• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ba ja: Ahmad Sarari ya sake zama shugaban MOPPAN na ƙasa

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
January 29, 2022
in Labarai
0
Sabon shugaba, Dakta Ahmad Sarari, ya na gabatar da jawabi a babban taron MOPPAN na ƙasa jiya a Kano

Sabon shugaba, Dakta Ahmad Sarari, ya na gabatar da jawabi a babban taron MOPPAN na ƙasa jiya a Kano

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A WANI abu mai kama da ‘dakan ɗaka shiƙar ɗaka’, ‘yan takarar zama shugabannin Haɗaɗɗiyar  Ƙungiyar masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (Motion Picture Practitioners Association of Nijeriya, MOPPAN), su ne aka zaɓa babu hamayya jiya domin riƙe muƙaman su a tsawon shekaru uku masu zuwa.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa wanda ya sauka kwanan baya domin a sake yin zaɓe, Dakta Ahmad Muhammad Sarari, shi ne aka sake zaɓa a matsayin sabon shugaba.

Ƙungiyar dai ta gudanar da babban taron ta na ƙasa ne a daren jiya Juma’a, 28 ga Janairu, 2022 a ɗakin taro na otal ɗin Ni’ima da ke Kano inda aka zaɓi shugabannin.

Da fari, a Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa, aka tsara za a gudanar da taron da kuma zaɓen, amma sai aka taho Kano.

Wani sashe na mahalartan taron

An dai gudanar da babban zaɓen ne haɗi da taron wakilan ƙungiyar da ke sassan jihohin ƙasar nan, musamman na Arewa inda a nan ne ƙungiyar ta fi ƙarfi.

An gudanar da zaɓen a ƙarƙashin kulawar kwamitin amintattun ƙungiyar (Board of Trustees) wanda Alhaji Sani Mu’azu ya ke jagoranta tare kuma da kwamitin gyaran kundin tsarin mulkin ƙungiyar wanda Malam Khalid Musa ya ke jagoranta. 

Tun kafin a fidda sunayen sababbin shugabannin, sai da Alhaji Sani Mu’azu ya yi jawabi ga mahalarta taron, inda ya gode masu bisa haɗin kai da kuma ƙwazo da su ka nuna tun farkon kafa wannan ƙungiya har zuwa yau.

Ya ce, ”Sanin kowa ne wannan ƙungiya an ƙirƙire ta ne domin inganta sana’ar finafinai tare da ƙara tallata kyawawan al’adun mu. Me ya sa Nijeriya ta zama ƙasa ɗaya? A wajen gabatarwar mu, a wajen labaran mu akwai wata ingantacciyar hanya da mu ka bambanta da juna, shi ya sa MOPPAN ta zo don ta bayyana kyawawan ɗabi’un wannan yanki na Arewa.

”Daga lokacin da aka ƙirƙiri wannan ƙungiya, ta zo da ƙudirin ta na ganin cewa kowace jiha da ke Nijeriya an samar da wakilan da za su wakilci ƙabilun su, don haka ina cikin matuƙar farin ciki ganin yadda ƙungiyar ke ƙara bunƙasa.

”Na tuna lokacin da aka ƙirƙiri wannan ƙungiya, mun fara da jihohi uku da ke arewacin Nijeriya, waɗanda su ka haɗa da Jihar Kano, Kaduna da kuma Jihar Filato. Bayan wani lokaci, ƙungiyar ta ƙara faɗi da bunƙasa tare da samun daɗin jihohi irin su Katsina, Zamfara, Sokoto har ta kai ga Jihar Nasarawa da kuma Bauchi. 

Alhaji Sani Mu’azu ya na gabatar da jawabi

“Ana ci gaba da tafiya a haka har ya zo ga lokaci ya yi da ƙungiyar MOPPAN ta zagaya sassan jihohin arewacin Nijeriya haɗi da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

”Fatan mu shi ne ba wai ƙungiyar ta tsaya ga ƙasa Nijeriya ba, har ma da sassan duniya baki ɗaya.”

Sani Ma’azu ya kuma yi fatan cewa ba wai burin su ya tsaya iya ƙungiyar MOPPAN karan kan ta ba ne, ya na fatan za a faɗaɗa tunani wajen samar da wasu ƙananan ƙungiyoyin da za su haɗa da ƙwararru a fannoni da dama a ƙarƙashin MOPPAN, wato ‘Guilds’, kama daga ƙungiyar jarumai, furodusoshi, masu ɗaukar hoto, marubuta, masu tace finafinai, masu kwalliya da sauran su.

Ya kuma bayyana farin cikin sa bisa wannan karɓar baƙuncin wannan gagarumin taro wanda ƙungiyar ke gudanarwa duk bayan shekara biyu wanda gwamnatin Jihar Kano ta yi, kuma ya bayyana abin da ya sa ba a tafi Jihar Nasarawa ba.

Ya ce, ”Mun yi fatan wannan taron namu zai gudana a wata jiha ba Kano ba, saboda kafin Jihar Kano akwai jihohi guda biyu da su ka nuna sha’awar su na ganin sun karɓi baƙuncin MOPPAN da wakilan ta a wannan taron namu na bayan shekara biyu. To sai dai Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya alamtar da mu cewa, ‘Kar ku manta da cewa Jihar Kano ita ce cibiyar shirya finafinai ta arewacin ƙasar nan, amma masu shirya finafinai a wannan ƙasa su na guje wa Kano zuwa wasu garuruwan domin yin tarurrukan su ko ɗaukar finafinai a madadin a ce a Jihar Kano ake yi’.

”Don haka ya umarce mu da cewa kada mu je ko’ina mu yi wannan taro, mu zauna a Kano, ‘za mu karɓe ku, za kuma mu tabbatar da mun yi maku tarbar girma a wannan jiha’.

Malam Ahmad Salihu Alkanawy ya na gabatar da jawabi

“A nan, dole na jinjina tare da yaba wa gwamnan wajen ganin ya cika alƙawarin da ya ɗauka, a yau ga mu a Kano.”

Ya kuma ce, ”Baya ga wannan tarba da aka mana, gwamnan bai tsaya a nan ba, sai da ya haɗa wa MOPPAN da ‘ya’yan ƙungiyar wani yawon buɗe ido mai cike da ilimi. Mun nishaɗantu da wannan abu da aka mana.

“Baya ga wannan kuma, gwamnan zai jagoranci rantsar da zaɓaɓɓun shugabannin da aka zaɓa tare da gudanar da liyafar cin abincin dare da gwamnan da sauran wakilai da mambobin ƙungiyar’.”

A ƙarshe, ya yi wa kowa da kowa fatan komawa gida lafiya da yin zaɓe cikin adalci da kwanciyar hankali.

To sai dai baya ga kammala bayanin Alhaji Sani Mu’azu, shi ma Malam Khalid Musa ya miƙe domin karanto wa wakilan ƙungiyar wasu daga cikin gyararrakin da aka yi wa kundin tsarin mulkin ƙungiyar. 

An tafka muhawara tsakanin kwamitin gyaran da wakilan ƙungiyar na jihohi. Daga cikin dokokin da kwamitin ya gyara akwai:

• ƙarin wa’adin zangon mulki daga shekara biyu zuwa shekara uku;

• bai wa wasu jarumai da ba ‘yan Nijeriya ba damar shiga ƙungiyar;

• ƙara yawan kwamitin amintattu daga biyar zuwa tara;

• neman sahalewar yin aiki da kayayyakin da zamani ya zo da su, wanda a da sai dai a yi amfani da na Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (Nigerian Film Corporation); da kuma

• dokar da ta ce a duk lokacin da ƙungiyar ta lalace ko ta rushe kayan ƙungiya da ƙuɗin ƙungiya ba na wani mutum ba ne na jama’a ne gaba ɗaya.

Yawancin wakilan MOPPAN na jihohi sun amince da waɗannan da sauran wasu daga cikin dokokin da aka yi wa gyara.

Malam Khalid ya bayyana cewa da zarar kwamitin su ya kammala gyaran wannan kundi, za su miƙa shi ga Hukumar Rajistar Kamfanoni da Ƙungiyoyi (CAC) don tabbatar da shi.
 Daga nan, shugaban kwamitin shirya zaɓen ƙungiyar na bana, Malam Ahmad Alkanawy, da ya zo ya gudanar da zaɓen kamar yadda aka shirya, sai ya nuna cewa kaɗa ƙuri’u ba zai samu ba kamar yadda aka saba yi a dukkan wani zaɓe.

Alkanawy ya faɗa wa ‘yan ƙungiyar cewa, ”Kafin na fara cewa komai ina so na ba wa kowa haƙuri. Ina so na sanar da ku cewa wannan zaɓen na yau ya sha bamban da irin zaɓuɓɓukan da ake aiwatarwa a baya, domin kuwa abin da zan gaya maku idan kun aminta da shi shi kenan, idan kuma ba ku aminta ba sai mu ɗauko akwatin mu na zaɓe, da man mun tanade shi kawai jinkirta shi aka yi.

”Kafin shigowar mu wannan ɗaki, mun samu takarda daga hannun ‘yan takara cewa su na buƙatar ba sai an wahalar da kwamiti ba domin kuwa sun riga sun yi sulhu a tsakanin su, wasu sun haƙura sun bar wa wasu. Don haka kowa ba shi da abokin takara, wato abin nan a taƙaice kowa ya ci zaɓe babu hamayya. To amma fa idan kun yarda.”

Sababbin zaɓaɓɓun shugabannin MOPPAN

Bayan amincewar wakilan ƙungiyar na jihohi 19, Alkanawy ya bayyana sunayen ‘yan takarar da su ka samu nasarar hawa kujeru 13 ba tare da wani ya ja da su ba, kamar haka:

1. Dakta Ahmad Sarari daga Jihar Kano – Shugaban ƙungiya na ƙasa

2. Habibu Barde daga Abuja – Mataimakin Shugaba, Arewa ta Tsakiya

3. Ibrahim Amarawa daga Jihar Barno – Mataimakin Shugaba, Arewa Maso Gabas

4. Umar Maikuɗi (Cashman) daga Jihar Kaduna – Mataimakin Shugaba, Arewa Maso Yamma

5. Salisu Mu’azu, daga Jihar Filato – Babban Sakatare

6. Fatima Ibrahim Lamaj daga Jihar Kaduna – Sakatariyar Kuɗi

7. Umar Mohammed Gombe daga Jihar Kano – Mataimakin Babban Sakatare

8. Al-Amin Ciroma daga Jihar Kaduna – Jami’in Hulɗa da Jama’a.

9. Maijidda Abbas daga Jihar Kaduna – Jami’ar Kula da Walwala

10. Haladu Muhammad daga Jihar Neja – Sakataren Tsare-tsare

11. Mustapha Naburaska daga Jihar Kano – Mataimakin Jami’in Hulɗa da Jama’a

12. Ibrahim l. Ibrahim a daga Jihar Nasarawa – Mai Binciken Kuɗi na 1

13. Bello Achida daga Jihar Sokoto – Mai Binciken Kuɗi na 2.

Wani sashen mahalarta taron a Kano jiya

Ana sa ran gwamnan Jihar Kano ne zai jagoranci rantsar da shugabannin a yau Asabar, 29 ga Janairu, 2022 a babban ɗakin taro na Coronation da ke cikin Gidan Gwamnatin Kano.

Loading

Previous Post

‘Yan Kannywood sun kai ziyarar ta’aziyyar rasuwar Hanifa Abubakar

Next Post

Gwamna Ganduje ya naɗa Malam Khalid da Nabraska jakadun Kannywood a gwamnati

Related Posts

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta
Labarai

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta

June 23, 2025
Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima

June 22, 2025
Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau
Labarai

Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau

June 22, 2025
Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji

June 22, 2025
Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano
Labarai

Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano

June 20, 2025
Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza
Labarai

Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza

June 20, 2025
Next Post
Daga hagu: Malam Khalid Musa da Alhaji Mustapha Nabraska

Gwamna Ganduje ya naɗa Malam Khalid da Nabraska jakadun Kannywood a gwamnati

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!