• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Hauwa Maina ta aurar da ‘yar ta

by DAGA ABBA MUHAMMAD
August 29, 2017
in Ranar Murna
0
Amarya Maryam da angon ta Umar a wurin bikin Ranar Al'adu

Amarya Maryam da angon ta Umar a wurin bikin Ranar Al'adu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HAUSAWA na cewa rana ba ta karya, sai dai uwar diya ta ji kunya. Allah cikin ikon Sa Ya nuna mana ranar da fitacciyar jaruma Hauwa Maina ba ta ji kunya, wato ranar auren babbar diyar ta, Maryam Bukar Hassan.

An dauren Maryam da Umar Ahmad a ranar Juma’a, 25 ga Agusta, 2017 a wani masallaci mai suna An-Nur da ke Abuja, bayan an idar da sallar Juma’a. An daura auren a kan sadaki N50,000.

Da misalin karfe 2:00 na rana kuma an yi wani gagarumin biki, wanda ake kira da suna lancin, a wani kayataccen wuri mai suna A-Class Park & Events Centre da ke Titin Kashim Ibrahim, a Maitama, Abuja.

Tun kafin ranar, mahaifiyar amarya ta shirya bikin ranar al’ada (Cultural Day), wanda aka yi a ranar Asabar, 19 ga Agusta a wani dakin taro mai suna Ceremonial Canopy da ke Rimi Drive, Unguwar Rimi, Kaduna.

An fara bikin da misalin karfe 5:30 na yamma. Mawaki El-Bash Muhammad shi ne kadai mawakin da ya halarci bikin. Wannan ne ya ba shi damar cin karen sa babu babbaka.

Wani abin mamaki shi ne duk da ya ke Hauwa Maina fitacciya ce a industiri, amma ‘yan fim da yawa ba su halarci bikin ba, sai kalilan. 

Wadanda su ka halarta sun hada da Ali Nuhu, Fatima Lamaj, A’isha ZIAU da mijin ta Yusuf Maina, sai Ibrahim Danguzuri, Abubakar Hunter, Mudassiru Barumi, A.A. Rasheed Kabala da Karima Dikko.

A wurin, wakilin mu ya ji wata furodusa ta  na fadin, “Inda Ali Nuhu ya bambanta da sauran kenan.” Ta ce tun kafin ranar bikin ya ke kira ya na tambaya yaushe bikin? Kuma sai ga shi ya cika alkawari.

An tashi daga bikin da misalin karfe 9:00 na dare.

. Kawayen Hauwa Maina su na yi mata liki

Haka kuma a ranar Lahadi, 20 ga Agusta, an yi bikin ranar iyaye mata (Mothers Day) wanda aka yi a babban dakin taro na Ahmadu Bello Sardauna Memorial Foundation da ke Titin Race, daura da Dandalin Murtala, Kaduna.

An fara bikin da misalin karfe 7:00 na yamma. A nan ma mawaki El-Bash Muhammad ne ya baje kolin sa.

Iyayen amarya da na ango sun cashe, an kuma ci an sha. Ita ma mahaifiyar amarya ba a bar ta a baya ba, domin kuwa ta rangada wa ‘yar tata wakar bankwana da yaren su na Babur. Ta na fara rera wakar, sai kuma ta fashe da kuka. Nan da nan ‘yar ta zo ta na lallashin ta.

An tashi daga bikin da misalin karfe 10:00 na dare.

Tuni dai Maryam ta tare a gidan mijin ta.

Loading

Previous Post

Ganduje na so Afakallah ya yi amfani da fasahar zamani a aikin tace finafinai

Next Post

Ishaq ya samu dan fari

Related Posts

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira
Ranar Murna

Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira

August 2, 2026
Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a
Ranar Murna

Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a

July 31, 2026
An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5
Ranar Murna

An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5

July 15, 2026
Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu
Ranar Murna

Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu

July 12, 2026
Next Post
Ishaq ya samu dan fari

Ishaq ya samu dan fari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!