• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

An kulle mawaƙin Kwankwasiyya bisa zargin ya tozarta matar Ganduje

by DAGA ISAH BAWA DORO
February 5, 2020
in Labarai
0
Kosan Waƙa (a hagu) da Afakallahu

Kosan Waƙa (a hagu) da Afakallahu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
MAWAƘIN nan da ‘yan sanda su ka kama a Katsina su ka kai shi Kano ana zargin sa ne da laifuffuka da su ka haɗa da aikata ɓatanci a kan iyalin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
 
A jiya Talata mu ka ba ku labarin yadda ‘yan sandan su ka tashi takanas ta Kano su ka je Katsina su ka kamo mawaƙin siyasar mai suna Muhammadu Buhari, wanda aka fi sani da Kosan Waƙa, su ka tafi da shi Kano.
 
Wata majiya ta ce tare da amincewar rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina aka kama Kosan Waƙa, wanda mawaƙin rundunar siyasar Kwankwasiyya ne wadda ke adawa da Ganduje.
 
A yau Laraba aka gurfanar da shi a kotu mai lamba 72 da ke Nomansland a Kano, aka tuhume shi da sakin sabuwar waƙar sa mai taken ‘A Wanki Gara’ ba tare da sahalewar Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ba.
 
A kotun, an zarge shi da aikata ɓatanci ga Gwamnan Kano da iyalan sa, inda har aka faɗi inda ya ambaci kalmar “Gwaggo” a waƙar, wanda laƙabi ne na matar gwamnan, Hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje.
 
Wata tuhuma kuma ita ce yunƙurin tayar da tarzoma a cikin al’umma.
 
Bayan an karanta masa tuhumar da ake masa, Kosan Waƙa ya musanta zargin, ya na faɗin cewa shi ba da kowa ya ke ba, domin ai babu wanda ba ya da gwaggo.
 
Lauyan gwamnati, Barista Wada A. Wada, ya gabatar da shaidun da ake tuhumar mawaƙin a kan su.
 
Da lauyan da ke kare mawaƙin ya nemi a bada beli, sai Mai Shari’a Aminu Gabari ya ƙi.
 
A maimakon haka, sai ya tura mawaƙin zuwa gidan yari bayan ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar Talata, 11 ga Fabrairu, 2020.
 
Bayan an tashi daga kotun, mujallar Fim ta tuntuɓi shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alh. Isma’il Na’abba (Afakallahu), game da lamarin, inda ya ce ba shi da hurumin da zai yi magana saboda maganar ta na kotu. “A jira abin da kotu za ta ce,” inji shi.
 
Wannan shari’a dai ta tada muhawara musamman a Katsina inda wasu ke ganin hukumar ta wuce gona da iri, su ka ce ba ta da hurumin da za ta kai kama wani wanda ba ɗan Jihar Kano ba ta kai shi Kano. 
 
Wani tsohon shugaban hukumar, wanda ya buƙaci a sakaya sunan sa kuma, ya ce: “Hukumar Tace Finafinai iya Kano ne kawai ta ke da hurumi. Idan mutum ba a Kano ya ke ba, ba ta da hurumin hukunta shi. 
 
Ya ce, “Sai dai idan ka yi abin aka kama ana sayarwa a Kano, za a nemi ɗan kasuwar da ka sayar masa ya nemo ka a gurfanar da ku a kotu baki ɗaya. 
 
“Misali, Gwamnan Kano zai iya magana da Gwamnan Katsina ya sa a nemo yaron a kan me ya sa ya yi waƙar? 
 
“Ko kuma hukumar ta kai shi ƙara a Katsina tunda a can ya yi laifin, wanda ya ke zargin an yi waƙar don shi sai ya bi kadin haƙƙin sa a can, idan an same shi da laifi za a iya ladabtar da shi. 
 
“Amma a je Katsina a kamo shi a kai shi kotu a Kano, babu wani sashe inda aka rubuta haka a dokar hukumar.”

Loading

Previous Post

An kama mawaƙin Kwankwasiyya saboda waƙa mai taken ‘A Wanki Gara’

Next Post

Mahaifiyar Halima Atete ta rasu

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Marigayiya Hajiya Maryam Yusuf

Mahaifiyar Halima Atete ta rasu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!