• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cin zarafin Musulunci: Ali Nuhu da sauran ‘yan Kannywood sun yi tir da mawaƙi Davido

by DAGA ALI KANO
July 23, 2023
in Labarai
0
Saƙon da Ali Nuhu ya wallafa a Instagram kan Davido

Saƙon da Ali Nuhu ya wallafa a Instagram kan Davido

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMI Ali Nuhu da wasu ‘yan masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood sun yi Allah-wadai da mawaƙin Turanci Davido saboda cin mutuncin da ya yi wa addinin Musulunci.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa Davido, wanda ɗan Kudu ne kuma Kirista, ya wallafa bidiyon waƙar wani sabon mawaƙi da ya ɗauka a kamfanin sa mai suna Logos Olori inda ya ci zarafin Musulunci a waƙar sa ta ‘Jaye Lo.’

Kamfanin kaɗe-kaɗe mallakar Davido, wato Davido Music Worldwide (DMW), shi ne ya ɗauki nauyin buga wa Logos Olori sabon faifan waƙar tasa tare da fitar da ita. 

Logos Olori ya saki bidiyon wannan waƙar tasa, wadda ita ce ta farko da ya rera, a soshiyal midiya a shekaranjiya Juma’a, 21 ga Yuli, 2023.

A guntun bidiyon, an nuno shi ya na waƙa a kan rufin masallaci yayin da wasu Musulmi su ke sallah kan tabarmi a harabar masallacin, wai kuma can sai daɗin kiɗan waƙar ya kama su, sai su ka daina sallar, su ka shiga taka rawa.

Musulmi da dama, ciki har da ‘yan fim, sun kalli abin da Logos Olori ya yi a matsayin cin mutuncin Islama, kuma sake wallafa waƙar da Davido ya yi a Twitter da Instagram ya ƙara tunzura su.

Masallaci ya na daga cikin wurare tsarkaka a Musulunci, kuma Musulmi ba su ɗauke shi wurin wasa ko abin wasa ba.

A shafin sa na Instagram, Ali Nuhu ya ce abin da Davido ya yi “ba a amince da shi ba ko kaɗan a Musulunci.”

Ali ya yi kira a gare shi da ya cire bidiyon kuma ya ba Musulmi haƙuri saboda “baƙanta” masu rai da ya yi.

Abin da jarumin ya rubuta da Turanci shi ne: “I just came across the controversial video by @davido, as much we want to be creative in our various fields, we should learn to respect other people’s religion, culture and tradition.

“This is totally unacceptable in Islam. You should pull down that video and apologise for hurting the entire Muslim ummah.”

Mujallar Fim ta fassara rubutun nasa kamar haka: “Yanzun nan na ci karo da bidiyon da ya tayar da ƙura wanda @davido ya tura, duk yadda mu ke son mu nuna basira a ayyukan da mu ka sa a gaba, dole ne mu san yadda za mu riƙa girmama addini da al’adu da ɗabi’un sauran mutane.

“Wannan abu ba a amince da shi ba ko kaɗan a Musulunci. Ka je ka cire wannan bidiyon kuma ka ba da haƙuri ga dukkan al’ummar Musulmi saboda baƙanta masu rai da ka yi.”

‘Yan Kannywood da dama, jarumai da mawaƙa da furodusoshi, irin su Mustapha Ahmad (Alhaji Sheshe), Jamilu Yakasai, Hafsat Idris, Aishatulhumaira, Abubakar Ibrahim (G Fresh Alameen), Adam Abdullahi Adam (Daddy Hikima), Salim Smart, Nura M. Inuwa, DJ Abba, Tijjani Asase, Auta Waziri, Umar M. Shareef, Chizo 1 Germany, da sauran su, duk sun yi tir da bidiyon waƙar. Sun yi kira ga jama’a da su daina bin shafukan Davido da Logos Olori na soshiyal midiya ko sauraren waƙoƙin su.

Davido dai ya na daga cikin mawaƙa ‘yan kudancin ƙasar nan waɗanda matasan Arewa su ke matuƙar ƙauna.

Loading

Tags: Ali NuhuDavidoKannywoodLogos OloriMusulmiSallahtirwaƙa
Previous Post

Naɗin El-Mustapha: An aje ƙwarya a gurbin ta, inji ‘yan Kannywood

Next Post

Tace finafinai: Zan yi iya ƙoƙari na don fita kunyar Kannywood da jama’ar Kano, inji El-Mustapha

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Abba El-Mustapha ya na karɓar takardar naɗa shi Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai daga hannun Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Dakta Baffa Bichi, a ranar Juma'a

Tace finafinai: Zan yi iya ƙoƙari na don fita kunyar Kannywood da jama'ar Kano, inji El-Mustapha

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!