A DAIDAI lokacin da wasu matasa ke yin wasa da irin fasahar da Allah ya yi masu wajen aiwatar da ita ta inda ba ta kamata ba, wani jarumi a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood kuma mawaƙi a ɓangaren gambarar zamani, wato hip-hop, ya na shirin kafa tarihi a masana’antar.Jarumin, mai suna Umar Ayuba Isah, wanda aka fi sani da laƙabin Dabo Daprof (Mister Lada Goma), ya ƙware ta fannoni daban-daban da su ka haɗa da waƙa, rubutu, wasa a fim, aikin rediyo, mai shela (MC), mai shiryawa da gabatarwa, mai koyarwa, ɗan wasan barkwanci da sauran su. Mujallar Fim ta tattauna da wannan ɗan baiwa inda ya bayyana irin faɗi-tashin da ya sha a rayuwa kafin duniya ta gane irin fiƙirar da ya ke da ita.Dabo ya yi wannan hirar a lokacin da ya ke bikin zagayowar ranar haihuwar sa kuma a daidai lokacin da ya ke cika shekara 11 a Kannywood.
FIM: Menene tarihin ka a taƙaice?
DABO DAPROF: Suna na Umar Ayuba Isah, wanda duniya ta fi sani da Dabo Daprof (Mister Ladagoma). An haife ni a unguwar Sabon Gari da ke Ƙaramar Hukumar Fagge a Jihar Kano.
Na yi makarantar firamare a makarantar ‘Dabo Special Primary School’, inda daga nan ne na samu sunan Dabo. Na yi sakandare a ‘Government Secondary School Stadium’. Daga nan ne na shiga ‘Kano State Polytechnic’, inda na karanci fannin lissafi na ‘Accounting’.
Ni mawaƙi ne, marubuci ne, jarumi, ma’aikacin rediyo ne, MC ne, mai shiryawa da gabatarwa ne, mai koyarwa, ɗan barkwanci da sauran baiwa da Allah ya ba ni.
Na gaji waƙa daga gurin mahaifiya ta, kuma ita ta gada daga wajen kaka na. Na fara waƙar a situdiyo a shekarar 2010, kimanin shekaru goma sha ɗaya kenan.
FIM: Ya aka yi ka shiga harkokin fim da waƙa?
DABO DAPROF: Na shiga masana’antar nishaɗi ne ta sanadiyyar waƙar farko da na fara yi mai suna ‘Baby Girl’ ta sanadiyyar aboki na da ya nemi mu yi wa budurwar sa waƙa a wannan lokacin. Daga nan ne na fara waƙa a situdiyo gadan-gadan.
FIM: Da me ka fara, waƙa ce ko fim ko kuma rubuce-rubuce?
DABO DAPROF: Da rubutu na fara a cikin baiwa ta, kafin na fara waƙa; sai barkwanci, kuma na fara MC daga baya, sai kuma fim da sauran abubuwan da su ka biyo baya.
FIM: Zuwa yanzu adadin waƙoƙin ka nawa?
DABO DAPROF: Waƙoƙi na da na mallaka ni kaɗai guda goma sha biyu ne, na kuma yi waƙoƙi da wasu da su ka kai sama da guda ɗari da hamsin.

FIM: Finafinai nawa ka yi zuwa yanzu?
DABO DAPROF: Finafinai na guda biyar ne, wanda su ka haɗa da ‘There’s A Way’, ‘Light and Darkness’, ‘Saboda Buhari’, ‘Arewa Got Talent’ da kuma fim ɗin ‘Nabila’.
FIM: A cikin shekara 11 da ka yi a fagen nishaɗi, waɗanne nasarori ka samu?
DABO DAPROF: Nasarorin da yawa, alhamdu lillah. Kaɗan daga ciki sun haɗa da lambobin yabo sama da 25, waƙoƙi 11 sun ɗaukaka a cikin waƙoƙi 12 da na yi, sama da mawaƙa ɗari sun saka ni a cikin waƙar su, MC mafi shahara a Hausa Hip-hop, mawaƙi, marubuci da ya fi kowane mawakin Hausa Hip-hop yawan fitattun littattafai shahararru a yanar gizo, da dai sauran su.
FIM: Dole idan aka yi maganar nasara sai an faɗi ƙalubale. Shin ko wanne ƙalubale ka fuskanta?
DABO DAPROF: Ƙalubale kam akwai su, amma alhamdu lillah ba su kai nasarori ba.
Cikin ƙalubalen da mu ke fuskanta akwai rashin karɓuwa a wajen ‘yan Arewa, rashin haɗin kai a tsakanin mawaƙa, rashin tsayayyar kasuwar saida waƙa, rashin gudunmawar masoya yadda ya kamata, da dai sauran su.
FIM: Wanne abu ne ba za ka taɓa mantawa da shi ba wanda ya faru da kai a wannan masana’anta?
DABO DAPROF: Abubuwan da ba zan manta da su ba su na da yawa sosai, amma biyu a ciki su ne na farko lokacin da na ke bin motar masu saida layin waya don kawai su saka waƙoƙin mu a manyan ‘speakers’, amma yanzu ni kai na ban san adadin gidajen rediyon da su ke saka waƙoƙin na a duniya ba ma.
Na biyu shi ne ranar da na bai wa wani waƙa ta a Bata, wajen masu ‘downloading’, amma ya ce wai sai na biya shi zai karɓa, bayan kuɗi zai samu da shi. Abin ya ɗaure mani kai sosai a lokacin. Amma yanzu kam waɗanda ke cin abinci da waƙoƙi na ban san adadin su ba.
FIM: Menene burin ka a nan gaba?
DABO DAPROF: Buri na nan gaba shi ne Hausa Hip-hop ta fi haka karɓuwa a duniya, mu kuma fara tallafa wa juna sosai.
FIM: Wanne kira za ka yi ga matasa, musamman masu tasowa a wannan masana’anta?
DABO DAPROF: Shawara shi ne su dinga haƙuri, su dinga biyayya, su dinga kuma neman shawara kafin su fara abu, ba sai ta lalace ba a nemi babba.
