
Litinin, 23 ga Janairu
Allah ya azurta jarumi a Kannywood, Malam Aminu Mirror da ‘ya mace. Matar sa Malama Zulaihat ta haihu a gidan sa da ke Zariya.
Lahadi, 29 ga Janairu
Allah ya albarkaci tsohuwar jarumar Kannywood, Maryam Musa Waziri, da ɗa namiji. Maryam ta haihu a wani asibiti a Kaduna. An raɗa wa jaririn suna Muhammad (Fadeel).
Litinin, 9 Oktoba
Allah ya azurta jarumin Kannywood, Yusuf Muhammad Abdullahi (Sasen) da ɗa namiji. Ameena Zakari Yusuf ta haihu asibitin MGK, daura da asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano a birnin Kano. An raɗa wa jariri Muhammad Auwal.
Lahadi, 10 ga Disamba
Allah ya albarkaci tsohuwar jarumar Kannywood Malama Zulaihat Ɗalhat da jarumin Kannywood Shu’aibu Idris Lilisco da ‘ya mace. Zulaihat ta haihu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano. An raɗa wa jaririya Halima.