* Rasuwar Alhaji Sani Labaran babban rashi ne ga Jihar Gombe baki ɗaya, inji tsohon gwamna, Ibrahim Ɗanƙwambo
FITACCEN jarumi Umar Gombe ya bayyana cewa ya na alfahari da mahaifin sa, Alhaji Sani Labaran, wanda Allah ya yi rasuwa jiya.
Ya ce ya na alfahari da shi ne saboda ilimi da tarbiyyar da ya ba shi.
Haka kuma ya gode wa dukkan ‘yan fim da su ka yi masa ta’aziyya tare da yi wa mahaifin nasa addu’a.
Kamar yadda mujallar Fim ta bada labari jiya, Alhaji Sani Labaran ya rasu ne a jiyan, wato Talata, 16 ga Nuwamba, 2021, tare da bayyana cewa za a yi jana’izar sa a yau a Gombe.
Umar Gombe ya faɗa wa mujallar Fim cewa mahaifin nasa, wanda ɗan kimanin shekara 94 ne, ya rasu da misalin ƙarfe 4:05 na yamma a Asibitin Gwamnatin Tarayya, wato ‘Federal Medical Centre’, da ke garin Gombe, sakamakon ciwon ajali.



An yi jana’izar sa a yau Laraba da misalin ƙarfe 10:00 na safe a babban masallacin Juma’a da ke gidan Sarkin Gombe.
Alhaji Labaran, wanda ya na daga cikin sanannun dattawan Jihar Gombe, ya rasu ya bar mata uku da ‘ya’ya 22, kuma Umar ne na 12 a cikin su.
Da wakilin mu ya tambayi jarumin abin da zai ce game da wannan babban rashi da ya yi, sai ya ce, “Ba na so in yi kuka, amma kamar wannan magana na so ta sa ni kuka. Ina fata kamar yadda mahaifi na ya jiƙai na a lokacin da na ke yaro har zuwa girma na, Allah ya jiƙan shi.
“Kamar yadda na yi wa hira a baya, ina faɗa kullum ina alfahari da mahaifi na. Ina alfahari da shi sosai saboda ilimi da tarbiyyar da ya ba ni.”
Umar ya ƙara da cewa, “Alhamdu lillahi, na rayu rayuwa sosai da mahaifi na. Ya ilimantar da ni, ya tarbiyyatar da ni, kuma ya yi min komai na rayuwa.
“Babu abin da zan ce sai dai in ce Allah ya jiƙan shi da rahama, ya kuma jiƙan sa kamar yadda ya jiƙai na ina yaro.
“Haka kuma ina alfahari da ‘yan fim, kamar yadda na ke alfahari da ‘yan’uwa na. Domin idan ka duba tun daga ‘A to Z’ na Kannywood babu wanda bai ɗora hoton mahaifi na a shafin shi na soshiyal midiya ya yi masa addu’a ba, haka kuma babu wanda bai kira ni ta waya ya yi min ta’aziyya tare da yi wa mahaifi na addu’a.
“Babu abin da zan ce masu sai godiya. Ku ma ina yi maku godiya.”
Tsohon gwamnan Jihar Gombe, Dakta Ibrahim Hassan Ɗanƙwambo, ya na daga cikin manyan mutanen jihar da su ka aika da saƙon ta’aziyya.
Ɗanƙwambo ya yi ta’aziyya kamar haka: “Inna Iillahi wa inna ilaihi raji’un! Abin da Allah ya bayar nashi ne, wanda ya karɓa ma nashi ne, kuma kowane ya na da ƙayyadadden lokaci a wajen Allah.
“Cikin alhini da tsananin kaɗuwa na samu labarin rasuwar ɗaya daga cikin dattawan mu na Jihar Gombe, Alhaji Sani Labaran, wanda Allah ya karɓi rayuwar sa a yammacin jiya Talata.
“Marigayi Alhaji Sani Labaran dattijo ne wanda ya yi rayuwa abin koyi ga na baya, ya sadaukar da rayuwar sa wajen hidimta wa jama’a da kuma ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’umma.
“Tabbas, rasuwar wannan dattijo babban rashi ne gare mu baki ɗaya.
“A madadin ni kai na da iyalai na, ina miƙa ta’aziyyar mu ga iyalai da ‘yan’uwan wannan dattijo da sauran jama’ar Jihar Gombe baki ɗaya.
“Ina roƙon Allah (swt) ya jiƙan sa, ya gafarta masa, ya sa Aljannah Firdausi ce makomar sa. Ameen.”
A tasa ta’aziyyar, Ministan Sadarwa da Fasahar Zamani, Sheikh Isa Ali Pantami, ya faɗa cewa: “Allah Ya dauki rayuwar ɗaya daga cikin iyayen mu kuma aminin iyayen mu, a Jihar Gombe, shi ne Alhaji Sani Labaran.
“Allah Ya gafarta masa, Ya masa rahama, Ya kyautata makwancin sa, da na sauran iyayen mu da malaman mu, da ‘ya’yan mu.
“Allah Ya kyautata namu bayan na su.”
Pantami ya wallafa saƙon ne a Facebook tare da hotuna guda huɗu da ya ɗauka da mamacin a falon sa, lokacin da ya kai wa shi Alhaji Sani wata ziyara a gida.
Dubban mutane sun ci gaba da yi wa marigayin addu’a.