• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, October 9, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Batun Gwanja: In gaskiya ne, NBC ta soke soshiyal midiya mana – mawaƙi Ɗayyab Maiɗa’a

by DAGA ABBA MUHAMMAD
September 8, 2022
in Labarai
0
Ɗayyab Hassan (Maiɗa'a)

Ɗayyab Hassan (Maiɗa'a)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN mawaƙi a Kannywood, Ɗayyab Hassan, wanda aka fi sani da Maiɗa’a, ya ce idan da gaske Hukumar Kula Da Gidajen Rediyo da Talbijin ta Nijeriya (Nigerian Broadcasting Corporation, NBC) ta ke yi, to ta dakatar da saka waƙoƙin Ado Gwanja a soshiyal midiya.

Ɗayyab ya yi waɗannan kalamai ne a lokacin da ya ke zantawa da mujallar Fim, bayan hukumar ta ba da umarnin dakatar da saka waƙar ‘Warr’ a gidajen rediyo da talbijin.

Mawaƙin ya ce, “Da ya ke hankali ya koma kan Ado Gwanja, wallahi wannan sam ba adalci aka yi wa kafafen yaɗa labarai ba, sai ma rainin wayo da ake nuna wa mutanen Arewa.”

Ya ci gaba da cewa, “Wallahi mawaƙan Turanci sun fi mu rashin mutunci da waƙoƙin su marasa ɗa’a.

“Idan ka duba, za ka ga suna da yawa. A nawa fahimtar, kawai ana so a nuna wa duniya cewa mu mawaƙan Arewa ba mu da tarbiyya ne. Kuma wannan al’amari kaf mutanen arewacin ƙasar nan zai shafa.

“Ni ba na goyon bayan Ado Gwanja na ke yi ba sam, amma ina aka kai mawaƙan (kudancin) Nijeriya marasa tarbiyya masu nuna tsiraici da nuna baɗala?

“Waɗannan waƙoƙi ana ganin cewa kamar ba za su ɓata mana tarbiyyar yara masu tasowa kamar ƙanne, ‘ya’ya da sauran su ba? Ko ana ganin ba za a riƙa motsa masu sha’awa ba ne?”

Ɗayyab Maiɗa’a ya ce, “Idan ka na mawaƙin Arewa, ba ka da galihu; duk abin da ka yi komai, ƙanƙantar sa, idan ya samu karɓuwa shi kenan ka zama mai lalata tarbiyya.

“Abin da ake tunanin Gwanja ya yi akwai ƙuruciya a cikin sa, ko kuma in ce akwai jahilci, ba ina nufin jahili ba ne, a’a, duk abin da ba ka da ilimin sa kai jahilin sa ne, in fa bai sani ɗin ba kenan.

“Wannan waƙa ta ‘Warr’ ko da an hana saka ta a gidajen talbijin da gidajen rediyo, to fa ta zama gwal a sana’ance, domin yanzu a TikTok, Instagram, Facebook, WatsApp da sauran su ake kallo yayin da komai ƙanƙantar waya za ta biya wa kowa buƙatun sa kowane iri.

“Idan gwamnatin Nijeriya ta na so ta burge, to ta rufe kafafen sada zumuntan na zamani, shi ne mafita, kuma shi ne zaman lafiya a kan dukkan makircin masu yaɗa farfaganda da sauran abin da ke kawo mana matsalolin rayuwa.”

Loading

Tags: Ado Gwanjadokamawaƙamawaƙan kuduNBCTarbiyya
Previous Post

Haramcin waƙa ta: Na yi gum, ba zan ce komai ba yanzu, inji Gwanja

Next Post

Zaɓen 2023: Fiye da mutane miliyan 3 za su yi zaɓe a sansanin ‘yan gudun hijira – INEC

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post

Zaɓen 2023: Fiye da mutane miliyan 3 za su yi zaɓe a sansanin 'yan gudun hijira - INEC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!