* Zan zama mace ta farko da za ta tsaya takarar mataimakiyar gwamnan Kano
FITACCIYAR jaruma Rasheeda Adamu Abdullahi (Maisa’a) ta yi watsi da ce-ce-ku-cen da wasu ke yi a soshiyal midiya cewar ita da babban furodusa Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama za su yi aure.
Mutane da dama sun yi zaton manyan furodusoshin biyu su na daf da auren juna ne bayan bayyanar wasu hotuna da Rasheeda ta wallafa a Instagram inda aka gan su tare kamar cikin shauƙin soyayya.
Amma a cewar Rasheeda, babu wata maganar soyayya a tsakanin su, abin duk shiri ne.
Maisa’a ta bayyana haka ne a safiyar yau Talata a zantawar da ta yi da mujallar Fim jim ƙadan bayan ta kammala wani shirin rediyo a Kano.
Jarumar ta ƙara da cewa ita kam tsakanin ta da Iyan-Tama sai girmamawa, kuma ta ɗauke shi a matsayin uba.
Ta ce, “Kowa ya san cewa Hamisu Iyan-Tama darakta ne, furodusa ne kuma jarumi ne a Kannywood, kuma a gefe guda uba ne. Ni da Iyan-Tama akwai girmamawa da mutuntawa tsakani na da shi ƙwarai da gaske, domin kuwa a lokacin ma da ya yi finafinan sa ina jaririya, ban ma shigo industiri ba.
“Wannan abu kuma da mutane su ke faɗa na cewa zan auri Iyan-Tama ba haka ba ne. Kawai dai akwai wani fim ɗin shi wanda ya ɗauki ƙudirin dawo da ni masana’antar shirya finafinai a matsayin jaruma, wanda da har na ce ni ba zan yi ba, daga baya kuma na amince. To shi ne sai mu ka ɗan yi wasu hotuna, domin idan za ka yi fim sai ka yi hotunan da za a sa a fastar fim ɗin.
“Sunan fim ɗin kuma ‘Saura Ƙiris’. To sai mu ka ɗan yi waɗannan hotunan, na ɗora su a kan shafi na na sada zumunta na Instagram tare da rubuta cewa ‘Saura Ƙiris’.
“Tab! Wallahi ranar ban yi bacci ba saboda wannan kalmar da na saka ta ‘saura ƙiris’. Nan fa duniya ta ɗauka, masu kira na su na mani fatan alkairi, da masu yin maganganu daban-daban.
“Wanda ma ya ke a kusa da ni cajin wayar sa ma sai da ya ƙare a ranar nan saboda amsar kira.”

Jarumar ta ƙara da cewa, “A lokacin da na saka hoton, mu na tare da Iyan-Tama. Sai na ce masa, ‘Yanzun nan ‘yan YouTube za su ɗauki abin nan su canza masa manufa.’
“Kamar baki fa na yi! Ai kuwa hakan ne ya faru. Har ma da ‘yan jaridu, wasu ma ba su tattauna da ni ba, kawai wasu su ka gani sun yi su ma su ka ɗauka.
“Da na ga abin ya yi yawa a kan wannan maganar auren, da har zan yi fuska, na ce, ‘Menene? Ba za mu yi auren ba in auren ne?’ Sai na ga dai to shi za a hana bacci.
“A dai kuma wannan lokacin na ga dai ‘yan tsofaffin zawarawa na duk hankalin su ya tashi! (dariya) Don wallahi akwai bazawari na da matar sa ta ke ba ni labari, a ranar ya shiga ɗaki ya fi sau talatin ya na maimaita suna na, ‘Maisa’a! Maisa’a!’ Na yi dariya na ce da na sani ma auren nan na yi, tunda ina da samarin.
Kuma ta ce, “Ina tabbatar wa da jama’a da masoya na cewa babu wannan maganar ta aure tsakani na da Hamisu Iyan-Tama domin shi baba na ne, kuma tsakani na da shi addu’a ce da fatan alkairi.
“Kuma har yazu akwai wanda bai yarda ba cewa aure za mu yi da Iyan-Tama. Na ce masa wallahi tallahi a fim ne, kuma kwanan nan fim ɗin zai fito.”
Maisa’a ta yi wa masoyan ta albishir da cewa ta amsa kiran su, nan ba da jimawa ba za su fara ganin ta a finafinai waɗanda kamfanin ta ya shirya tare da na jama’a.
Ita dai Rasheeda Maisa’a, ta yi ɓatan dabo a Kannywood tun bayan da ta tsunduma cikin harkar siyasa tare da maida hankali wajen taimakon marayu da mata ta hanyar gidauniyar ta mai suna ‘Maisa’a Charity Foundation’.
A ɓangaren siyasar, jarumar kuma babbar furodusa ta faɗa wa mujallar Fim cewa a da ba ta da niyyar shiga takarar wata kujera, amma yanzu ta na sa ran za ta zamo mace ta farko da za ta fito takarar zama mataimakiyar gwamnan Jihar Kano.

![]()







