• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

by MUKHTAR YAKUBU
June 15, 2025
in Labarai
0
Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

Malam Abubakar Galadima

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN furodusa a Kannywood, Malam Abubakar Galadima, ya bayyana cewa naɗa shi jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry Powder da aka yi zai amfani masana’antar baki ɗaya, ba shi kaɗai ba.

Ya faɗi haka ne a yayin tattaunawar da ya yi da mujallar Fim kan wannan cigaba da ya samu.

Kwangilar dai ta shekara biyu ce ya samu.

An daɗe ana damawa da Abubakar a masana’antar finafinan, domin kuwa tun a 2001 kamfanin sa na ASG Movies yake shirya finafinai, wanda zuwa zuwa yanzu ya shirya finafinai da suka haɗa da ‘Alƙawari’, ‘Baɗini,’ ‘Juyin Zamani’, ‘Haƙƙin Uwa,’ ‘Bazata’, ‘Ya Kamata”, ‘Kurman Gari’, ‘Sajida’, ‘Rai Ɗaya’, ‘Sarina’, ”Yar Boko’, ‘Ƙawayen Zamani’, ‘The is the Way’, ‘Light and Darkness’, da sauran su.

Haka nan a ɓangaren tallace-tallace ya yi wa kamfanoni da dama talla waɗanda ake sakawa a cikin finafinai da kuma sauran kafafen sadarwa.

A lokacin da mujallar Fim ta ji ta bakin sa dangane da irin rawar da yake takawa a Kannywood, Abubakar ya ce: “Ita masana’antar finafinai ta Kannywood tana da girman da duk wanda ya zo da basirar sa zai samu gurbin da zai samu rabon sa, saboda masana’anta ce da Allah ya yi mata albarka ta kowanne ɓangare. Zaɓi kawai ya rage wa mutum ya zaɓi wajen da zai gwada baiwar da Allah ya ba shi domin ya samu arziki.”

Ya ƙara da cewa, “Idan ka duba, ni ina matsayin furodusa ne, a nan na fi ƙwarewa tun da na shigo harkar. Amma ka ga a cikin hakan nake samun damar da har nake yi wa wasu kamfanoni tallace-tallace.

“Duk da cewa an fi sanin jarumai da tallace-tallace a masana’antar, amma ni sai Allah ya sa na haɗa biyun har ta kai ga a wannan shekarar na samu zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry Powder.

“Wannan kuma abin alfahari ne a gare ni da ma ‘yan masana’antar finafinai ta Kannywood baki ɗaya. Don hakan ya nuna nan gaba ƙwarewar mutum za a kalla a ba shi jakadancin wani kamfani ba yawan fitowar sa a fim ba.

“Ka ga a yanzu ina matsayin furodusa ne, amma ina yin tallace-tallace na kamfanoni har ma da na gwamnatocin jiha da na tarayya, saboda ana kallon ƙwarewa ta. Don haka ina godiya ga Allah da wannan baiwa da Allah ya yi mini.”

Da muka tambaye shi ta inda masana’antar za ta ci gajiyar wannan tsarin nasa, sai ya ce, “Ai wannan abu ne da yake a bayyane, masana’antar finafinai ta Kannywood za ta ci moriyar ta, domin ka ga duk wani aiki da na samu ba ni kaɗai zan gudanar da shi ba, sai na jawo wasu da za mu haɗu mu yi aikin da su waɗanda su ma za su yi mini aiki na biya su. Kamar ɗaukar hoto, kula da waje da wasu jarumai da za mu haɗu mu yi aikin da su.

“Don haka mutane za su ci abinci ta hanyar aikin da za mu yi da su, wanda hakan zai kawo cigaba da kuma bunƙasar masana’antar.

“Wannan kuma wani abu ne da duk wani mai kishin harkar fim da masana’antar finafinai ta Kannywood zai yi murna da shi.

“Don haka a matsayi na na furodusa da yake son cigaban Kannywood, zan yi ƙoƙarin shiga sahun mutanen da suke jawo cigaban Kannywood, wanda shi ne babban burin mu a kullum.”

Daga ƙarshe, Abubakar ya yi kira ga masu harkar fim da su yi ƙoƙarin kiyaye mutuncin su day’ na harkar fim domin kawo cigaba mai ɗorewa a cikin masana’antar.

Loading

Tags: AbubakarGaladimakwangilatallaZahirSpiceCurry
Previous Post

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

Related Posts

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!