AN zabi Rahama Sadau, daya daga cikin fitattun jaruman finafinan Hausa, a matsayin daya daga cikin mutum biyu da za su yi aikin gabatarwa a gagarumin bikin karramawa na finafinan Nollywood wanda ake kira Best of Nollywood Awards (BON) na bana. Dayan shi ne wani fitaccen dan wasan kudu mai suna Gbenro Ajibade.
Za a gudanar da bikin a ranar Asabar, 16 ga Disamba, 2017 a garin Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.
Gwamnatin Jihar Ogun din ce ta dauki nauyin shirya bikin a wannan shekarar.
A lokacin da ya ke magana da manema labarai kan zaben wadannan jarumai biyun, babban daraktan gasar ta BON, Mista Seun Oloketuyi, ya ce, “Zaben Rahama da Gbenro ya gudana ne bayan an bata hankalin dare sosai. Mun yi amfani da ka’idoji da su ka hada da tunanin saka mutane daga sassa daban-daban, kwarewa, da kuma yarinta; akwai wasu ’yan wasan wadanda mu ka lura da su, to amma dai Gbenro da Rahama ne su ka fi samun maki. Kuma a gaskiya mun yi murna da yadda su ka karbi gayyatar mu tare da nuna jin dadin su don shiga wannan abin tarihin.”
Ita dai Rahama, ba ta bukatar wata gabatarwa ga masu karanta mujallar Fim, illa iyaka mu kara da cewa kakar ta ta yanke saka ne a finafinan kudancin Nijeriya tun bayan da kungiyar masu shirya finafinan Hausa, wato MOPPAN, ta kore ta daga harkar fim saboda ta yi rawa da waka da rungume-rungume da mawakin hip-hop din nan mai suna Classic a shekarar 2016. Tun daga lokacin ta ke samun damar fitowa a finafinan Nollywood, har ta kai ma ta na jan finafinan a matsayin babbar jaruma.
An taba nada ta mukamin “Face of Kannywood” a bikin gasar City People Entertainment Awards a shekarar 2016.
Rahama ta fito a wasannin kwaikwayo na talbijin da su ka hada da ‘Super Story’, ‘Shuga – Season 6’ na kamfanin MTV, da kuma ‘Sons of the Caliphate’. Sannan ta fito a finafinan Nollywood irin su ‘Ajuwaya’, ‘Tatu’, ‘The Accidental Spy’ da kuma ‘Hakkunde’ wanda ya fito kwanan nan.
Shi kuma Gbenro, ya na daga cikin fitattun ’yan wasan kwaikwayo din nan da gidan talbijin na M-Net ya ke nunawa mai suna ‘Tinsel’. Ya na da digiri a fannin Biology daga Jami’ar Jihar Binuwai.
Ya fito a finafinai da dama, wadanda su ka hada da ‘The Wages’, ‘Twisted Throne’, ‘Gbomo Gbomo Express’ da kuma ‘10 Days in Suncity’. Shi ne mijin ’yar wasa Osas Ighodaro, wadda su ka haifi ’ya daya da ita.
A yanzu haka dai masu shirya gasar sun fitar da sunayen ’yan takarar gasar, inda su ka nuna cewa jaruma Omotola Jalade Ekeinde (fim din ‘Alter Ego’) ce za su kara da Mitchell Dede (‘What Lies Within’), Ufuoma McDermott (‘The Women’), Rahama Sadau (‘Tatu’) da Esther Audu (‘Inikpi’) a tseren zama Jarumar Jarumai a gasar.