LITTAFI: Da Ban San Shi Ba
MARUBUCIYA: Fauziyya D. Sulaiman
KAMFANI: Abin Yabo Publishing Company, Kano
SHAFUKA: 152
FARASHI: N200
SHEKARA: 2016
ISBN: BABU
Fauziyya D. Sulaiman sananniya ce kuma shahararriyar marubuciyar da za a iya kira lamba daya a mata marubuta na wannan zamanin. Bayan rubutun littafi, marubuciyar finafinan Hausa ce, sannan ma’aikaciya ce a gidan talabijin na Arewa24 da ke Kano.
LABARI
‘Da Ban San Shi Ba’ labarin wani yaro ne Aliyu da aka kawo shi almajiranci a birni daga kauyen su Sambauna. Bayan ya sha wahala irin ta almajiranci sai tsautsayi da tsananin wahala ta rayuwa ta sa shi zuwa wurin wani gardi a tasha, wanda ya nemi bata masa rayuwa ta hanyar neman maza. A dole Aliyu ya gudu ya sha da kyar, ya fadi a kofar gidan wani mutum a sume. Da safe mutumin, mai suna Alh. Musa, ya tsince shi ya kuma taimaka masa.
Alh. Musa na da mata, Hajiya Bilkisu, da ‘ya mai suna Hanan. Ya rike Aliyu da amana, ya saka shi a makarantar addini da ta zamani har ya zama mutum ya kammala digirin sa. Sai dai Hajiya Bilkisu da Hanan sun tsani Aliyu matuka, su na cewa almajiri ne, su kuma ‘yan gayu.
Alh. Musa ya nada Aliyu a matsayin manaja, ya gina masa gida, sannan ya wanke ‘yar sa zai ba shi.
A nan fa aka fara cakwakiya, domin bayan tsanar da Hanan ke yi wa Aliyu akwai saurayin da ta ke so (Mansur), wani baduniyi wanda ya yi karatu a Turai.
A gefe kuma wata budurwa ‘yar wani attajiri (Fa’iza) ta dage Aliyu ta ke so, yayin da shi kuma bai damu da ita ba. Cikin kankanin lokaci ya tsinci kan sa a soyayyar Hanan ba tare da ya sani ba.
Alh. Musa kuma ya dage kan lallai Aliyu ne zai auri Hanan, domin ya yi kama da dan sa da ya yi hadari ya mutu tare da mahaifiyar sa.
WARWARAR JIGO
– Labarin ya fito da illar kai yara kanana almajiranci, domin da Aliyu ya biye wa son zuciya da ya tsinci kan sa a mummunar hanya.
– An nuna amfanin taimaka wa wanda ya ke cikin wani hali, kamar yadda Alh. Musa ya yi.
– Biye wa son zuciya da bijire wa iyaye ba shi da alfanu, kamar yadda Hanan ta yi, daga baya ta kwana nadama.
SALO
Marubuciyar ta yi amfani da mkakken salo ne ta hanyar da zai kayatar. Hausar littafin mai saukin fahimta ce. Haka kuma taurari da garuruwan labarin sun dace da labarin sosai. Akwai rike tunanin mai karatu ta yadda labarin zai ba shi sha’awa.
ZUBI DA TSARI
An zubo labarin ne bisa amfani da karin magana da salon magana, zubin da ba kowanne marubuci ba ne ke iyawa. Haka tsarin labarin ya tafi tiryan-tiryan ba karaya, ta yadda ba zai gimshi mai karatu ba.
KA’IDOJIN RUBUTU
An kiyaye ka’idojin rubutu a littafin, duk da yake a wasu wuraren an rika rubuta wata kalma ba daidai ba (abin da marubutan ke kira typing error).
KKURAKURAI
1. Shafi na 3 littafi na 1: “… su na barar tumun dawa…” Ba a cewa tumun dawa sai dai tumun gero.
2. A shafi na 27 littafi na 1: Marubuciyar ta ambaci “garken akuyoyi” maimakon “garken awaki”.
3. Littafi na 1 shafi na 56: Marubuciyar ta ce, ran Alu ya rabu da gangar jikin sa, wato ‘ya mutu’, amma a shafi na 58 sai ga shi Alu ya farfado. Da ma ana mutuwa a dawo? Ina ma dai cewa ta yi, ‘…ran shi ya rabu da gangar jikin sa na wucin-gadi.’
4. A wajen zubin labarin an maimaita taken, ‘KOWA YA BAR GIDA,’ maimakon a samar da wani taken a matsayin ci-gaban labarin. Duba shafi na 11 da 35 littafi na 2.
5. Canjin suna daga shafi na 41 zuwa na 42 a littafi na 2: Lokacin da Rabe ya ke ba wa Aliyu labarin bayan rabuwar su, ya ce ya hadu da wani almajiri Baba, amma sai sunan Buba ya koma Ilu.
6. Duk da yake jigon labarin ya na nuna illar kai yara almajiranci, amma marubuciyar ta bar kashi casa’in cikin dari na labarin ya koma kan soyayya.
7. A littafi na 3 shafi na 107: ‘Yan fashi sun shiga gidan makwabtan Aliyu da Hanan, sai aka ce Hanan ta ji karar harbi… har kuma harsashi ya fado gidan su. Daga baya marubuciyar ta ce sun kashe mai gidan ne kawai. A yanayin wurin ya fi kama da musayar wuta da ‘yan sanda, saboda harbin ya yi yawa.
8. A shafi na 109 littafi na 3: Marubuciyar ta ce ‘yan fashin sun kashe mai gidan kadai, amma a can gaba sai ta ce “an fita da gawarwakin zuwa makwancin su.” Shin mutum nawa aka kashe?
9. A shafi na 87 littafi na 4: Sunan mahaifiyar Mansur Zaituna, amma a shafi na 125 sai ga shi sunan ta ya koma Haj. Bahijja. Ko ya aka haihu a ragaya?
10. Abu ne mawuyaci a saka ranar auren Aliyu da Fa’iza har kuma a yi biki ta tare da wata guda ba tare da ta san labarin rabuwar Aliyu da matar sa ba. Duba shafi na 87, littafi na 4.
11. Babu inda aka rubuta kalmar ‘yarda’ daidai a gaba daya littafin daidai, sai dai ‘yadda’. Wadannan kalmomi su na da bambanci a jimlace.
A gaida hazikar marubuciya.