JARUMIN Kannywood da ake ganin ya fi kowane ɗan fim kusanci da zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wato Abba El-Mustapha, ya bayyana cewa sabuwar gwamnatin da za a kafa za ta tafi tare ‘yan fim duk da yake yawancin su sun yi adawa da takarar sa.
El-Mustapha ya faɗi haka ne a lokacin da ya ke tattaunawa da mujallar Fim game da canjin gwamnati da aka samu da kuma irin kallon da su ke yi wa sabon gwamnan.
El-Mustapha ya ce: “To, alhamdu lillahi, wannan nasara ce da ta zo wa jama’ar Kano da masana’antar Kannywood da ma jama’ar ƙasa baki ɗaya, saboda in aka ce Kano ana maganar Hausa baki ɗaya, don nan ce cibiya.
“Kuma kamar yadda kowa ya sani ne, Jihar Kano ta zama koma-baya a kan abubuwa da dama.
“Kuma a game da masana’antar Kannywood, kowa ya ga yadda ta tsaya cak ta koma ziro, wanda hakan ya sa mu ka ga mu ma sai mun fito mun ba da gudunmawa an yi harkar nan da mu. Kuma a yanzu alhamdu lillah, Allah ya kawo mu ga cin nasara a yanzu. Kuma ko babu komai mun samu darussan rayuwa a yanzu. Amma dai abin da ya fi zama darasin shi ne mutum ya tsaya a kan aƙidar sa ta gaskiya, ta kasance ta taimakon al’umma ce, ta ina za a cicciɓa jama’a su yi gaba, to ka tsaya a nan wajen.
“Kuma wani darasi babba da na samu na kuma yarda da shi shi ne haƙuri. Don haka in dai ka yi haƙuri a rayuwa, to nasara za ta zo maka, don haka duk in da ka tsaya kuma ka bi abin da jama’a su ke so, to in-sha Allah darajar ka za ta ɗagu, ƙimar ka za ta ƙaru. Sannan kuma ka na bai wa jama’a gudunmawa ba wai don wani abu da za a ba ka ba.”
Da mu ka tambaye shi yadda mafi yawan ‘yan fim sun ƙi tafiyar Kwankwasiyya a wannan zaɓen, sai El-Mustapha ya ce: “To ni na sha faɗa a duk lokacin da aka tambaye ni, cewa an kassara mana harkar fim har ta kai matakin ziro wadda babu wata mamora a cikin ta, su kuma waɗanda su ka rage ‘yan kaɗan a ciki bayan an kashe ta, duk da yake mu ‘yan fim mu na cikin waɗanda mu ka bayar da gudunmawa wajen kafuwar gwamnatin, amma sai aka wofantar da harkar aka bar mu, aka ƙi tallafa mana. Sai ya zama babu wani abu na gwamnati da ya zo aka mayar da mu mutane. Wannan sa kasuwar babu ita, harkar fim duk ta tashi ta koma ‘online’. Abin ya yi tsamari da tsanani, kuma dole sai mutum ya nemi abinci da harkar tunda ita aka sani.
“To wannan sai ya zama dole sai ka bi gwamnati ka je ka na ta raragefe, su ba ka ɗan tallar da za ka samu ka ciyar da iyalan ka.
“Don haka ban ga laifin ‘yan fim da su ka koma su ka bi gwamnati ba, saboda su na samo ‘yar tallar da su ke ciyar da iyalan su, saboda gwamnatin ba za ta ba ka kuɗin ba sai ka yi mata talla, idan ka yi mata sai ta ɗan tsakuro abu ta ba ka. Wannan ya sa duk ‘yan fim suka bi gwamnati.
“To mu kuma ɓangaren da mu ke Allah ya gani na cigaban jama’a ne da neman cigaban ta, kuma kowa ya san ba gwamnati ce a hannun su ba. Azumi ake yi, dai ka yi haƙuri da ɗan abin da ka ke samu. Haka aka ci gaba da yaɗa manufa har jama’a su ka karɓa har zuwa matakin nasara da mu ka samu a yanzu, wanda na ke yi wa mutane albishir, domin a yanzu mafi yawan ‘yan fim da su ka tafi su ka ɓata tafiyar a yanzu sun fara dawowa.
“Kuma billahil lazi nan da ɗan wani lokaci duk za ka gan su duk sun dawo. A baya idan ana yi mana dariya, a yanzu mun zama abin sha’awa. Wannan kuma kishin jama’a ne da riƙo da gaskiya ya kawo mu ga haka.
“Kuma ni na fada: duk wani ɗan fim ɗan Kwankwasiyya ne, domin ita ce ta yi masa gatan da aka san cewa shi mai sana’a ne. Ta samar masa da Hukumar tace Finafinai, hakan ya kyautata alaƙa tsakanin ‘yan fim da gwamnati. Sannan aka bayar da tallafa na kuɗi da na karatu duk a gwamnatin Kwankwasiyya, kowa ya san an ɗauki ‘yan fim an kai su ƙasashen waje irin su Indiya da sauran kasashe domin ƙaro ilimi a kan harkar fim. Sannan aka samar da wasu kwasakwasai a Jami’ar Maitama Sule, ga kuma makarantar da aka samar a Tiga. Don haka ina tabbatar maka babu wani ɗan fim da ba ɗan Kwankwasiyya ba, an dai tafi can ne, don a ɗan samu abin da za a ci.”
El-Mustapha ya yi tsokaci kan yadda ‘yan fim su ke dawowa tun lokacin da a sanar da cewa Abba Kabir Yusuf ya ci zaɓe cewa ya yi: ” Mu da man tsarin mu shi ne duk wanda zai taimaki jama’a to ya shiga cikin mu da man namu ne.

“Amma idan ka na tunanin an kafa gwamnati ne za ka zo ka ci daɗi, to mu na jiran ka. Mun san da yawa mutane ba sa son zama a wajen da ba a yi nasara ba. Mutane sun fi neman a ina nasara ta ke, don haka sun ga an samu nasara ga su nan su na ta faɗowa. Sai dai su sani wannan tafiya ce ta daraja, ta kishin jama’a don cigaban jama’a.”
Da muka tambaye shi ko wane irin sauyi su ke son gani a masana’antar Kannywood bayan kafa gwamnati kuwa, cewa ya yi, “Ai mu na da ƙudirori da dama. Kuma mu da muke zaune kusa da shi, mun san yadda mu ke tattaunawa da shi, don haka ban taɓa ganin gwamna da ya ke son ‘yan fim kamar Abba Kabir Yusuf ba don kamar yadda, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya ke son ‘yan fim, to haka shi ma Abba Kabir Yusuf ya ke son mu da kuma ƙudirin taimaka mana, saboda haka ya san kowa kuma mu na zama da shi da kuma yadda ya ke kallon yadda mu ke gudanar da sana’ar mu tare da tunanin in an samu gwamnati ga yadda za a bi a inganta harkar yadda kowa zai ji daɗin harkar. Don haka mu na da tsari a rubuce dangane da masana’antar Kannywood, ba ma yin abu da ka, kuma gwamnati a shirye ta ke ta yarda mu ‘ya’yan ta ne, kuma sanin kowa ne in aka inganta harkar fim an inganta cigaban matasan Jihar Kano.
“Don haka ina kira ga Jama’a da su yi fatan alheri da kuma addu’a ga wannan sabon gwamna, Abba Kabir Yusuf, da Allah ya ba shi nasara. Don ba don wayon mu ba ne, Allah ne ya ga dama ya ƙwaci mulkin ya ba mu, don haka sai mu taya shi da addu’ar Allah ya dafa masa kada ya bar shi da iyawar sa. Allah ya haɗa shi da mashawarta na kirki yadda zai kai Jihar Kano zuwa mataki na cigaba.”