KARIN maganar nan da ke cewa matar mutum kabarin sa ya yi daidai da abin da ya faru ga fitaccen mawaƙi kuma jarumi Abdu Boda da Hafsat Sabi’u Sani waɗanda aka ɗaura wa aure a yau Asabar, 27 ga Maris, 2021.
Ko kaɗan Boda, wanda mazaunin Katsina ne, bai da niyyar yin aure nan da shekara goma ma, kamar yadda ya faɗa wa mujallar Fim, amma da yake aure haɓo ne sai ga shi ya angwance ba zato ba tsammani.
An dai ɗaura auren ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe a gidan su Muntari Masko da ke Layin Zana a unguwar Ƙofar Marusa, Katsina, a kan sadaki N50,000.
‘Yan Kannywood da su ka halarta sun haɗa da Abdul D. One, Hassan Danja, Ali Show, M.M. Na Manzon Allah, KB Sikko, Jamil M. Hamid Sakatare da marubuci Nura Salah. Wasu mahalartan sun zo ne daga Jamhuriyar Nijar.
Bayan kammala ɗaurin auren, an ɗunguma zuwa wajen liyafar cin abinci.
Tun shekaranjiya Alhamis an buga wasan ƙwallon ƙafa a filin wasa na Scorpion Arena da ke birnin Katsina inda aka fafata tsakanin ƙungiyoyi da dama don taya ango da amarya murna.
Jiya kuma da misalin ƙarfe 4:00 na yamma aka shirya Wasan Ƙauyawa a wurin taro na Continental Computers.
‘Yan fim da mawaƙa sun yi wa Boda kara, domin sun baje kolin su a wurin. Sun kuwa haɗa da mawaƙi KB Zango wanda ya wakilci Adam A. Zango, da Abdul D. One, da wasu, sai kuma jarumai mata da su ka haɗa da Saratu Giɗaɗo, Fati Baffa Fagge da Ummi El-Abdul (‘Duniyar Nan’).

Bayan kammala ɗaurin auren ne Boda ya faɗa wa mujallar Fim yadda aka yi har ya auri zankaɗeɗiyar sahibar tasa.
A zantawar da ya yi da wakilin mu, angon ya bayyana cewa daga raka abokin sa zuwa wajen Hafsat ne sai reshe ya juye da mujiya.
Boda ya fara labarin da godiya ga Allah ne kan wannan abin farin ciki, ya ce, “Ina godiya ga Allah da ya nuna mani wannan rana ta farin ciki, kuma wani abu da Allah ya haɗa wanda ba na ma tunanin aure yanzu, nan da shekara goma ma ba na tunanin aure amma kuma sai ga shi Allah ya kawo shi.
“Don ita yarinyar ma da farko wani aboki na ne ya ce ya na son ta. A matsayin mu na mutane sanannu ga jama’a, bayan na raka aboki na gun ta, don ko layin ma ban taɓa zuwa ba, sai ta leƙo ta gan mu kuma ta koma gida; don ni ban ma gan ta ba.
“Bayan shigar ta gida ake tambayar ta, ‘Ya ku ka yi?’ Sai ta ke cewa da dai Boda ne ya ce ya na son ta…! To, ta yadda mu ka haɗu kenan, kuma Allah ya sa da rabon zan aure ta da kuma taimakon baban ta, don shi abokin yaya na ne.

“Ana dai tambayar ta maganar aure sai ta ce ai ni ta ke so. Daga nan kuma baban nata su ka dinga waya inda ni ma aka tambaye ni ga abin da wance ta ke cewa. Sai na ce, ‘Ni da ban taɓa ganin ta ba, ban san ta ba?’ Daga nan kuma na je mu ka sasanta har abu ya tabbata.”
A ƙarshe, mawaƙin ya miƙa godiya ga mahalarta ɗaurin auren nasa, ya ce, “Zan yi amfani da wannan dama wajen miƙa saƙon godiya ga duk waɗanda su ka halarci taron ɗaurin auren da ma waɗanda ba su zo ba su ka kira ni a waya.
“Sannan ina miƙa gaisuwa ta ga furodusa Abdul Amart Maikwashewa kan wasu wakilai da ya turo mani; shi bai samu damar halarta ba. Ina godiya sosai.”
To, mu ma a mujallar Fim mu na addu’ar Allah ya ba Abdu Boda da Hafsat zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.

