
DAGA ABBA MUHAMMAD
INNA lillahi wa inna ilaihir raji’un! Allah ya yi wa darakta a Kannywood, Aminu Surajo Bono, wanda ake kira da Aminu S. Bono, rasuwa a yammacin yau Litinin, 20 ga Nuwamba, 2023.
Aminu ya rasu ba tare da ciwo ba, domin an ce yau ya fita aiki, kawai sai ya yanke jiki ya faɗi.
Za a yi jana’izar sa gobe da safe a Kano.
‘Yan fim sun kaɗu da wannan rasuwa, musamman ganin rasuwar bazata, ba ciwo ba ko haɗari.
Marigayi Aminu ya na daga cikin daraktocin da tauraron su ke haskawa, musamman a ɓangaren bada umarnin waƙa.
Allah ya jiƙan shi da rahama, amin.