• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, October 13, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamna Ganduje ya naɗa Malam Khalid da Nabraska jakadun Kannywood a gwamnati

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
January 30, 2022
in Labarai
0
Daga hagu: Malam Khalid Musa da Alhaji Mustapha Nabraska

Daga hagu: Malam Khalid Musa da Alhaji Mustapha Nabraska

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNAN Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya naɗa ɗaya daga cikin dattawan masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Malam Khalid Musa, a matsayin mai taimaka wa gwamna kan masana’antar Kannywood, kuma ya naɗa fitaccen jarumin barkwanci, Alhaji Mustapha Nabraska, a matsayin mai taimaka wa gwamna kan farfaganda.

Naɗe-naɗen sun biyo bayan buƙatar da Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (Motion Picture Practitioners Association of Nigeria, MOPPAN) ta yi masa na ya samar da wani jakada tsakanin gwamnatin sa da masana’antar.

Hakan ta faru ne a daren jiya Asabar, 29 ga Janairu, 2022 lokacin da gwamnan ya jagoranci taron rantsar da sababbin shugabannin ƙungiyar na ƙasa da aka zaɓa a ranar Juma’a, tare da haɗa masu liyafar cin abincin dare da aka yi a Gidan Gwamnati.

A jiyan ne kuma aka rantsar da sababbin shugabannin ƙungiyar su 13 a babban ɗakin taro na ‘Coronation’ da ke gidan gwamnatin. 

Shugabannin sun karɓi rantsuwar kama aiki tare da yin alƙawarin gudanar da aikin su kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙungiyar da ma na ƙasa baki ɗaya su ka tanada.

Jim kaɗan bayan kammala rantsuwar, gwamna ya jagoranci ‘yan ƙungiyar zuwa ɗakin cin abincin da ke cikin gidan gwamnati domin cin abincin dare tare da gwamna.

Jim kaɗan bayan kammala liyafar, an tattauna abubuwa da dama da su ka jiɓinci cigaban MOPPAN.

Ana rantsar da sababbin shugabannin MOPPAN na ƙasa

Babban sakataren kwamitin amintattu (Board of Trustees) na ƙungiyar, Alhaji Sani Mu’azu, ya miƙe ya gabatar da jawabin sa cikin salon godiya da yabawa ga gwamnan bisa wannan karramawa. Haka kuma ya bayyana wasu buƙatu da su ke neman alfarmar gwamnatin jihar ta yi masu.

Ya ce, ”Haƙiƙa mu na yaba wa gwamna bisa irin manyan ayyukan cigaba da ya ke aiwatarwa a Jihar Kano.

“Mu a matsayin mu na masu yin fim, mu na zaga jihohin ƙasar nan, amma a yau na tabbatar da cewa Jihar Kano ta samar mana da abin da za mu iya nunawa mu ma a duniya na ci gaba wanda kuma zai taimaka mana wajen rage zuwa wasu garuruwan ko ƙasa neman wurin ɗaukar fim.

Ana miƙa wa Gwamna Ganduje kyautar karramawar sa

”A zagayen da aka yi da mu a wannan jihar, mun ga abubuwa da dama, ciki har da abin da ya ɗauki hankali na, wato wajen koyar da sana’a na ‘Ɗangote Skills Acquisition Centre’. Wannan wuri, maganar gaskiya, zai taimaka wajen samar wa da matasa ayyukan yi, don na zaga na ga ɓangarori da dama da mata sa za su ƙaru da wannan wuri.

“Haka kuma an kai mu cibiyar masu kula da ciwon kansa wanda duk Afrika babu irin sa, wanda yanzu haka mu ka ga ana gudanar da aiki a cikin sa.

“Wannan abin cigaba ne da yabawa ƙwarai da gaske a gefe guda kuwa ga gadojin zamani da ake yi wa wannan jihar da sauƙaƙawa al’umma wajen sufuri”

Gwamna Ganduje ya na gabatar da jawabi ga taron na MOPPAN

Daga nan Sani Ma’azu ya gabatar wa da gwamna wasu daga cikin buƙatun Kannywood, ya ce, ”Mu ana so mu ma ‘yan Kannywood a yi mana alfarma wajen samar da wani ɓangare a cikin waccan santar ta koyar da sana’o’i da zai dinga koyar da matasa yadda za su dinga sarrafa na’urar ɗaukar hoto da murya, wato ‘cinematography’, da kuma koyar da su yadda ake tace hotuna.

”Mu na neman alfarmar a ba mu damar shiga irin waɗannan wuraren domin ɗaukar fim ɗin mu don wuri ne da idan aka tsara labari zai dace da irin wuraren da mu ke zuwa mu yi fim a ƙasashen Turai; ko ni idan na tsara fim ko ɗan kallo ba zai ce a nan ƙasar aka ɗauka ba”.

Ya ƙarƙare da neman gwamnati da ta samar masu da wani tsani da zai dinga haɗa gwamnati da ‘ya’yan ƙungiyar.

A nasa ɓangaren, sabon shugaban ƙungiyar MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, shi ma ya yi jawabin godiya a taƙaice tare da bayar da taƙaitaccen tarihin ƙungiyar da yadda ta faro har zuwa yau.

Shugaban MOPPAN, Dakta Ahmad Sarari, ya na kai caffa ga Gwamna Ganduje a lokacin taron

Haka kuma ya ba gwamnati tabbacin goyon baya daga ƙungiyar.

Da ya ke maida jawabi, Gwamna  Ganduje ya yaba wa membobin MOPPAN bisa damar da su ka bai wa jihar ta gudanar da babban taron su a cikin ta tare da gudanar da zaɓe lafiya.

Ya ce: ”Babu shakka, wannan taro da ku ka yi a Kano dole a kira shi da an yi nasara a kan wannan taro, bayan ma zaɓe da aka yi lami lafiya aka samu shugabanci. 

“Sannan kuma kun samu an tattauna abubuwan da su ka shafi wannan sana’a, sannan uwa-uba kun daɗa matsowa kusa da gwamnati yadda za a ƙara samun danƙon zumunci da kuma taimaka wa juna; shi kan sa wannan babban abu ne sosai da sosai.

”Na ji daɗi kwarai da gaske da ku ka samu dama ku ka zagaya ku ka ga wasu daga cikin ayyukan mu kuma ku ka yi sharhi a kan abin da ku ka gani domin duk ayyukan mu an yi su da ilimi, da tunani da hangen nesa da lissafi, domin mu mun dogara a kan sani da ilimi. 

Wani sashe na mahalarta taron a ‘Coronation Hall’

“Saboda haka, duk abin da za mu yi sai mun yi bincike a kai, don gwamnatin mu ba gwamnatin awon igiya ba ce.”

Gwamnan ya yi alƙawarin zai taimaka wa MOPPAN kamar yadda ta nema. Ya ce, ”Kamar yadda ku ka buƙaci da a taimake ku, to in Allah ya yarda mu abin da mu ke buƙata kuma mu ke so shi ne buƙata ta hankali, buƙata ta tsari, buƙata ta ilimi, ba buƙatar awon igiya ba, abin da zai yi amfani ba wai buƙatar sama da faɗi ba.

”Don haka sai a rubuto mana, sai mu zauna a duba a gani. Ba shakka, mu na so mu taimaka maku kamar yadda mu ke faɗa, ko wata cibiya haka ko aikawa da mutanen ku zuwa ƙasashen da su ka ci gaba a harkar fim kamar Indiya wanda sun yi nisa, duk gwamnati za ta taimaka a wannan.”

A nan take sai gwamnan ya bayyana naɗin Malam Khalid da Nabraska.

Lokacin cin abinci a daren jiya

Gwamnan ya ƙarƙare da yi wa baƙi addu’ar komawa garuruwan su lafiya.

A ƙarshe, MOPPAN ta karrama Gwamna Ganduje da maiɗakin sa, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje.

Loading

Tags: Dr Ahmad SarariFarfesa Hafsat GandujeGwamna Abdullahi Umar GandujeKano State GovernmentMalam Khalid MusaMOPPANMotion Picture Practitioners Association of NigeriaMustapha NabraskaSani Mu'azu.
Previous Post

Ba ja: Ahmad Sarari ya sake zama shugaban MOPPAN na ƙasa

Next Post

Aure: Hauwa Rafin Guza ta shiga ɗakin ta

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Amarya Hauwa'u Abubakar a ranar auren ta

Aure: Hauwa Rafin Guza ta shiga ɗakin ta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!