MAWAƘIN yabon Annabi (s.a.w.), Malam Bashir Ɗandago, ya bayyana cewa rashin haɗin kan da ke tsakanin sha’irai shi ne ummulhaba’isin koma-bayan da harkar tasu ta ke ciki.
Malam Bashir, wanda da shi aka fara harkar bege kusan shekara arba’in da ta gabata, ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar sa da mujallar Fim kan matsalolin da ke faruwa a cikin harkar sha’irai, musamman ma a yanzu da jama’a su ka yi yawa a cikin ta.
A cewar sa: “Tun a farko aka samar da wannan matsalar, tun a lokacin da mu ka sharafin mu, to a lokacin sai ya zama mun samu masu kula da mu tsakanin su da Allah, sai ya zama a cikin mu mu ka samar da matsalar, don mun samu masu kuɗi da su ka riƙa yi wa mawaƙan Annabi hidima iya ƙoƙarin su har da ba da kujerar Makka.
“To amma sai ya zama mu a kan mu da ya kamata a ce mun riƙe abin da hannu biyu, kuma ba mu yi ba. Don su masu yi wa Annabi hidimar, an shiga inuwar su an yi masu dashi, duk sai su ka ja baya da kulawar da su ke yi mana.
“Don haka daga an ji wani mai ki da ya ke son yin hidimar Annabi, sai wasu su je a guje su kewaye shi su hana kowa ya je wajen. Kuma idan su ka tarar da wani a wajen, to sai sun yi yadda su ka kore shi.
“Don haka harkar yabon Annabi a yanzu sai dai mu ce inna lillahi, don ba a ganin girman masu girma.
“Wannan ya sa samar da ƙungiyar da za ta wakilce mu a gwamnati ta gagara.
“Akwai lokacin da aka kira mu, mu sha’irai, mu ka tattauna da gwamna, inda mu ka faɗa masa buƙatun mu: mu na so a samar da mai ba gwamna shawara a kan sha’irai. Kuma an amince da hakan, aka ce mu samar da wani daga cikin mu.
“Tun da mu ka taso abin bai yiwu ba saboda mun kasa fitar da wanda zai riƙe muƙamin a cikin mu, saboda kowa bai yarda da kowa ba.
“Da na kira Yusuf Tumfafi, mai ba gwamna shawara a kan harkar ƙungiyoyi, na tambaye shi halin da ake ciki, sai ya ce, ‘Ai kun kasa haɗa kan ku, don wasu daga cikin ku su na ta bugo waya su na cewa su fa idan wane ne to ba za su amince ba. Don haka abin ya yi yawa, mu ka rabu da ku.’
“Irin wannan halin harkar yabon Annabi ta ke ciki; duk an bi an saka son zuciya da son girma.”
Da wakilin mu ya tambaye shi yadda za a yi a gyara matsalar a matsayin sa na uba a cikin harkar, sai Malam Bashir ya ce, “A gaskiya tun da Hukumar Tace Finafinai ta kasa haɗa kan sha’irai, ai ina ganin a jira a gani kawai daga Allah. Saboda hukumar ta shiga ta yi wa kowa rajista, to amma matsalar a jagorancin ta ke; duk wanda aka ɗauko aka ɗora shi, sai ya saka son rai a ciki. Shi kuma shugaban Hukumar Tace Finafinai ya ɗauki abin da zafi, sai ya zama ƙarshe abin ya yi shiru.
“Don haka tun da Hukumar Tace Finafinai ta gaza, to fa abin sai dai addu’a.”
Mawaƙin ya yi kira ga sha’irai da cewa su sani harkar yabon Annabi su ke yi, don haka ya kamata a riƙa ganin siffar Annabi a wajen aikin su da kuma mu’amalar su da jama’a.
![]()






