HOTON fitaccen darakta Sanusi Oscar 442 a cikin motar “ba biya” ta gidan yarin Goron Dutse ya fara yawo a soshiyal midiya a ranar Alhamis, 15 ga Agusta, 2019, a daidai lokacin da ’yan fim su ka fara kamfen ɗin a yi masa adalci sakamakon kama shi da aka yi bisa zargin ya saki bidiyon wasu waƙoƙi biyu ba tare da izinin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ba. Su na kamfen ɗin ne da ‘hashtag’ ɗin #justiceforoscar442.
A hoton, an ga Oscar sanye da shuɗiyar shadda da jar hular Kwankwasiyya, kuma ya naɗe wuyan hannu da tasbaha, lokacin da za a kai shi a sakaya shi a gidan maza bayan an gurfanar da shi a daɗaɗɗiyar kotun tafi-da-gidan-ka da aka kafa domin ’yan fim.
Hukumar ta kama Oscar ne a ranar Laraba, 14 ga Agusta, 2019 a bisa tuhumar cewa ya saki wasu waƙoƙi biyu ba tare da izini ba. Waƙoƙin su ne ‘Hasashe’, wadda jarumi Garzali Miko da jaruma Sadiya Adam su ka hau, sai kuma ‘So Na Amana’ wadda Garzali Miko da wata sabuwar jaruma ’yar ƙasar Nijar mai suna Rakiya Moussa Poussi su ka hau.
Ita ‘Hasashe’, ta kai aƙalla shekara biyu da aka yi ta, ‘So Na Amana’ kuma ba a kai wata uku da sakin ta ba.
A kotu, Oscar ya kare kan sa da cewa ba shi ba ne ya ke da haƙƙin sakin waƙa, shi iyakar aikin sa shi ne ya bada umarni, amma furodusa ne ke da ikon sakin waƙa ko fim.
Haka kuma ya ce shi bai da shafi a YouTube, don haka ba shi ne ya aikata laifin sakin waɗannan waƙoƙi biyu a soshiyal midiya ba.
A ranar Laraba, 17 ga Yuli, 2019 ne dai gwamnatin Jihar Kano ta sabunta naɗin Alh. Isma’il Na’abba (Afakallahu) a matsayin shugaban hukumar. Ta ce ta gamsu da yadda ya gudanar da aikin sa a cikin shekaru huɗu da su ka gabata.
A ranar Litinin, 22 ga Yuli ya shiga ofis tare da wasu ’yan fim.
A jawabin da ya yi a wurin, Afakallahu ya bayyana cewa sun kafa doka daga kan marubucin labarin fim har zuwa kan editoci sai sun yi rijista da hukumar, duk kuma wanda bai yi ba, ya yi aiki ya fitar, to doka za ta hau kan shi. Sannan kuma irin waƙoƙin da ake yi ba tare da fim ba ana sakin su a kafafen sadarwa na soshiyal midiya irin su YouTube da sauran su, su ma kafin a sake su sai an yi masu rajista, in kuma ba a yi ba doka za ta hau kan wanda ya yi aikin.
To, da ma a cikin daraktocin Kannywood, Sunusi Oscar da Aminu S. Bono ne su ka fi ƙwarewa wurin bada umarnin irin waɗannan waƙoƙi, inda shi Oscar kusan ta wannan hanyar ya ƙara yin suna a masana’antar, domin za ka ga an shirya fim ba shi ba ne daraktan fim ɗin, amma shi ne daraktan waƙoƙin fim ɗin.
Wasu daga cikin ’yan fim sun bayyana rashin jin daɗin su da kama Oscar da aka yi, su na faɗin cewar zalunci ne irin na zamanin tsohon shugaban hukumar, Malam Abubakar Rabo Abdulkarim, wanda ya riƙa kama ’yan fim ya na gurfanar da su a kotun musamman da aka kafa don ’yan fim, inda daga can ake tura su gidan yari.
Jarumi Mustapha Nabraska ya faɗa cewar shi ya ma fita daga Kannywood har sai wannan gwamnati ta Gwamna Umar Abdullahi Ganduje ta shuɗe. Wato kenan zai yi zaman jira na shekara huɗu.
A nasa tsokacin, jarumi Adam A. Zango ya faɗa wa Oscar cewa: “KA SAKE SAMUN SABUWAR ILIMI. @sunusi_oscar__442 . Ka yi haƙuri ɗan’uwa, babu abin da ba ya wucewa. Wata rana yadda na ke bada labarin shiga gida yari, kai ma haka za ka bada.”
Mawaƙi Aminu Alan Waƙa (Ɗan’amanar Bichi) ya ce: “A yanzu ka taka babban mataki wanda ba duka ido ke iya hangen sa ba. Idan akwai matsala a shiga kurkuku ba ta wuce dalilin shigar ka ba. In ya zamo an kai ka ne bisa zalunci kar ka damu, ka saurari sakamakon da Allah zai maka a kan duk wanda ya zalunce ka. Ina yi maka jajen wannan halin rayuwa, kuma ina yi maka murna da alkhairi da zai biyo bayan ƙasƙanci.”
Wasu fitattun jarumai waɗanda su ka nuna rashin goyon bayan kamun Oscar sun haɗa da Misbahu M. Ahmad, Abba El-Mustapha, Sani Danja, Maijidda Abbas da Teema Makamashi. Dukkan su sun yi bidiyo inda su ka yi kakkausar suka kan Afakallah.
Sai dai kuma akwai masu kallon lamarin ta fuskar siyasa, su na faɗin cewa an kama Oscar ne saboda goyon bayan sa ga ɓangaren Kwankwasiyya maimakon Gandujiyya.
Biri ya yi kama da mutum, domin kuwa a yawancin lokuta daraktan ya na sukar gwamnatin Ganduje, kuma ya na nunawa ƙarara cewa ya na adawa da gwamnatin, ya na nuna shi ɗan Kwankwasiyya ne, kuma kusan duk lokacin da za ka gan shi da jar hula za ka gan shi.
Wannan shi ke nuni da cewa shi ga ɓangaren da ya ke a siyasa.
Mujallar Fim ta lura da cewa yawancin ’yan fim ba su ce uffan ba game da kama daraktan da aka yi, ciki har da manyan jarumai irin su Ali Nuhu da kuma manyan furodusoshi waɗanda ya sha yi wa aiki.
Hasali ma dai, wasu sun yi zargin cewa wai da haɗin bakin Ali Nuhu wajen kamun Oscar, amma babu hujjar da su ka bayar kan hakan.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan labarin dai an hana kowa ya ga Oscar a gidan yari, an kuma ƙi bada belin sa.
An tsaida Talata, 20 ga Agusta, 2019 a matsayin ranar da za a koma kotu don ci-gaba da sauraren shari’ar.