* ‘Ba abin da ya rage a Kannywood sai zalunci da sharri da cin mutunci’
* ‘Zan maida iyali na Legas nan da wata 6’
ADAM A. Zango ya bayyana cewa ya koma Legas da zama saboda harkar fim da waƙa ta ruguje a Arewa.
Haka kuma ya ce nan da watanni shida ko sha-biyu masu zuwa zai ɗauke iyalin sa kacokam daga Kaduna ya mayar da su Legas.
Ya ce zai yi hakan ne domin shi fa yanzu ya bar harkar finafinan Hausa kwata-kwata, ya koma Legas da zama domin gudanar da sana’ar waƙa.
A hirar da ya yi da jaridar mako-mako ta Aminiya wadda aka buga a jiya Juma’a, shahararren jarumin kuma mawaƙi ya ce, “Na fara harkoki na (a Legas), komai ya kankama. Ina shirin cikin wata shida zuwa shekara ɗaya zan dawo da iyali na gaba ɗaya nan Legas, har da mahaifiya ta, cikin yardar Allah.”
A hirar, wadda wakilin jaridar ya yi da shi a garin Legas ɗin, Zango ya bayyana cewa tunda ya kai ƙololuwa a harkar fim a Arewa, to abu mafi a’ala gare shi shi ne ya koma Kudu da zama domin harkokin sa za su fi ci a can.
Ya ce, “Kamar ɗalibin ilimi ne da ya kammala karatun sakandare; idan ya na so ya ci gaba da karatu sai ya tafi makarantar gaba da sakandare ko ya je jami’a.”
Wani dalilin da jarumin ya bayar kuma shi ne Legas gari ne inda ake samun kuɗi sosai.
“Legas gari ne na samun rufin asiri,” inji shi. “Idan mutum na so ya samu rufin asiri mai nauyi, to Legas zai nufa.”
Jarumin ya bayyana baƙin cikin sa kan yadda al’amurran sana’ar fim da waƙa su ka sukurkuce a Arewa.
Ya ce: “A yanzu a arewacin Nijeriya mun samu matsaloli na wargajewar harkokin mu da lalacewar su da kuma matsala da mu ka samu da gwamnati wacce ta yi alƙawarin za ta tallafa mana ta gina mana harkokin mu, mu ka bada gudunmawar mu iya yin mu, amma har yanzu gwamnati ba ta waiwaye mu ba. Babu wani yunƙuri da su ka yi.
“Don haka dole ta sa duk wanda ya ke meman cigaba, dole ya yunƙura ya fito daga Arewa a wannan harka tamu.
“Kuma ina fatan abin da zan samu zai nunnunka abin da na ke samu a baya tun shiga ta harkar.”
Zango ya bayyana cewa in har aka ƙara ganin sa a Arewa, to wani aiki na musamman aka gayyato shi ko kuma biki ya kawo shi.
Ya yi kira ga al’ummar Arewa mazauna kudancin Nijeriya da su rungume shi da kyau, su riƙa gayyatar sa zuwa bukukuwa ko tarurrukan su domin ya nishaɗantar da su yadda ya kamata.
“Yadda su ka san ni da jajircewa wajen bai wa jama’a nishaɗi, to ga nesa ta zo kusa, na zo kusa da su. Za su riƙa gani na a wasanni da bukukuwa.”
Zango ya na da yaƙinin cewa kakar sa za ta yanke saƙa sosai a zaman sa na Kurmi, musamman ganin cewa “da ma a Kudu babu manyan jarumai ‘yan wasan Hausa.”
Ya ce yanzu haka ya na kan aikin ƙulla dangantaka da wasu manyan mawaƙa biyar na Kudu, wato su Davido, Burna Boy, Tekno, Olamide da Lighter. Ya ce a wannan shekara mai shigowa ta 2020 za a ga bidiyoyin waƙoƙi da za su shirya shi da waɗannan mawaƙan.
Amma dai ya sha alwashin cewa duk abin da zai yi a Legas, to zai kiyaye duk abin da zai taɓa mutuncin sa da na addinin sa.
Ya ƙara da cewa, “Kuma buri na shi ne ɗaga martabar harshen Hausa; don haka ne na zo in bunƙasa shi a nan Legas, in kuma ɗabbaka al’adar Bahaushe.”
A ƙarshen hirar tasa da Aminiya, Adam A. Zango ya ragargaji abokan aikin sa na masana’antar finafinai ta Kannywood masu yi masa bi-ta-da-ƙulli, ya ce saboda su ne ma ya sa ya fice daga masana’antar.
Ya ce: “Babu abin da ya rage a wannan masana’anta sai zalunci da sharri da cin mutunci a kai na. Ban ce a kan kowa ba.
“Me ya sa za ka zauna a wajen mutanen da su ke cin mutuncin ka, su ke yi maka ƙazafi, su ke yi maka sharri, su ke neman lallai sai sun binne ka da ran ka? Wannan shi ne dalilin da ya sa na yanke hukuncin barin masana’antar Kannywood.”