• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ba hauka ke damun Ashiru Nagoma ba, inji Fauziyya D. Sulaiman

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
January 14, 2021
in Labarai
10
Ba hauka ke damun Ashiru Nagoma ba, inji Fauziyya D. Sulaiman
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAR gidauniyar taimaka wa mabuƙata ta Creative Helping Neddy Foundation  kuma fitacciyar marubuciya da ke Kano, Malama Fauziyya D. Sulaiman, ta ƙaryata ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa cewa darakta Ashiru Nagoma ya samu lalurar taɓin hankali.


Haka kuma ta faɗi dalilin da ya sa ta jagoranci kai fitaccen daraktan na finafinan Hausa asibiti a yau saboda a duba lafiyar sa.


Shi dai Nagoma, wanda a zamanin tashen sa a industiri ake kiran sa da “the Intelligent Director”, ya daɗe ba a jin ɗuriyar sa a masana’antar finafinan wadda ake kira Kannywood.


Mujallar Fim ta taɓa buga labari a kan halin rashin lafiya da ya ke ciki kamar shekara biyu da ta gabata.


A safiyar yau kuma, wato 14 ga Janairu, 2021, sai aka tashi da labarin cewa wai Ashiru ya haukace, har aka nuno wani hoto nasa wanda ya ke nuna shi a matsayi mara kyau.


Ɓullar hoton tare da surutun da ake yaɗawa na cewa ya taɓu ya zagaye ko’ina a soshiyal midiyar Hausawa, inda mutane su ka dinga faɗin albarkacin bakin su.


Daga baya kuma sai labari ya ɓulla cewa Fauziyya ta jagoranci kai Ashiru asibiti domin a duba shi.

A hirar da ta yi da mujallar Fim ɗazu, Malama Fauziyya ta ce, “Tun lokacin da na wayi gari a safiyar yau Alhamis na ga yadda ake saka hotunan wannan bawan Allah a kan shafukan yanar gizo, abin ya tayar mani da hankali ganin yadda na gan shi cikin wani mummunan yanayi.


“Kuma ka san cewar duk da dai ni ban taɓa yin hulɗa da shi ba, ban taɓa yin aiki da shi ba, amma dai na san sunan shi. Sai hankali na ya tashi, saboda haka sai na fara tuntuɓar wasu waɗanda na sani ‘yan Kannywood ɗin, musamman a wani guruf na Kannywood, sai na tura maganar cewa su waye ne su ka fitar da wannan hoto, ai bai kamata ba.


“To a wannan lokacin ne dai na yi wannan maganar a guruf ɗin, aka fara tattaunawa a kan batun nasa, sai dai kuma da yawan ‘yan Kannywood su ka nuna cewa sun yi yunƙurin taimaka mai a baya amma dai ‘yan’uwan sa su ka nuna cewa ba sa buƙata, kamar irin an ɗora mai wani lalura ne da bai kamata a ɗora masa ba. Su kuma da su ka gaji su ka janye hannun su.”


Fauziyya ta ci gaba da bayyana cewa, “Ganin haka ya sa na fara neman wanda ya ɗauki wannan hoton, wato Aminu Bacci, inda na tuntuɓe shi a kan cewa ya aka yi ya saka wannan hoto? Sai ya ce shi dai gaskiya Ashiru Nagoma ya zo gurin su ne sun yi wasa sun yi dariya kuma sun ci abinci tare, to shi ne su ka dafa juna da Musa Maisana’a da shi Aminu Bacci su uku su ka yi hoton kuma su ka saka shi a soshiyal midiya, su ma kuma su na takaicin halin da ya tsinci kan sa ne a ciki, shi ya sa su kai haka.


“Saboda haka, mu ƙarƙashin ƙungiyar mu mu na so za mu kai shi asibiti. Kuma da man na faɗa a cikin shi guruf ɗin na Kannywood cewa in dai ɗaukar sa zuwa asibiti ne, mu ba zai dame mu ba, za mu ɗauki nauyin sa mu kai shi asibiti a ƙarƙashin gidauniyar mu ta ‘Creative Helping Neddy Foundation, to amma wanda zai iya shigowa daga baya ya taimaka  sai ya shigo ya tai maka a yi tare.”


Fauziyya, wadda ita ma marubuciyar finafinai ce, ta ƙara da cewa, “A daidai lokacin da mu ka yi yunƙurin taimakawa sai mutane su ka fara nuna mana cewa ai ‘yan’uwan sa ne ba za su yarda ba. Hakan ta sa mu ka ƙara tuntuɓar Aminu Bacci a kan cewa mu na so ya neman mana yardar ‘yan’uwan nasa, in dai sun amince su ba mu a rubuce to za mu je.


“Ana haka kuma, cikin ikon Allah, wani ya kirawo mu ya ce ya samu damar zantawa da ‘yan’uwan shi Ashiru ɗin kan ko za su yarda a taimaka masu, kuma haka aka yi su ka yarda.”

Hoton Ashiru Nagoma wanda ya tayar da hankalin jama’a a soshiyal midiya a yau


Sai dai da mujallar Fim ta tambayi Fauziyya kan raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa ‘yan fim sun yi wani yunƙuri na tallafa wa wannan bawan Allah, sai ta kada baki ta ce, “’Yan’uwan wannan matashi sun bayyana mana cewa babu wani wanda ya taɓa zuwa ya ce zai kai shi asibiti. To a nan ne na ce to mu haɗu da su, dan da nan kuwa su ka ɗauko shi wajen ɗaukowar ma sai da su ka yi masa dabara ta hanyar ɗauko ɗan sanda a matsayin za a kai shi kotu ya yi laifi sannan ya yarda su ka kawo shi.

“Daga nan ne kuma mu ka ga likita, ya duba shi, kuma ‘yan’uwan sa su ka ba mu takarda a rubuce cewa sun yarda mu kula da shi.”


A cewar Fauziyya, “Babu ce da man ta hana a kai shi asibitin kuma ‘yan’uwan sa sun nemi taimako domin a taimaka a kai shi asibitin amma ba su samu an taimaka ba, saboda ɗaukar nauyin jinyar ya na da ɗan tsada sakamakon magungunan sa akwai kuɗi kuma alhamdu lillahi kowa ya amince kuma mun yi hakan a rubuce.


“Yanzu haka dai an bai wa Ashiru Nagoma kwanciya a nan Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.”


A game da zargin da ake yi na cewa wai ciwon hauka ne ya sami Ashiru, marubuciyar ta ce, “Gaskiya ba haka ba ne. Kawai abin da mu ka sani shi ne damuwa ce ta sa shi haka kamar yadda su likitocin su ka nuna. Kuma ai da man can ma za ka iya hira da shi sosai. In ka na magana da shi, ya san komai sai dai kawai a cikin hirar za ka ji ya na ɗan sako shirme. Dalilin haka shi ya sa ya ke zuwa ko’ina kuma ya na gane kowa, wanda kuma yanzu haka an ajiye shi a ɓangaren masu cutar damuwa, ‘depression’ a turance kenan.”


Ta ƙara da cewa, “Ɗaya daga cikin abin da ya sanya shi wannan damuwa ita ce rashin iyaye. Ba shi da uwa ba shi da uba, duk sun mutu. To wannan ma ya ƙara masa damuwa.”


Mujallar Fim ta nemi sanin ko tsohon daraktan ya na da mata ko ‘ya’ya. Fauziyya ta ce, “A’a, ba shi da mata ba shi da ‘ya’ya, shi kaɗai ne. 


“Kuma yawanci ko da yaushe sai ya shiga wurin ‘yan Kannywood kamar yadda su ke faɗa kuma su ba shi kuɗin abinci; wannan ya ba shi dubu biyu wannan ya ba shi kaza. Haka su ke yi masa, don su na kiran shi ma wani lokacin su na yin wani aiki na ɗora murya.


“Kuma ko yanzu akwai waya a wurin shi, zai iya kiran kowa. Sannan san da za a yi aiki su na kiran sa ya ɗora murya.”


Awoyi kaɗan kafin hirar ta da ɓujallar Fim, Fauziyya ta saki wata sanarwa inda ta tura hotunan su a asibiti tare da faɗin cewa: “Alhamdu lillah ala kulli halin, bayan amincewa da ‘yan’uwan Ashiru Nagoma su ka yi an kai shi asibiti yanzu haka. Kuma kamar yadda mu ka yi alƙawari in-sha Allah za mu ci gaba da ɗaukar nauyin sa ƙarƙashin ƙungiyar mu ta Creative Helping Neddy Foundation.


“Ga wanda ya ke son taimaka masa zai iya kiran lambar ɗan’uwan sa Kabir Yusif 09060345731.”

Ashiru Nagoma (na 2 daga dama) tare da Fauziyya D. Sulaiman da 'yan'uwan sa
Likita ya na duba Ashiru Nagoma a Asibitin Malam Aminu Kano a yau

Loading

Previous Post

INEC za ta shigo da sababbin hanyoyin fasaha kafin zaɓen 2023

Next Post

Abin da ya sa zan riga ƙanwa ta, Rahama Sadau, yin aure – Abba Sadau

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Abin da ya sa zan riga ƙanwa ta, Rahama Sadau, yin aure – Abba Sadau

Abin da ya sa zan riga ƙanwa ta, Rahama Sadau, yin aure - Abba Sadau

Comments 10

  1. Ladidis weahave says:
    6 years ago

    ALLAH sarki. Allah ya bashi lahfiya yasa kaffara ne, Wallahi ni.har na manta da ashiru nagoma. Daraktan daraktochi. Allah ya baka Lahfiya, fauziyya Allah ya biyaki da Aljannah.

  2. Hayatu Dangaladima says:
    6 years ago

    Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ba shi lafiya don alfarmar fiyayyen talikai Annabi Muhammad SAW.

  3. Nura murtala says:
    6 years ago

    Allah yabashi lfy da sauran yan’uwa musulmi bakidaya wayanda basuda lfy

  4. MUSA USAINI GARA says:
    6 years ago

    allah sarki ashiru nagoma allah ya baka lafiya inama ina da arziki wallah bazan taba bari har wasu suji halin da kake ciki ba.

  5. Hawwa Mikail says:
    6 years ago

    Allah ya bashi lfy

  6. king samin bauchi says:
    6 years ago

    Allah yabaka lapiya ashiru nagoma nima danaga hoton sanda hankalina yatashi

  7. Hassan prince says:
    6 years ago

    Allah ya bashi lfy sukuma su fauziyya d sulaiman Allah ya biyasu da gidan aljannan fidausi ameen

  8. Rukaiya Abba says:
    6 years ago

    Allah yabashi lafiya

  9. Aliyu maitama Yusuf says:
    5 years ago

    A gaskiya fauziyya kin ciri tuta Allah ya sakamaki da alheri,wannan yanuna ‘yan’uwantaka da kaunar juna,Amma yakamata asan yadda za’a tallafa Masa yasamu kudi Dan ya inganta rayuwarsa da ya wasuma.

  10. abubakar Salisu danbare says:
    5 years ago

    Allahu akhbar Allah yabashi lpy, kuma duk wanda yake cikin irin wannan damuwa Allah kacire mishi Dan alfarmar rasulillahi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!