BABBAR ‘yar Shugaban Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), Dakta Ali Nuhu ta kammala digirin ta a Jami’ar Skyline da ke Kano.
Fatima Ali Nuhu ta na ɗaya daga cikin ɗaliban da Jami’ar Skyline ta yaye a ranar Lahadi, 17 ga Nuwamba, 2024.
Fatima ta karanci Arts in International Relations, inda ta fito da Second Class Upper.
Mahaifin ta Ali Nuhu ya nuna farin cikin sa, inda ya wallafa hoton ta sanye da kayan yaye ɗalibai a shafukan sa na soshiyal midiya, ya kuma rubuta cewa, “We’re proud of your achievements, but even more proud of the person you’ve become. Congratulations on your graduation”.
Ma’ana, “Mu na alfahari da nasarar ki, amma kuma mu na ƙara alfahari da irin mutumiyar da ki ka zama. Barka da kammala karatun ki.”
Abokai, masoya, ‘yan’uwa da abokan sana’ar Ali Nuhu, ciki har da mujallar Fim sun taya Fatima murnar kammala karatun ta.
Allah ya sa karatun ya amfane ta da kuma al’umma baki ɗaya.