen jarumi ne, har ila yau ya yi kira ga jama’a masu kallon ‘yan fim a matsayin “masu faɗakarwa” da su fahimci cewa su ba faɗakarwa su ke ba, neman kuɗi su ka fito, don haka su ba malamai ba ne. Haka kuma ya yi tsokaci a kan tataɓurzar da ke wakana tsakanin ‘yan fim da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano.

Ga dai yadda hirar ta gudana:

FIM: Tun bayan shigowar shekarar 2021 ba a ji amon wannan ƙungiya da ka ke jagoranta ba, ga shi kuwa har ana kama wasu daga ‘ya‘yan ta ana gurfanar da su a kotu. Shin me ya faru ne?


ALHASSAN KWALLE: Alhamdu lillahi, kamar yadda mu ka ga shekara ta 2020 tun daga farkon ta har ƙarshen ta, ga shi har mun shiga shekara ta 2021 har ma da wasu ‘yan watanni. Babu abin da za mu ce da Allah sai godiya. Abubuwa da kuma su ka faru na jin daɗi da rashin sa a waccan shekarar da ta gabata, wannan wani abu ne wanda Allah ya kawo wanda ba yadda za a yi da shi, kuma abin da ya shafi duniya ne baki ɗaya, musamman wannan harkar ta cutar korona da ta faru wanda kuma ta kawo tsaikon abubuwa da yawa. Amma dai ko babu komai daga irin asarorin da mu ka yi da rashin ayyukan yi, to ko ba komai mu na gode wa Allah. Wato mu ‘ya‘yan ƙungiyar mu, wato jarumai, daidai gwargwado Allah bai hana su samun yadda za su yi ba domin su kan samu tallallika, su kan je gayyata zuwa wuraren taro daban-daban wanda za su je a gan su a gurin a biya su, da kuma tallallika irin na kamfanoni da makamantan su.

Wasu daga cikin mu akwai waɗanda su kan je wajen ‘yan siyasa su ba su aikin da za su amfana da iyalan su da kuma ci gaba da wayar wa da mutane kai.

A ɓangaren fim, abubuwa duk sun zama abin da su ka zama domin fim yanzu ya koma soshiyal midiya, musamman kafar nan ta YouTube; kowa ya na buɗe shafin sa kuma daidai gwargwado mutanen mu ana yin abin da ya dace. Waɗanda kuma su ke abubuwa na rashin ɗa’a, mu na ta sa ido a kan su da faɗakar da su.

FiM: A nan Jihar Kano jarumai na fama da Hukumar Tace Finafinai, musamman yadda ta ke kama su har ta kai ana kai wasu gidan yari. Wane ƙoƙari ku ke yi domin sasantawa da wannan hukuma?


ALHASSAN KWALLE: Abubuwa sun ragu sosai, domin a shekarar 2019 ƙungiya ta je Hukumar Hisbah aƙalla kusan sau talatin wajen yin belin mutanen mu da aka kama bisa kuskure, wani lokacin kuma a bisa ganganci na wasu daga cikin ‘ya’yan ƙungiyar mu. Sannan kuma wajen ‘yan sanda mun samu kyasakyasai kimanin guda arba’in duk a shekarar 2019. Amma a shekara ta 2020 mun samu kyakkyawan haɗin kai tsakanin tsohon Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, AIG Habu Sani, wato ‘Kalamu wahid’, wanda a lokacin in ka ga an kai ɗan mu kotu to ya fi ƙarfin sa ne da sauran D.P.O. na wurare da dama. Wannan dalilin ne kuma ya sa a shekarar da ta gabata ta 2020 bai fi sau shida mu ka je wajen ‘yan sanda ba. Ka ga daga arba’in aka dawo shida, an ci nasara. 

Su kuma hukumar Hisbah da na ambata a baya, wanda na ce mun je kimanin sau talatin a shekararar 2019, amma su ma da mu ka shiga shekarar 2020 bai fi sau uku mu ka je mu ka karɓo wasu mutane da aka kama ba.

A ɓangaren rigimar cikin gida kuma, tsakanin jarumai, su ma yanzu duk mun ɗinke ɓarakar saboda irin yadda mutane su ke fuskantar irin wayar masu da kan da mu ke na ba dare ba rana kuma su na ba mu haɗin kai.

A ɓangaren Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano kuwa, mu na da kyakkyawan haɗin kai da fahimtar juna domin shugaban ya na ganin mu da mutunci kuma duk abin da aka yi ya na tuntuɓar mu domin jin tamu matsayar.

FIM: A ko da yaushe ana ganin sababbin jarumai na ƙara kwararowa cikin wannan masana’anta duk da yake kasuwar fim ta ja baya. Shin ku a ƙungiyance ya ku ke da waɗannan jarumai masu ɓarkowa?


ALHASSAN KWALLE: Dangane da jarumai masu tasowa, ni sai dai in ce ina tausaya masu. Tausayin da na ke masu, na farko dai masana’antar ta cika, cikar da ya kamata a ce ma an daina ɗaukar sababbin jarumai. Amma babu yadda za mu yi saboda cikar da ta yi ayyuka sun yi ƙaranci wanda kamar mu a nan Jihar Kano a rana ɗaya a da za ka ga an fita wajen ɗaukar fim kafin zuwan cutar korona wurare kamar guda goma sha biyar a rana, kuma kowanne fim daban-daban, to amma a yanzu sai ka ga a sati bai fi ka ga an fita lokeshin uku ko huɗu ba. Ka ga kuwa abin ya ragu da yawa.

Kuma ɗiɗɗikowa da yara su ke yi saboda halin da ƙasa ta ke ciki ne; yaran da yawa sun yi karatu amma ba su da aikin yi, wasu talauci ne da halin da iyayen su su ke ciki, karatun ma ya kasa yiwuwa. Saboda haka mutane su na ganin cewa wannan wata masana’anta ce da ta ke bada sana’a mai ƙarfi, dan da nan sai a ga mutum ya sayi gida da mota, ya na ta facaka da kuɗi, ga kuma suturu mai kyau. Wannan dalilin ne ya ja hankalin matasa da yawa su ka shigo wannan masana’anta duk da cewa kowace masana’anta akwai irin tata matsalar. 

To amma duk da haka mu na haƙuri mu na karɓar su, mu na kuma nuna masu akwai kamfaninnikan mu da ya kamata su dinga zuwa, mu na koyar da su yadda ake waɗannan abubuwan. Haka zalika mu na ba su shawarwari a kan su nemi ayyukan yi. Mu na koƙarin haɗa kai da gwamnati domin ɓullo masu da sana’o’in da za su dinga yi. Ko ba komai dai yanzu yaran mu sun gane cewa harkar ba a dogara da ita ita kaɗai; za ka ga akwai waɗanda su ka rungumi sana’ar sayar da takalma, wasu shagunan saida kayan lemo su ka buɗe, wasu kuma kayan sawa. To ka ga hakan ya kan sa a sami raguwar wasu abubuwan tsakanin su.

Su ma mata mu na koya masu sana’o’in hannu da irin su ɗinkuna domin su ma su ɗan riƙe kan su kafin lokacin da fim zai samu a zo a yi. 

Don haka mu na karɓar mutane a babu yadda za mu yi ne. Domin in ka ƙi karɓar su, su na iya zuwa su faɗa mugun hannu; a maimakon mutum ya zo ya kashe wani ɗan ƙaramin kuɗi don yin rijista da ƙungiya, sai ka ga ya je ya faɗa mugun hannu, su na ta karɓar kuɗaɗe a gun su da zummar yi masu rijista. Don haka mu na jan hankali da a kula da irin waɗannan mutane.

Hatimin Ƙungiyar Jaruman Kannywood ta Nijeriya

FIM: Waɗanne nasarori da ƙalubale ne wannan ƙungiya ta samu a cikin shekarun da ta yi tun da aka kafa ta?


ALHASSAN KWALLE: Cigaban da mu ka samu a ƙungiyance a shekarar da ta gabata mun samu damar yin rijista ta CAC ta ƙasa, sannan a shekarar da mu ka yi bankwana da ita matsugunin zama na wannan ƙungiya ya tabbata, dukkanin wani kayan aiki da ake nema na zaman ofis ya tabbata, an samu; sannan wannan ƙungiyar duk wani abu da ake nema yanzu an samu. Kowanne jarumi, kama daga tsoho zuwa matasa, duk yanzu sun san cewa wurin nasu ne, su na zuwa ana haɗuwa ana zumunci ana tattaunawa kuma ana samar da ayyukan yi.

Saboda haka mu na gode wa Allah a kan wannan abu.

A ɓangaren ƙalubale kuma, mun fuskanci ƙalubale da dama, amma ina tabbatar maka da cewa ko babu komai mun yi nasara domin duk mutumin da Allah ya kawo shi wannan lokacin babu ciwo babu mutuwa, to sai ya gode wa Allah, ya kuma hari abin da Allah ya tanadar masa a gaba.

FIM: Ya alaƙar ku ta ke da sauran ƙungiyoyin cikin wannan masana’anta?


ALHASSAN KWALLE: Sai godiya, saboda mun samu fahimtar juna da su sosai wanda hakan ya sa ko da wani abu ne aka kawo masu wanda ya shafe mu, za su ce wa mutum ya garzayo gun mu, ba su ne su ke da alhakin abin ba. Mu ma kuma duk lokacin da wani al’amari ya taso wanda su ne su ke da haƙƙi, mu na ƙoƙarin tura mutum can domin samun mafita. Don haka mu ba abin da za mu ce da sauran ƙungiyoyin Kannywood sai sambarka da fatan alheri.


FIM: A ƙarshe, wane kira ka ke da shi ga ‘ya’yan ƙungiya da sauran jarumai masu tasowa? 


ALHASSAN KWALLE: Kira na ga jarumai sabbi da tsofaffi shi ne su gane cewa duk wanda zai shigo wannan masana’anta ya dai shigo da niyyar ya zo ne domin neman kuɗi. Mu ba faɗakarwa mu ke ba, sana’a mu ke; idan mutum zai zo don neman kuɗi ya zo neman kuɗi kawai. Amma kuma shi neman kuɗi ba zai sa ka zo ka lalata mana masana’anta ba. 

Kar wani mutum ya ƙara tunanin cewa mu malamai ne. Mu ba malamai ba ne, sana’a mu ke. Idan Allah ya sa mun samu kuɗi mu taimaki iyalan mu da abokan mu da sauran mutanen da su ke kusa da mu, mu kuma taimaki addinin mu. Idan Allah bai ba mu ba, wannan daga Allah ne.

Saboda haka kar a ƙara tunanin yadda manyan malaman nan su ke mu ma haka mu ke. Harkar malamai ta malamai ce, mu kawai masu nishaɗi ne da kuma neman kuɗi a kan ƙa’ida.

Alhassan Kwalle da Ali Nuhu
Alhassan Kwalle a wani fim
Tags: Alhassan KwalleArewa entertainmentFim MagazineHausa Authors Guildhausa filmsKannywoodKano State Censorship Board
Previous Post

Yadda waƙar ‘Da Ma’ ta fito da mawaƙi Namenj a duniya

Next Post

Abdu Boda ya yi auren ba-zata

Related Posts

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 
Tattaunawa

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 

March 1, 2025
Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah
Tattaunawa

Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah

November 13, 2024
Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala
Tattaunawa

Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala

August 2, 2024
Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde
Tattaunawa

Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde

March 13, 2024
Mahaifiyar Afakallahu ta kwanta dama
Tattaunawa

Afakallahu: Abin da mahaifiyar mu ta karantar da mu

March 11, 2024
Gaskiyar abin da ya faru gare ni a haɗarin da na yi – Jarumar Kannywood Maryam CTV
Tattaunawa

Gaskiyar abin da ya faru gare ni a haɗarin da na yi – Jarumar Kannywood Maryam CTV

February 14, 2024
Next Post
Abdu Boda ya yi auren ba-zata

Abdu Boda ya yi auren ba-zata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!