ƊAYA daga cikin jaruman barkwanci a TikTok, Idris Mai Wushirya, ya ce alhakin su ya kama jaruma Murja Ibrahim Kunya, shi ya sa faɗa cikin matsala.
Idris, wanda aminin Murja ɗin ne, ya ce jarumar ta ci amanar su ne shi da jarumar ‘Izzar So’, wato Aisha Najamu, domin sun tsaya kai da fata a lokacin da ‘yan sanda su ka kama ta, amma abin mamaki sai ta zarge su da cewa su ne su ka sa aka kama ta.
A cikin wani bidiyo da ya wallafa a Instagram a yau Juma’a, Mai Wushirya ya ce su na tare da Murja a lokacin da aka kama ta, har aka tafi da ita, daga nan ne ya kira Aisha Najamu a waya, bayan ta zo su ka tafi hedikwatar ‘yan sanda ta Jihar Kano da ke Bompai, su ka yi ƙoƙarin ganin ta amma hakan bai samu ba sai da gari ya waye.
Ya ce bayan an ba da belin Murja a kan sharaɗin za ta yi bidiyo ta ba da haƙuri kuma ba za ta sake aikata abubuwan da ake tuhumar ta da su ba (batsa, cin mutunci, rashin tarbiyya), sai kawai ta kira shi ta ce masa ai an dakatar da asusun ta na TikTok, “sai na ce to ni zan ba ta nawa guda ɗaya ta yi amfani da shi.”
Mai Wushirya ya ƙara da cewa bayan mun yi haka, kawai sai na ga Murja ta yi ‘status’ a WhatsApp ta na cewa burin su ya cika (Mai Wushirya da Aisha Najamu) tunda an kama ta, daga nan abin ya dawo soshiyal midiya ta fara zage-zage musamman a TikTok.
Ya ce shi ya sa malaman da su ka shigar da ƙorafi a kan ta su ka ce a kai ta kotu kawai tunda ba za ta canza hali ba.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ruwaito a jiya cewa wata kotun shari’ar Musulunci da ke Kano ta ba da umarnin a tsare Murja a gidan yari, kafin a dawo a ci gaba da shari’a a ranar 16 ga Fabrairu, 2023.
Hakan ya biyo bayan ƙarar ta da wasu su ka yi na cewa ta ɓata masu suna a TikTok, sannan ta na shigar baɗala a soshiyal midiya.
![]()







