ALLAHU Akbar! A kwana, a tashi ba wuya. Shekaranjiya Litinin, 18 ga Nuwamba, 2024 mijin tsohuwar Shugabar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kaduna, Hajiya Fatima Ibrahim Ahmad (Lamaj) ya cika shekara ɗaya da rasuwa.
Wannan dalili ya sa aka gayyaci malamai daga masallatai daban-daban, inda aka yi saukar Alƙur’ani, Dala’ilu da kuma addu’o’in neman rahama a gare shi.
An yi saukar Alƙur’anin ne da safiyar ranar, a gidan ta da ke unguwar Rigachikun, Kaduna.
‘Yan’uwa, ‘ya’ya da abokan arziki duk sun halarci taron saukar Alƙur’anin da addu’o’i.
Marigayi Alhaji Ibrahim Sa’idu Gamagira (Maje), ya rasu ne a daren Asabar, 18, ga Nuwamba, 2023 a wani asibitin kuɗi mai suna Neman, a Abuja, bayan ya yi fama da jinya har na tsawon wata uku.
Haka kuma a ɓangaren abokan sana’ar ta, wasu sun halarta. Daga cikin su akwai Malam Musa Isah, Faisal Kirista, Sani Amalo, Ibrahim Daddy, A’isha B. Umar, Hadiza Madina, Sa’idu Rigachikun, El-Bash Muhammad, Ladi Paul, sai kuma wakilin Hakimin Rigachikun, Wazirin Rigachikun, Alhaji Jibril.
Allah ya jaddada rahama a gare shi.
![]()







