• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Waƙar Ta’aziyyar Mallam Mu’azu Haɗejia ta Alhaji Mudi Sipikin

by DAGA ALHAJI MUDI SIPIKIN
January 10, 2017
in Marubuta
0
Daga hagu: Alhaji Mudi Sipikin (1930-2013) da Malam Mu'azu Haɗejia (1918-1958)

Daga hagu: Alhaji Mudi Sipikin (1930-2013) da Malam Mu'azu Haɗejia (1918-1958)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Ya Rabbi ya Rabbi ya mai iyawa,

Ya wanda kai ke da iko da kowa,

Mai raya kowa a ya mai kashewa,

Ya wanda rayin sa ba ya tuƙewa,

Kai ke da iko Ilahi ɗaya.

Ya wanda yai wo mu ya mai sama,

Wajen ka Ilahi a nan za mu koma,

Mun tabbata kai ke da girma,

Iko da mulki sa’annan da rahama,

Kai ke da su duk ga baki ɗaya.

Mun shaida Allahu guda ɗaya ne,

Muhammadu Manzo ma’aikin sa ne,

Tashin ƙiyama ko duk gaskiya ne,

Rasawa ga duk masu rai zahiri ne,

Mun gaskata za mu bar duniya.

Ilahi ka gafarci Mallam Mu’azu,

Ka yafe shi ya Rabbi ya Al-Azizu,

Mallam Mu’azu mutum mai wa’azu,

Haƙiƙa cikin zamanin nan na yanzu,

Samun kama tasa a sha wuya.

Wajen dai fasaha da halin nagarta,

Da kirki da son jama’a da fahimta,

Wajen yin ibadar sa ba ya bakinta,

Halin sa duk ya wuce a kwatanta,

Na kirki da ƙaunar zaman lafiya.

Idan mu ka koma wajen tsara waƙa,

Ya san ta sosai sani na haƙiƙa,

Mallam Mu’azu ya na da hazaƙa,

La shakka wallahi innal firaƙa,

Ta na ba mu tsoro a duk safiya.

Na san shi ba wai sanin nesa ba,

Na san fasahar sa ba ‘yar kaɗan ba,

Ko littafan sa idan mu ka duba,

 Ta hanyar su ne har ya ƙara muhibba,

Gama ya yiwo su cikin gaskiya.

Dukkan mawaƙi idan har ya lura,

Ya duba su in dai ya na da basira,

Ya nuna ilmin sa ya yi ishara,

Yai gargaɗi kuma ya yi bushara,

Ta’ala ka yafe shi baki ɗaya.

Rashin sa rashi ne na dukkan ƙasar mu,

Gama shi guda ne cikin masu ilmu,

Wallahi mu kam rashi ne gare mu,

Allahu kai gafara a gare mu,

Dukkan mu ya Rabbi baki ɗaya.

Tuna shi haƙiƙa ya na ba ni kewa,

Ganin dai zaman duniya mai wucewa,

Haƙiƙa abin nan akwai tsoratarwa,

Wallahi tallahi kowa da kowa,

Dukkan mu dai za mu bar duniya.

Ya ‘yan’uwa ku gane ku lura,

Abin nan fa ya isa dukkan ishara,

Mu tuba ga Allah mu dinga basira,

Mu tabbata dukkan mu ran lahira,

Duk za a tara mu baki ɗaya.

Ai mutuwa dai tafakun mu ce,

Dukkan mu tilas mu zo mu wuce,

Ta kan ta gama babu mai karkace

Wa wannan tafarki kawai sai mu ce,

Ta’ala ya yafe mu baki ɗaya.

Ba tsimi ba dabara gare mu,

Ba wani wayo da himma wajen mu,

Mu zam masu ɗa’a mu taimaki kan mu,

Mu zam bauta Ilahu ɗaya.

Wallahi tallahi ba ni kaɗai ba,

Mai hankali duk ya na fargaba,

Wajen mutuwa sai mu dai roƙi Rabbi,

Ya tsarad da mu daga dukkan azaba,

Ya cece mu tun daga nan duniya.

Wallahi tallahi in mun fahimta,

Idan mun tsaya mun shiru mun kawaita,

Za mu da wallahi duk mun bakinta,

Batun mutuwa mun ƙi yin tattalin ta,

Mun kasa gane ta nan duniya.

Ya Rabbana na yi roƙo gare ka,

Don Annabawan ka don ɗaukakar ka,

Mu’azu ka yafe shi ga ni gare ka,

Allahu nai sujjada a wajen ka,

Ka yafe shi ya Rabbi Sarki ɗaya.

Allahu in ya yi laifi gare ka,

Wallahi na tabbata rahamar ka,

Ta na nan a duk ko’ina babu shakka,

Ka kai gare shi ya san taimakon ka,

Kai ne da rahama Ilahi ɗaya.

Mu’azu mutum ne sahihi na kirki,

Tawali’u sannan ga ƙwazo ga aiki,

An gaskata ba shi san nuna raki,

Allahu yai wo shi mai arziki,

Da son jama’a ba shi son tankiya.

Na gode Allah da dai mu ka saba,

Da wannan mutum mai basira da haiba

Mai kwarjinin zahiri mai muhibba,

Ilahi ka sanya ba zai sha wuya ba,

Ka sanya shi Aljanna baki ɗaya.

Ka sa haƙuri gun iyalin sa Rabbi,

Ka yafe shi ya Rabbi in ya yi aibi,

Mutanen sa duk ummin shi har da abbi,

Allahu don Musɗafa Annabi,

Ka shafe zunuban sa baki ɗaya.

Na tabbata shi da Mallam Sa’adu,

Su na shan yabo kuma sun sami shaidu,

Na kirkin su domin fasahar su du,

Allah ya Rabbi ya Alshahidu,

Ka yafe su dukkan su baki ɗaya.

Babu kamar su a dukkan Arewa,

Irin ɗabi’o’in su kirki ga kowa,

Da son jama’ar su kaza girmamawa,

Da son Musulunci su na taimakawa,

A san ilimi duk ga baki ɗaya.

Sun san Arewa fa sun san halin ta,

Sun san mutanen ta har asalin ta,

Gama sun fahimci irin sha’anin ta,

Kuma sun fahimci mazauna cikin ta,

Sun gane komai ga baki ɗaya.

A loton zaman su cikin rayuwar su,

An ƙaru sosai da halin zaman su,

Ina ma loton su an ƙarfafa su,

An ba su komai da zai taimake su,

Da an ga haske ga baki ɗaya.

Babban rashi kuma Mallam Makama,

Mutum ne fasihi da ke bada himma,

A kan ‘yan Arewa su dai ƙara azama,

Domin ta yin haka ne za su girma,

Su san matsayi har su zam siniya.

Ɗabi’ar sa hali na kirki, kawaici,

Kullum nufin sa a dai sami ‘yanci,

A zauna cikin lafiya da mutunci,

Mai bada himma wajen Musulunci,

Dattijo ne mai sanin gaskiya.

Ta’ala ka kai rahama kabarin su,

Ka yafe su dukkan su kai ne ka yi su,

Ka sa haƙuri wajen ‘yan’uwan su,

Ka kai ran su Aljanna firdausiya.

Wallahi ba za na manta da su ba,

Cikin rayuwa har in koma ga Rabba,

Garin ko irin yadda dai mu ka saba

Da su ya ishe ni tunanin gaba,

Muddin zama na cikin duniya.

Ya Rabbi ya Rabbi kai ne da iko,

Gare ni Ilahi ka yiwo taimako,

Ya wanda ba shi da ƙarshe da farko,

Na tabbata babu mai taimako,

Sai kai kaɗai ya Ilahi ɗaya.

Mai tsara waƙa idan za ku nema,

Alhaji Mudi Sipikin na Darma,

Ina yin salati ga Sarkin karama,

Ya ‘yan’uwa na mu dai ƙara azama,

Mu san za mu koma ga Sarki ɗaya.

Loading

Previous Post

Da Ban San Shi Ba

Next Post

An nada Rahama Sadau mai gabatarwa a bikin gasar BON Awards ta bana

Related Posts

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 
Marubuta

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 

January 1, 2025
Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 31, 2024
‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 20, 2024
Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai

November 30, 2024
Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau
Marubuta

Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau

November 27, 2024
Ƙungiyar matasa da mata za ta naɗa Ado Gidan Dabino Sarkin Mawallafan Arewa
Marubuta

Gasar rubutu: Hukumar Tace Finafinai ta bayyana gwaraza 50 na zagayen farko

November 24, 2024
Next Post
Rahama Sadau da Gbenro Ajibade

An nada Rahama Sadau mai gabatarwa a bikin gasar BON Awards ta bana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!