WATA ƙungiya ta masu kishin harkar nishaɗantarwa a arewacin Nijeriya mai suna ‘Entertainment for Arewa 2022’ ta shirya taron ta karo na farko domin karrama mutanen da su ka bayar da gudunmawa ga cigaban harkar fim da waƙoƙi.
An gudanar da taron mai taken Makon Nishaɗantarwa na Arewa (Northern Entertainment Week) a ranar Asabar, 10 ga Disamba, 2022 a Abuja.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa masu shirya taron sun bayyana cewa manufar su ita ce samar da wani tsari da zai kasance ana karrama mutanen da su ka daɗe su na ba da gudunmawa a harkar nishaɗantarwa tare da samar masu wata gudunmawa idan ƙarfin su ya ƙare ko rashin lafiya ko kuma iyalan su idan ba su da rai.
Don haka ne su ka fitar da wannan tsarin da su ke fatan nan gaba zai ɗore ya zama hanyar samar da tallafi ga mabuƙata ba tare da an shiga gidan rediyo ko soshiyal midiya ana neman taimako ba.
A taron na Abuja, bayan an yi jawabai tare da waƙoƙi, daga ƙarshe an karrama wasu fitattun mutane da su ke da rai da kuma waɗanda Allah ya yi masu rasuwa.

Cikin masu rai da aka karrama akwai Farfesa Abdalla Uba Adamu, Ado Ahmad Gidan Dabino, Balaraba Ramat Yakubu, Ibrahim Mandawari, Ƙarƙuzu, Dakta Ahmad Sarari, Sani Idris Kauru (Moɗa), Ladin Cima, Idris Shu’aibu (Lilisco) da Shehu Hassan Kano.
Cikin marasa rai da aka karrama kuma akwai Ƙasimu Yero, Goloɓo, da Usman Baba Pategi (Samanja Mazan Fama).
Taron ya samu halartar jama’a da dama da aikin su ko sana’ar su ya shafi harkar fim ko waƙa.
Shugabannin taron sun tabbatar da cewa za su ci gaba da yin taron domin ciyar da harkar nishaɗantarwa a Arewa gaba.
Shi dai wannan taro, Dattawan Kannywood sun yi murna da shi. A saƙon taya murna da ta wallafa, ƙungiyar dattawan mai suna ‘Kannywood Foundation’ ta bayyana jin daɗi kan wannan karramawa da aka yi wa ‘ya’yan ta.
A sanarwar, daraktan hulɗa da jama’a da kyautata harkokin sadarwa na ƙungiyar, jarumi Alhaji Mohammed Kabiru Maikaba, ya ce: “A madadin shugabancin majalisar ƙoli da ɗaukacin zauren dattawan masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, mu na matuƙar farin cikin taya manya-manya gwarazan ‘ya’yan wannan majalisa, wato Kannywood Foundation.
“Waɗannan gwarazan jarumai sun haɗa da mai girma Mai’unguwar Mandawari, Alh. Ibrahim Mohammed Mandawari, da Alh. Shehu Hassan Kano, da gwarzuwar marubuciya kuma jajirtaciyyar mai shirya finafinai, Hajiya Balaraba Ramat Yakubu Mohammed, da sauran ‘ya’yan wannan masana’anta da su ka sami wannan karramawa da tagomashi.
“Haƙiƙa, samun irin wannan girmamawa daga babbar ƙungiya da ta karaɗe Arewa don shirya bikin makon nishaɗi na Arewa, wato ‘Arewa Entertainment Week’, abin yabo ne kuma abin farin cikin ne da taya murna.
“Don haka Kannywood Foundation na farin da taya ku murnar samun irin wannan girmamawa da ɗaukaka. Haƙiƙa ya zama wajibi mu taya ku murna kuma mu taya ku addu’ar Allah ya taya ku riƙo. Kuma Allah ya ƙaro nasarori masu girma da albarka irin wannan da za su ƙara wa wannan masana’anta ta ƙara shahara da kuma ƙara sa ‘ya’yan cikin ta su ƙara zama mashahuran mutane a cikin wannan al’umma mai albarka. Allah taya ku riƙo. Mun gode.”
A wani saƙon na daban kuma, ƙungiyar ta yabi shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Mohammed Sarari, da cewa “ya kasance ɗaya daga cikin gwarazan furodusoshi kuma shumagabanin da katafariyar ƙungiyar ‘Entertainment for Arewa 2022’ ta ga dacewar su karrama a taron da su ka gudanar a Abuja. Don haka Kannywood Foundation ta ga dacewar da mu taya shi farin cikin samun wannan katafariyar lambar girmamawa da karramawa.
“Haka ya faranta wa shugabanci da ɗaukacin babban zauren majalisar rai. Don haka mu na taya Dr. Ahmed Mohammed Sarari murnar samun wannan katafariyar lambar girmamawa. Haƙiƙa an ajiye ƙwarya a gurbin ta.
“Mu na roƙon Allah ya taya riƙo kuma ya ƙara yauƙaƙa alheran da ke cikin lamarin.
“Kuma mu nai masa fatan Allah ya ƙaro dubban irin su. Kuma mu na taya ‘ya’yan wannan masana’anta mai albarka murnar samun ɗaya daga cikin iyaye kuma shugabannin wannan masana’anta ya samu wata alama da ke nuni da cewar wasu daga wani guri sun shaida kuma sun tabbatar da irin ƙoƙari da jajircewa da taimakon da wannan bawan Allah ya ke bayarwa wajen wakilta da kawo al’amurran da ke kawo ɗaukaka da cigaban wannan masana’anta. Dr. Sarari, Allah ya taya riƙo.”

