• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yaƙi da satar basira: Kama ‘yan ‘downloading’ ba mafita ba ce, inji hukuma

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
June 12, 2021
in Labarai
0
Yaƙi da satar basira: Kama ‘yan ‘downloading’ ba mafita ba ce, inji hukuma
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram


* Ta fito da sabon tsarin kasuwanci da kowa zai amfana

HUKUMAR Tace Finafinai ta Jihar Kano ta bayyana cewa kama masu sana’ar tura finafinan Hausa a waya ko komfuta, waɗanda ake kira ‘yan ‘downloading’, ba ita ce mafita ba wajen yaƙi da satar basira, wato ‘piracy’.

Ta ce a maimakon haka, za ta samar da wata kafa da masana’antar Kannywood za ta riƙa samun kuɗin shiga.

Wannan kuwa ita ce sayar da finafinan Hausa kai-tsaye ga ‘yan ‘downloading’ ɗin, ta yadda furodusoshi za su amfana. 
Daraktan Wallafe-wallafe (Publications) kuma mai kula da harkar ‘yan ‘downloading’ a Hukumar Tace Finafinan, Malam Idris Zakari Ya’u, shi ne ya bayyana haka a yayin wata zantawa da ya yi da mujallar Fim.

Yayin da ya ke yin ƙarin haske kan sabuwar hanyar da ake son samarwa, daraktan ya ce tare da haɗin gwiwar ƙungiyar masu rarraba finafinan Hausa, wato ‘Kannywood Distribution Network’, za a gudanar da tsarin. 

Ya yi nuni da cewa maimakon a ce ko da yaushe hukuma na bin ‘yan ‘downloading’ ta na kama su tare da kai su kotu ana cin su tara, gara ƙungiyar masu rarraba finafinai da ƙungiyar masu ‘downloading’ ɗin su zauna su san yadda za su gudu tare su tsira tare.

Ya ƙara da cewa shigo da ‘yan ‘downloading’ cikin lamarin hukumar ne kaɗai zai bada damar a shimfiɗa masu dokoki tare da ba su damar sayen finafinan da hukumar ta saki a kowane mako domin samun finafinan ba tare da sun ji shakkar wani zai zo ya kama su ba.

Malam Idris ya ce, “Mun dai cimma matsaya kan cewa ƙungiyar ‘yan ‘dowloading’ za ta riƙa sayen finafinai tare da fastoci a gun ƙungiyar ‘Kannywood Distribution Network’ domin rarraba wa ‘ya’yan ta. 

“Kuma mu na sa ran shugabannin wannan ƙungiya za su ci gaba da ba mu haɗin kai don cigaban kasuwancin su kamar yadda su ka rubuta a cikin kundin dokokin da su ka gabatar mana.”

A cewar sa, “Tun bayan shigowar Isma’il Na’abba Afakallah a matsayin mai jagorantar wannan hukuma, ya ke ƙoƙari wajen ganin an kawo daidaito ga masu sana’ar tura finafinai, wanda a baya su ke sayen finafinai su yi kwafin su a kan komfutocin su su na tura wa mutane ba tare da sun nemi izinin mai fim ɗin ba. Amma yanzu masu shirya fim ɗin da kan su su ke kawo finafinan su tare da fastoci domin a sayar wa da waɗannan mutane.”

Bayan haka, mujallar Fim ta tuntuɓi shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar ‘yan ‘downloading’ ta Jihar Kano, Malam Yakubu Yahaya, wanda ya bayyana jin ɗaɗin sa dangane da wannan al’amari da Hukumar Tace Finafinai ta bijiro da shi tare da bada tabbacin samun haɗin kan ‘ya’yan ƙungiyar a ko da yaushe kamar yadda aka nema a gare su.

Ya ce tabbas an ɗauko hanyar warware dukkan wata matsala tsakanin su da furodusoshi waɗanda a da su ke zuwa tare da jami’an tsaro su na kama su tare da komfutocin su.

Malam Yakubu ya yi kira ga sauran masu tura finafinan Hausa waɗanda ba su yi rajista da ƙungiyar ba da su hanzarta yi tare da sayen finafinai a wurin su.

Ya yi gargaɗin cewa duk wanda ya bijire wa wannan yarjejeniya, akwai tsattsauran mataki da hukuma za ta ɗauka a kan sa, ya ce “gudun kar a yi kar a soma”.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa tun bayan da kasuwancin finafinan Hausa da ake saki a faifan sidi ko dibidi ya taɓarɓare dai, masu ruwa da tsaki a Kannywood su ke ta ƙoƙarin ganin sun samar da sabbin hanyoyin samun kuɗin shiga da za su maye gurbin harkar sidi ko dibidi.

 Ana ganin bin wannan sabuwar hanyar zai taimaka wajen dawowa tare da farfaɗo da kasuwancin finafinai ta wannan ɓangaren.

Loading

Previous Post

Wuta a masaƙa: Sabon littafi kan nazarin adabin Hausa

Next Post

Dabo Daprof: Abin da ba zan manta da shi ba…

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Dabo Daprof: Abin da ba zan manta da shi ba…

Dabo Daprof: Abin da ba zan manta da shi ba...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!