* Ya ba Nura Hussain muƙami a Hukumar Alhazai
GWAMNA Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga Babban Sakatare na Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alh. Isma’il Na’abba (Afakallah), da ya yi amfani da hanyoyi na fasahar zamani wajen gudanar da ayyukan hukumar.
Ganduje ya bayyana haka ne lokacin da ya sake naɗa Afakallah a matsayin shugaban hukumar.
A sanarwar naɗin, wadda Babban Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan, wato Alh. Abba Anwar, ya bayar a ranar 17 ga Yuli, 2019, gwamnan ya bayyana cewa ya sabunta wa Afakallah naɗin ne saboda gwamnati ta gamsu da nasarorin da ya samu a shekaru huɗu da su ka gabata.
Bugu da ƙari, Ganduje ya tabbatar da cewa shugaban zai ci gaba da yin aiki babu ƙaƙƙautawa kamar yadda ya yi a baya, tare da fatan zai ɗora a kan haka.
Ya ce, “Aikin tace finafinai ya cimma nasarori masu ban-sha’awa saboda kyakkyawan tsarin shugabanci da ya bayar a hukumar. Ganin abin da ya aiwatar a zangon farko na mulki na, na tabbatar zai ɗora a kan hakan.”
Ya yi kira ga babban sakataren da ya yi amfani da hanyoyi na ƙirƙirar zamani wajen aiwatar da ayyukan sa.
Ya ƙara da cewa, “Yanzu mu na cikin zamanin amfani da sababbin hanyoyin fasaha, don haka za mu so mu ga yadda zai yi amfani da fasahar yaɗa labarai ta zamani a ayyukan sa.”
A wata sabuwa kuma, Gwamna Ganduje ya naɗa jarumi Nura Hussain a matsayin Memba na Kwamitin Gudanarwa na Hukumar Alhazai ta Jihar Kano.
![]()







