HARKAR fim ta na da wani abu: ta na ɗauka ta na ajewa. Da ma haka rayuwar duniya ta ke; in kai ne yau, gobe wanin ka ne.
Don haka, a masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood akwai jaruman da ke tashe a wata shekarar, a wata shekarar kuma sai ka ji shiru, ba su ba labarin su.
Akwai kuma waɗanda Allah ya tarfa wa garin su nono, ta yadda duk wani juyi da za a yi za ka same su a fagen, duniya ba ta wancakakar da su ba.
Hakan ya faru a Kannywood a cikin wannan shekara mai ƙarewa ta 2020. Mujallar Fim ta duba shin waɗanne jarumai ne tauraron su ya haska a shekarar?
Ga sunayen su maza da mata, tsofaffi da sababbi:
MAZA:-
Ali Nuhu
Adam A. Zango
Sadiq Sani Sadiq
Ado Ahmad Gidan Dabino
Sani Mu’azu
Falalu Ɗorayi
Mustapha Naburaska
Nura Ɗandolo
Ado Gwanja
Umar M. Shareef
Abdul M. Shareef
Shamsu Ɗan’iya
Nuhu Abdullahi
Ibrahim Bala
Nasiru Horo Ɗanmama
Rabi’u Rikadawa
Sulaiman Bosho
Rabi’u Ibrahim (Daushe)
Tijjani Asase
Bashir Nayaya
Aminu Mirror
Musa Maisana’a
Yusuf Sasen
Yusuf Lazio
MATA:-
Nafisa Abdullahi
Rahama Sadau
Teema Yola
Ruƙayya Dawayya
Maryam Yahya
Bilkisu Shema
Bilkisu Abdullahi
Hafsat Idris
Hauwa Ayawa
Hadiza Kabara
Hannatu Bashir
Sabira Mukhtar
Rahama MK
Surayya Aminu
Ummi Ibro
Sajida Hussain Abubakar
Aysha Humaira
Amal Umar
Khadija Kyari
Asiya Abdullahi Chairlady
Hadizan Saima
Maryam Wazeeri

Comment: iam comrd Abba m umar from maiduguri me is my fans sarki ali nuhu