KWAMITIN Amintattu (BoT) na Ƙungiyar Ƙwararru ta Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ya bada sanarwar naɗa babban furodusan nan mazaunin Abuja, Alhaji Habibu Barde Muhammad, a matsayin Shugaban Riƙo na ƙungiyar.
Kafin naɗin nasa, shi ne Mataimakin Shugaban ƙungiyar a shiyyar Arewa-ta-tsakiya.
A cikin wata sanarwa da Shugaban kwamitin amintattun, Makama Sani Mu’azu, ya bayar a yau, kwamitin ya ce naɗin nasa ya fara aiki ne ba tare da ɓata lokaci ba.
Kwamitin ya ce wannan naɗin ya biyo bayan murabus ɗin da Shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, ya yi a yau.
Kwamitin ya miƙa matuƙar godiya ga Dakta Sarari “saboda sadaukarwar sa da aiki tuƙuru ba tare da son rai ba da ya yi don haɓaka cigaban ƙungiyar na tsawon kimanin shekaru ashirin.”
Ya ce: “A zamanin mulkin sa a matsayin Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa, Dakta Sarari ya kawo yanayin yin aiki tsakani da Allah, da tsare gaskiya da kuma jawo wa ƙungiyar girmamawa a ƙasa baki ɗaya har ma da wajen ta.”
Kwamitin ya yi la’akari da cewa MOPPAN na ɗaya daga cikin ƙungiyoyi masu zaman kan su waɗanda ke da rajista kuma masu wakiltar ɗimbin jama’a a masana’antar shirya finafinai a Nijeriya, kuma ta na da membobi a cikin ƙungiyoyi daban-daban masu rassa a jihohin ƙasar nan.
“MOPPAN za ta ci gaba da sadaukar da kai ga cigaban masana’antar shirya finafinai a Nijeriya da ma harkokin nishaɗantarwa baki ɗaya,” inji kwamitin.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ruwaito cewar Dakta Sarari ya aje aikin shugabancin MOPPAN ne a wajen wani taro da manema labarai da ya yi a ofishin sa a Kano a yau.
Bai bada takamaiman dalilin sa na yin murabus ba, amma ya ce ya aje aiki ne a daidai ranar da ya cika shekaru biyu a wa’adi na biyu na shugabanci in da ba domin an yi gyara a kundin tsarin mulkin ƙungiyar ba, aka ƙara shekara ɗaya.
Ya ce ya na alfahari da irin ɗimbin nasarorin da MOPPAN ta samu a lokacin shugabancin da su ka yi, ya ce a shirye ya ke ya bayar da duk wata gudunmawa domin ƙara samun nasarori a nan gaba “saboda ni ɗan MOPPAN ne, shugabanci ne na sauka amma ina cikin ta, ni ɗan ta ne kamar yadda na ke ɗan fim harkar da na ke alfahari da ita domin ta yi mini komai a rayuwa ta.”
Sarari ya yi godiya kan haɗin kan da ‘yan ƙungiyar su ka ba shi har ya kawo zuwa wannan lokacin da ya ke bada sanarwar saukar da daga shugabancin, kuma ya nemi afuwar duk wanda ya ɓata wa rai a wajen gudanar da shugabancin.
“Ni ma na yafe wa kowa. Allah ya ƙara haɗa kan mu da masana’antar mu baki ɗaya nagode,” inji shi.