• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jarumar Kannywood Hafsat Idris ta yi bikin ‘yar ta ta uku

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
March 28, 2021
in Ranar Murna
4
Jarumar Kannywood Hafsat Idris ta yi bikin ‘yar ta ta uku
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A JIYA ne tauraruwar finafinan Hausa Hafsat Idris ta aurar da ɗiyar ta ta uku a ƙarshen gagarumin bikin da aka ɗau kwanaki ana yi a birnin Kano.

Hafsat, wadda ake yi wa laƙabi da ‘Ɓarauniya’, ta aurar da Khadija Kabir ne ga wani matashi mai suna Abubakar Ibrahim Muhammad.

An ɗaura auren da misalin ƙarfe 12:00 na rana a unguwar Ɗandago cikin ƙwaryar Kano a kan sadaki N50,000.

Taron ɗaurin auren ya samu halartar ɗimbin ‘yan’uwa da abokan arziki, amma mujallar Fim ba ta ga fuskar abokan sana’ar uwar amarya a wurin ba.

To sai dai sun yi mata kara a sauran shagulgulan da aka gudanar, ciki har da liyafar cin abincin dare da aka yi a shekaranjiya Juma’a, 26 ga Maris, 2021 a wurin taro na Fabs da ke Kano.

Hafsat Idris, uwar amarya, a cikin taron bikin ‘yar ta

Ɗimbin ‘yan’uwa da abokan arziki sun halarci dinar, ciki har da ‘yan fim da mawaƙa irin su Ali Nuhu, Nazifi Asnanic, Lawan Ahmad, Hamisu Breaker Ɗorayi, Teema makamashi, Ruƙayya Dawayya, Saratu Giɗaɗo, Halima Atete, Samira Ahmad, Fatima Ali Nuhu, Ummi Rahab, Aisha Humaira, da sauran su.

Tun a yammacin ranar Alhamis aka gudanar da kamu a Ezema Events Centre, taron da shi ma ‘yan’uwa da abokan arziki da dama su ka halarta.

Amarya Khadija Kabir dai ita ce ta uku a cikin jerin ‘ya’yan Hafsat Idris guda shida waɗanda su ka haɗa da maza biyu mata huɗu.

Bikin auren ya yi armashi, an ba naira kashi, sai dai mu ce Allah ya bada zaman lafiya da ƙazantar ɗaki, amin.

Ango Abubakar Ibrahim Muhammad (a tsakiya sanye da babbar riga) a wurin ɗaurin auren sa
Hafsat Idris a lokacin bikin Khadija

Previous Post

Abdu Boda ya yi auren ba-zata

Next Post

An sace wa jarumin ‘Labari Na’ mota, kwana 1 da sayen ta

Related Posts

Marubuci kuma furodusa Zubairu Musa Balannaji zai yi aure a ranar Lahadi
Ranar Murna

Marubuci kuma furodusa Zubairu Musa Balannaji zai yi aure a ranar Lahadi

December 26, 2025
Darakta Aminu Saira ya yi walimar buɗe gidan da babu mai irin shi a Kannywood 
Ranar Murna

Darakta Aminu Saira ya yi walimar buɗe gidan da babu mai irin shi a Kannywood 

December 20, 2025
Sarkin Daura ya naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa
Ranar Murna

Sarkin Daura ya naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa

December 14, 2025
Darakta a Kannywood, Balarabe Murtala Baharu zai yi bikin auren da ɗan sa ranar Asabar
Ranar Murna

Darakta a Kannywood, Balarabe Murtala Baharu zai yi bikin auren da ɗan sa ranar Asabar

December 3, 2025
Shekaru 10 da aure: Ba wanda ya taɓa jin kan mu tsakani na da mata ta – Adam M. Adam
Ranar Murna

Shekaru 10 da aure: Ba wanda ya taɓa jin kan mu tsakani na da mata ta – Adam M. Adam

December 3, 2025
Aure: Ahmad Yariman Tiga ya zama cikakken mutum
Ranar Murna

Aure: Ahmad Yariman Tiga ya zama cikakken mutum

November 28, 2025
Next Post
An sace wa jarumin ‘Labari Na’ mota, kwana 1 da sayen ta

An sace wa jarumin 'Labari Na' mota, kwana 1 da sayen ta

Comments 4

  1. Bunyamin Hafsa says:
    5 years ago

    I love Hafsa Idris

  2. Muhammadu yakubu says:
    5 years ago

    Allah ya bada zaman lapiya lalle hafsat idiris uwace

  3. Ismail Mai hasashen Yan'matan kaduna da kewaye says:
    5 years ago

    Lallle Masha Allah Amma Bata tsufa

  4. Pingback: HAFSAT IDRIS BATA AURI IYALAN SANI ABACHA BA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!