• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, April 5, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Haɗuwa ta da mutanen kirki ita ce babbar nasara ta, inji marubuciya Faridat Husaini

by MUKHTAR YAKUBU
November 14, 2024
in Marubuta
0
Haɗuwa ta da mutanen kirki ita ce babbar nasara ta, inji marubuciya Faridat Husaini

Faridat Hussaini

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
FITACCIYAR marubuciyar onlayin, Faridat Husaini, wadda a yanzu ta rikiɗe ta zama mawaƙiya, kuma ta samu karɓuwa sosai a fagen waƙar, ta bayyana wa mujallar Fim yadda ta fara rubutu da kuma nasarorin da ta samu da yadda ta samu kan ta cikin harkar waƙa:

FIM: Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatun mu.

FARIDAT HUSAIN: Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Da farko dai suna na Faridat Husain Mshelia, kuma haifaffiyar garin Suleja da ke Jihar Neja, ‘yar asalin Jihar Bornon Nijeriya. An haife ni a shekara ta 1995, yanzu haka ina da shekaru 29 cif.

Na yi makarantar firamare mai suna Shu’aibu Na’ibi Primary School inda na kammala a shekarar 2006, sannan na je Model Commercial College na samu takardar kammala sakandare. A taƙaice kenan.

Na yi aure, ina da yara guda huɗu. Kafin a aurar da ni a 2011 na fara karatun NCE ɗi na amma sanadin auren ya sa ban kammala ba, branch ɗin kwalejin da ke Suleja.

Ta fannin karatun addini kuwa na yi sauka tun ina da shekara 11, na sauke littattafai da dama. Don haka a rayuwa ta a yanzu cike take da tarin nasarori kuma babu abin da zan ce ma Allah da masoya sai godiya.

FIM: Ya aka yi kika zama marubuciyar onlayin?

FARIDAT HUSAIN: Farko dai makaranciya ce ni a farko a onlayin ɗin kafin in tsunduma cikin rubutu duk da tun kafin in fara hawa yanar gizo rubutu a jini na yake har ma na rubuta littafi biyu sai dai ban samu damar buga su ba. Zuwan onlayin da yadda na ga marubuta na bajekolin fasahar su shi ya busa mini ruhin fara yi gadan-gadan, kuma alhamdu lillahi ina farawa sai abin ya samu karɓuwa ƙwarai da aniya.

FIM: A wace shekara kika fara rubutun onlayin?

FARIDAT HUSAIN: Na fara yin rubutun onlayin a shekarar 2013. Duk da a lokacin ba a fara sani na sosai ba sai da na shiga gasar Aminiya Daily Trust a shekarar 2020 suka buga gajeren labari na a cikin littafin mai suna Sakamakon Gasar Aminiya Daily Trust. Kuma tun daga wannan lokacin nake da sha’awar buga littafi ko yau ko gobe matuƙar damar hakan ta samu, da izinin Allah da yardar sa zan buga

FIM: Wanne irin salon rubutu kika fi yin amfani da shi a rubutun ki?

FARIDAT HUSAIN: Na fi amfani da salon ciki duk da ban san salon da kake magana ba, amma ni abin da na fi mayar da hankali a kai shi ne ina rubuta abin da yake faruwa ne wanda yake ci mini tuwo a ƙwarya a cikin al’umma ta. Sannan ina amfani da lokacin da wani abu ya faru in yi rubutu a kai saboda tarihi kar ya mance gudunmawa ta.

FIM: Wane saƙo kika fi son isar wa al’umma a cikin rubutun ki?

FARIDAT HUSAIN: Babban saƙon da na fi son in isar wa al’umma a al’ummar ma mata ‘yan’uwa na shi ne mu gyara halayyar mu, musamman matan Hausawa waɗanda Allah ya sa namijin malam Bahaushe ke iya ƙoƙarin sa don ganin ya sauke haƙƙin da ya rataya a kan sa, saɓanin wasu ƙabilu. Don haka nake amfani da hikima ta don yi masu hannun-ka-mai-sanda ta hanyar hasko masu rayuwar wasu ƙabilu. Buri na dai kowane ɓangare a gyara a san aure bautar Allah ne.

FIM: A matsayin ki na marubuciyar onlayin sai kawai muka ji Faridat Husaini ta shiga harkar waƙa. Ko ya aka yi aka shiga harkar waka?

FARIDAT HUSAIN: Um! Zan iya cewa waƙar da na yi wa baba na Ado Ahmad Gidan Dabino ita ce waƙa ta farko da na yi ta jinjina. Don na rubuta ƙasidu da daman gaske, har ma na buga wasu.

Ban daɗe ina waƙa ba gaskiya duk da harkar waƙa ya so ni tun ina budurwa, na ɗan yi amshi kafin in yi aure, amma rubuta waƙa da buga tawa ta kai na a wannan shekarar ta 2024 na fara.

FIM: Wacce waƙa ce ta fito da ke aka san ki a fagen waƙa?

FARIDAT HUSAIN: Waƙar da ta fito da ni waƙar Marubuta ne wanda Al’uskun waƙa suka yi shi da Malam Abu Uthaimin da ni kai na mai suna ‘Taken Marubuta’. Duk da na yi waƙoƙi mabambanta, amma ita ce dai wacce ta sa marubuta suka san ni mawaƙiya ce bayan waƙar da na yi wa group ɗin marubuta.

Faridat Husain Mshelia

FIM: Da waƙa da rubutu a wanne mutane suka fi sanin ki?

FARIDAT HUSAIN: Mutane sun fi sani na da rubutu gaskiya. Sai dai fitar wannan waƙar da na yi ta jinjina ga baba na Ado Ahmad Gidan Dabino ta haska wa wasu sun san ni a matsayin mai waƙa.

FIM: Ko kin fuskanci wasu matsaloli a game da wannan harkar?

FARIDAT HUSAIN: Alhamdu lillahi zan ce na yi godiya ga Allah kuma zan yabi manzo na masoyi na saboda magana ta gaskiya ni ban fuskanci ƙalubale masu yawa ba. Duk da ba a rasawa amma gaskiya godiya ce tawa ga Allah. Domin ni’imomin sa a gare ni ya fi gaban kwatance don haka ba na duban ƙalubalen a matsayin tsaiko sai dai tudun da zai hayar da ni ga nasara.

FIM: Wace nasara kika samu a cikin harkar rubutun?

FARIDAT HUSAIN: Babbar nasarar da na samu a harkar rubutu, haɗuwa da mutanen kirki; wasu sun zamanto mini garkuwa, wasu ina jin su tamkar ciki ɗaya muka fito irin su Shatan Waƙa Ibrahim Jarumi duk a sanadiyyar rubutun onlayin muka haɗu, da bango na abin jinjina ta, wato baba na Ado Ahmad Gidan Dabino, da sauran ɗaruruwan mutane waɗanda ban ambata ba.Tabbas, haɗuwa da mutanen kirki ita ce babbar nasara ta a rubutu.

Nasara ta biyu kuma shi ne shiga gasanni mabambanta, ciki har da gasar BBC Hausa Hikayata inda a nan na samu satikifet na shaidar karramawa inda na yi zarra na zamto ta biyar.

FIM: Ya kike kallon kan ki a matsayin mawaƙiya a yanzu?

FARIDAT HUSAIN: To, waƙa yanzu na shige ta. Amma alamu sun nuna na shiga da ƙafar dama saboda yadda nasarori mabambanta ke tunkaro ni. Abin sai dai na yi wa Allah godiya. Don haka wannan ma babbar nasara ce samun karɓuwa cikin ƙanƙanin lokaci.

FIM: To madalla, mun gode.

FARIDAT HUSAIN: Ni ma na gode.

Loading

Tags: marubuciyamawaƙiyaRubutu
Previous Post

Hukumar Tace Finafinai ta maka Rarara a kotu

Next Post

Ban san an kai ni kotu ba, kawai a soshiyal midiya na gani, inji Rarara

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata
Marubuta

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

December 8, 2025
Next Post
Ban san an kai ni kotu ba, kawai a soshiyal midiya na gani, inji Rarara

Ban san an kai ni kotu ba, kawai a soshiyal midiya na gani, inji Rarara

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!