• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Bayan auren Rahama Sadau, ido ya koma kan Gabon, Nafisat, Washa, Amal da wasu ‘yan matan na Kannywood 

by ABBA MUHAMMAD
August 11, 2025
in Labarai
0
Bayan auren Rahama Sadau, ido ya koma kan Gabon, Nafisat, Washa, Amal da wasu ‘yan matan na Kannywood 

Fati Washa, Hadiza Gabon, Nafisat Abdullahi, Hauwa Ayawa, Amal Umar, da Maryam Yahaya

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
SAKAMAKON auren ba-zata da Rahama Sadau ta yi, yanzu hankalin mutane ya koma kan sauran fitattun ‘yan fim mata waɗanda ba su taɓa yin aure ba.
Ita dai Rahama, ta ba kowa mamaki da ta yi aure kwatsam ranar Asabar da ta gabata, domin babu wanda ya kawo mata aure a daidai wannan lokaci. Hasali ma dai, da yawa sun ɗauka ba auren ta saka a gaba ba.
Don haka da ta yi auren sai ta burge kowa, ana ta taya ta farin ciki da fatar alheri.
To sai dai kuma da ta yi auren sai sunayen wasu jaruman suka fara yawo a soshiyal midiya, su ma ana yi musu irin kallon da aka taɓa yi mata na cewar ba aure ne a gaban ta ba.
Jaruman sun haɗa da:
  • Hadiza Gabon
  • Nafisat Abdullahi
  • Fatima Abdullahi (Fati Washa)
  • Fati Yola
  • Amal Umar
  • Maryam Yahaya
  • Maryam Booth
  • Fati S.U. Garba
  • Hauwa Ayawa
  • Surayya Aminu
  • Hannatu Bashir (Hanan)
  • Hajara Isah Jalingo
  • Samira Saje
  • Hannatu S. Usman,
  • Bilkisu Wada Shema
Ban da ‘yan wasa, su kan su mawaƙan industiri ba su tsira daga wannan kallon ba, musamman fitattun matasan cikin su irin su Khairat Abdullahi, har ma da Sadiya Yarima da Fati Nijar wadanda sun taɓa yin auren.
Babban dalilin da ya sa ake ganin kamar ‘yan fim mata ba su so su yi aure, a binciken da mujallar Fim ta yi, shi ne yadda aka ga suna fantamawa da manyan gidaje da motocin alfarma da tsadaddun tufafi, da kayan alatu irin su babbar waya.
Hakan ya sa wasu suke ɗaukar cewa matsayin matan ya wuce su auri talaka, kuma wataƙila wannan ne ke hana su samun miji ko dai saboda tsadar rayuwar su ko kuma ƙalubalen samun wanda zai dace da matsayin su da ɗaukar nauyin su.
Jaruman sukan yi tseren nuna irin abin duniya da suka mallaka ko wuraren da suka je. Akan ga wasun su a manyan otal-otal ko biranen ƙasashen duniya irin su Masar, Dubai, Saudiyya, Istanbul, Rome, Paris, London, New York, da sauran su. Matan da aka gani a waɗannan ƙasashe a ‘yan shekarun nan sun haɗa da Rahama Sadau, Nafisat Abdullahi, Fati Washa, Maryam Yahaya, da Hadiza Gabon.
Wasu masu nazarin lamarin sun faɗa wa mujallar Fim cewa irin wannan nuna wadata da shahara yana sanya ‘yan matan Kannywood rasa damar samun miji da sauri, domin duk wanda ya yunƙuro sai ya yi tunanin anya zai iya da su kuwa?
A cewar wani, “Tunda suna da komai, me zai sa su damu da aure?”
Fati Yola, Hajara Isah Jalingo, Bilkisu Wada Shema, da Hannatu Bashir
Sai dai kuma, auren kwatsam na Rahama Sadau ya karya wannan zato. Ko da mutane da dama sun ɗauka ba za ta yi aure ba saboda shaharar ta da bayyana irin kuɗaɗen ta da rayuwar alfarma, sai ga shi wani mai suna Ibrahim Garba ya yi wuf da ita farat ɗaya. Wannan ya haifar wa da ‘yan matan kyakkyawar fatar cewa duk da wadata da shaharar su ko daɗewar su a industirin, suna da masoyan da ke son su da aure, kuma suna iya yin auren a kowane lokaci idan suka yarda.
Wani wanda ya yi nazarin lamarin ya ce wani abu da ke sa mata ‘yan fim su ƙi yin aure da wuri shi ne ruwan ido – wato su gaza fidda miji a cikin masu son su.
A cewar wata jaruma: “Lamarin Rahama ya zama darasi cewa ba za ka iya sanin yadda tafiyar rayuwar mutum za ta kaya ba. Aure abu ne da ke zuwa a lokacin da ya dace, ba bisa hasashen jama’a ba. Idan Rahama ta iya, babu wani abin mamaki idan gobe ko jibi mu ka ji wata daga cikin waɗannan jarumai ta shiga gidan aure.”
Ga jerin wasu hanyoyi da ‘yan matan Kannywood za su bi don ganin sun yi aure cikin sauƙi da kwanciyar hankali:
1. Rage bayyana sirrin rayuwa a idon jama’a. Wasu jarumai suna bayyana komai na rayuwar su a kafafen sada zumunta, wanda hakan kan sa mutane su ji tsoro ko jin ba za su iya kaiwa matsayin su ba. Yi wa sirri hijabi zai sa damuwar jama’a ta ragu.
2. Kula da dangantaka a bayan fage. Kamar yadda Rahama ta yi, haɗa soyayya da aure cikin sirri yana iya taimakawa wajen guje wa maganganu kafin lokacin.
3. Samar da hanyar hulɗa da masu niyya. Haɗuwa da mutane ta hanyar abubuwan jin daɗi na al’umma, tarurrukan jama’a, ko ayyukan alheri na iya buɗe ƙofa ga haɗuwa da masoyin aure.
4. Rage hasashen jama’a. Idan jaruman za su iya nuna a zahiri cewa suna da ra’ayin aure kuma suna maraba da shi, hakan zai canza tunanin da ake yi musu na “ba sa buƙatar aure.”
5. Zaɓar masoyi bisa ƙa’ida ba mulki. Wani lokaci ana tsammanin matan fim za su auri mai kuɗi ko babban mutum kawai, amma zaɓar wanda ya dace da hali da zuciya na iya kawo farin ciki mai ɗorewa.
6. Rage tallar kai a soshiyal midiya. Yawan bayyana surar jiki ko fuska a soshiyal midiya, musamman cikin ƙananan kaya, yakan sa wasu su ɗauka cewar ‘yan matan Kannywood ba kintsattsu ba ne. Don haka ko da mutum ya yi niyyar auren su sai iyaye ko dangin sa su hana.
A ƙarshe, an san aure haɓo ne, idan lokacin sa ya yi sai ka ga an yi shi ba makawa. Mun gani kwanan nan a auren Rahama Sadau. Amma fa Hausawa sun ce idan kana da kyau, ka ƙara da wanka.

Loading

Tags: aurejarumaiKannywoodmataRahama Sadau
Previous Post

Ranar Al’adu ta Duniya: Gwamnan Kano na so a yi riƙo da al’adun gargajiya

Next Post

Mawaƙi a Kannywood, TK ya yi rashin babban ɗan sa Isma’il

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Mawaƙi a Kannywood, ya yi rashin babban ɗan sa Isma'il

Mawaƙi a Kannywood, TK ya yi rashin babban ɗan sa Isma'il

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!