Abin kamar ba wuya! Kamar yau ne aka gama hidimar bikin auren Ishaq Sidi Ishaq da Nasiba Alkali Wada, wadda jarumin ya fara bayyana wa duniya soyayyar su a ran 8 ga Fabrairu, 2016. Ishaq ya wallafa dimbin hotunan da ke nuno shi tare da sahibar tasa don nuna shaukin so da ke tsakanin su.
An daura auren su a Minna, Jihar Neja, a ranar 26 ga Fabrairu. To yanzu dai wannan aure ya yi albarka, domin kuwa a ranar 7 ga Disamba, 2016 Allah Ya nufe su da samun karuwa ta da namiji. Nasiba ta haihu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano.
Ishaq da kan sa ne ya bayyana labarin haihuwar a shafukan sa na soshiyal midiya, tare da wallafa hotuna biyu na jaririn, da kuma hoton sa a asibiti ya na rungume da dan. A Instagram, ya rubuta da Turanci: “Alhamdu lillah! Yanzun nan mata ta ta haifi lafiyayyen da namiji! Su duka biyun, wato matar tawa da jaririn, su na cikin koshin lafiya.”
Nan da nan mutane su ka yi caa su na taya Ishaq da Nasiba murna.

An rada wa jaririn suna Sidi Abdulkadir, wato sunan mahaifin Ishaq din kenan, don haka yanzu ake kiran jaririn da sunan Sidi Ishaq Sidi. Haka kuma ana kiran sa da lakabin Abya’az.
Mu na fatan Allah Ya raya shi a cikin salihan bayi.