Ƙungiyar Masu Gidajen Sinima ta Nijeriya, wato ‘Cinema Exhibitors Association of Nigeria’ (CEAN), ta bayyana cewa an yi cinikin naira miliyan 471 wajen sayar da tikitin shiga sinima a faɗin ƙasar nan a watan Yuli na 2022.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Mista Ope Ajayi, shi ne ya bayyana haka a ranar Talata lokacin da ya ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Legas.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa cinikin shiga sinima shi ake kira ‘box office’ da Turanci.
Ajayi ya bayyana cewa an samu ƙarin ciniki d aka kwatanta shi da kuɗin da aka samu a watan Yuni, da kuma kuɗin da aka samu a Yulin shekarar 2021 da na 2022.
Ya ce: “An samu cinikin sinimu na N471,679,856.00 a Yuli, wanda ƙari ne na abin da abin da mu ka samu a Yuni, wato N363,274,999.00; wannan abu ne mai ƙara ƙarfin gwiwa.
“Fim ɗin ‘Thor: Love and Thunder’ shi aka fi zuwa kallo, domin ya samar da sama da kashi 54 cikin ɗari na jimillar cinikin da aka yi a Yuli sannan kashi 69 na finafinan Hollywood, yayin da ‘Ile Owo’ ne fim ɗin Nijeriya da ya fi kowanne kawo riba, domin ya samar da kimanin kashi 4 cikin ɗari na cinikin da aka yi.
“Duk da ƙarancin finafinan da aka fitar a Yuli (guda 31), idan an kwatanta su da na Yuni (41), sinimun Nijeriya sun samu cigaba wajen ciniki da kashi 30 cikin ɗari idan an kwatanta jimillar na watannin biyu.
“Sai dai kuma, idan an kwatanta cinikin Yuli na 2021 da na 2022, za a ga sinimu sun samu ƙarin kashi 5 cikin ɗari.
“Akwai alamun za a nuna manyan finafinan Nollywood a watan Agusta tare da fim ɗin ‘Bullet Train’, don haka sinimu sun hango za a samu ɗimbin ‘yan kallo a kashi na 4 na shekarar.”
Ajayi ya bayyana cewa finafinai biyar da su ka fi kawo ciniki a Yuli su ne: ‘Thor: Love and Thunder’, ‘Minions 2: The Rise of Gru’, ‘Jurassic Work: Dominion’, ‘Ile Owo’ da ‘Top Gun: Maverick’.
Ya ce finafinan da aka tsara za a nuna a gidajen sinima a Agusta su ne: ‘Runner’, ‘Bullet Train’, ‘Paws of Fury: The Legend of Hank’, ‘Cold’, ‘Akoni’, ‘Beast’, ‘The Set-Up 2’, da ‘Rubucon’.
Sauran su ne: ‘The Stranger I Know’, ‘Dragon Ball Super: Superhero’, ‘The Invitation to Hell’, ‘All or Nothng’, ‘Big Trip 2: Special Delivery’, ‘Nope’, ‘Hammer’ da ‘Obara’m’.
Comments 1