• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, October 12, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Buƙatar na sauya akalar siyasar da ake yi ya sa na tsaya takara – Aminu Ala

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
September 29, 2022
in Labarai
0
Alhaji Aminu Ala

Alhaji Aminu Ala

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MAWAƘI Aminu Ladan Abubakar (Ala) ya bayyana cewa ya shiga siyasa ne domin ya sauya akalar yadda ake tafiyar da harkar siyasa da tsarin ta a yau.

A tattaunawar sa da mujallar Fim, Ala ya ce: “Babu shakka, na shahara a waƙa ta fadakarwa da ilmintarwa da waƙoƙin sarakuna, da kuma wani siyasar da a yanzu na shige ta duka.  

“Da man can ina yin siyasa, amma a wani lungu, don siyasa ta na da lunguna da yawa. To, a cikin lungunan da ta ke da shi akwai waƙa, don haka mu na lungun tallar ɗan takara a tsakanin sa da jama’a. Kuma a yanzu sai aka wayi gari aka gan ni na fito takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano.”

Da mu ka tambaye shi ko wannan wani ƙudiri ne da ya ke da shi tun a baya ko sai a yanzu ne abin ya zo masa, sai ya amsa da cewa: “To, wannan ya zo ne daga baya, amma hakan bai zo mini da mamaki ba, tunda yanayi ne da ya zama mutane su na kiwon ka, kuma da man shi taken dimokiraɗiyya shi ne mulki daga mutane, su ne za su nuna nasu kuma sai a yi mulkin domin su.

“To mutane sun sun fito da ni a matsayin wanda su ke ganin sa a matsayin sananne kuma zai iya ba da gudunmawar sa saboda nagartar sa da su ke ganin idan su ka tsayar da shi ba za su ji kanya ba. 

“Ko waƙoƙin da na ke yi, za ka ga sadaukarwa ne, ba na samun kuɗi ba. Don haka ne ma jama’a su ka neme ni a wannan fage na takara. Don haka ni ina ganin saboda an zaɓe ni, rayuwa ta da halaye na ba za su sauya ba daga inda aka san ni.

“Don haka za mu yaƙi irin wasu matsaloli da su ka dabaibaye harkar siyasa ne don mu kawo sauƙi. Don haka ba za mu zo mu yi wa mutane ƙarya kawai don su so mu ba. 

“Don haka su mutane su san ma’anar wakili da aikin sa. To, ko iya wannan na yi na tsaya na wayar da kan mutane a kan haka zan iya cewa na ci riba. Don haka yunƙurin da na yi na fitowa takara shi ma na ci riba da shi, saboda a yanzu matasa iri na sun yarda cewa kowa ma zai iya. 

“Don haka aikin da ya ke gaban mu shi ne mu wayar da kan matasa a kan siyasar ‘yanci da kuma wayewa.”

Ɗan takarar ya yi kira ga matasa cewa su san kan su domin su ma su na da ‘yanci, bai kamata ya zama ana amfani da su ta wata hanya da ba ta dace ba, saboda buƙatun wasu na siyasa.

Loading

Tags: Aminu AladimokiraɗiyyaKanoMajalisar TarayyamatasaNassarawasiyasatainakon jama'a.waƙa
Previous Post

Mutuwar Bankaura: Mun yi rashi mai wuyar cikewa a Kannywood – Isa Ja

Next Post

Abin da ya sa mu sha’irai ba mu da haɗin kai – Bashir Ɗanɗago

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Malam Bashir Ɗandago

Abin da ya sa mu sha'irai ba mu da haɗin kai - Bashir Ɗanɗago

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!