FITACCEN jarumi a Kannywood, Bilal Mustapha, shi ma ya shiga ƙwaryar manya domin kuwa a ranar Lahadi 21 ga Disamba 2025 ne aka ɗaura auren sa da sahibar sa, Bilkisu Ahmad Sa’id.
An ɗaura auren da ƙarfe 10 na safe a masallacin Juma’a na Uhud Juma’at Mosque, da ke Maikalwa a unguwar Na’ibawa kusa da ‘Yanlemo, kan Titin Zariya, a cikin garin Kano.
Jarumai da dama sun halarci wajen.

Tun kafin ranar ɗaurin auren ta zo, an yi shagalin biki a ranar Juma’a 19 ga Disamba, sai kuma wasan ƙwallon ƙafa da aka yi a ranar Asabar da yamma.
Bilal Mustapha yana ɗaya daga cikin matasan jarumai a Kannywood a wannan lokacin.
Ya fito a cikin manyan finafinai da suka haɗa da ‘Zo Mu Zauna’, ‘Labari Na’, ‘Garwashi,’ da sauran su.

![]()







