TSOHUWAR jarumar Kannywood, Hajiya Muhibbat Abdulsalam, ta bayyana cewa idan har mace na jin daɗin aure, to da zarar an gan ta za a gane hakan. Ta ba da misali da ita kan ta.
A wani saƙo da ta wallafa a soshiyal midiya domin taya mijin ta, fitaccen daraktan nan a masana’antar finafinan Hausa, wato Hassan Giggs, murnar zagayowar ranar haihuwar sa a jiya, Muhibbat ta yabe shi, inda ta ce a gaskiya shi miji ne nagari.
A saƙon da ta rubuta da Hausa da Turanci a jiya, tsohuwar jarumar, wadda kuma darakta ce, ta kira shi da “best husband,” wato miji nagari.
Ta ce masa: “Ga ka da haƙuri da halin dattako, ga ka da mutunci. Kuma ka san mutunci daga kai na, ƙanne na, yayyi na da iyaye na. Mijin da ba ya baƙin ciki. In fact I can’t say it all on social media.

“Ba sai mata ta ce ta na jin daɗi ba, ana kallon ta an san ta na samun jin daɗi da kwanciyar hankali.
“Alhamdu lillahi, Alhamdu lillahi, Alhamdu lillahi.
“Alfarman Annabi Muhammadu sallalahu alaihi wassalam za ka gama da duniya lafiya.”
Muhibbat, wadda ‘yar kasuwa ce mai kamfanin Muhibbs da ke Kano, ta taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar sa, ta na faɗin, “HBD my lovely husband.I wish you all you always wish me, more health, more wealth, more taqwa, more patience, more imani, more blessing from all angles.
“May Aljannah be your reward, amin.”
Mujallar Fim ta fassara wannan Turancin da cewa: “Ina taya ka murnar zagayowar ranar haihuwar ka, miji na abin so na.Ina maka fatan duk alherin da kai ma ka ke mani a ko yaushe, kamar ƙarin lafiya, ƙarin arziki, ƙarin taƙawa, ƙarin haƙuri, ƙarin imani, ƙarin alheri daga kowace kusurwa.
“Allah ya saka maka da gidan Aljannah, amin.”
Ta ce ba sai ta bayyana komai da komai da Hassan ya ke yi mata ba a soshiyal midiya.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa ba wannan ba ne karo na farko da Muhibbat da Hassan Giggs su ka bayyana soyayyar su ga juna a zaman auren su. Kowannen su ya kan jaddada soyayyar sa ga ɗayan a bainar duniya, wanda abu ne da ba a saba gani ba a tsakanin ma’aurata a Nijeriya.