HAKIKA akwai badaƙala iri-iri a cikin masana’antar Kannywood kamar yadda Sheikh Musa Yusuf (Asadussunnah) ya bayyana a cikin wani faifan bidiyo da ya yi a kan “Illar Finafinan Hausa”. Hakika, na tabbata akwai kuma abubuwan alheri a cikin wannan masana’anta ta Kannywood duk da cewa na ga Malam ya gaza bayyana alheri ko da da ƙwayar zarra a cikin finafinan Hausa. Hakan rashin adalci ne da kawo gyara wurin sauya ba daidai ba da daidai.
Hakika, kowace irin al’umma – wala’allah masana’antar Kannywood, cikin kasuwa, ma’aikatun gwamnati ko masu zaman kan su – ba a rasa na kirki da baragurbi. Don haka babu yadda za a yi ka yi wa Kannywood kuɗin goro ka ce kowa da ke cikin ta mutumin banza ne ba tare da bambance aya da tsakuwa ba.
Akwai malaman addini da yawa da su ka taɓa yabo ko shaida irin ayyukan alheri da su ka jiɓinci adabi da ‘yan Kannywood ke gudanar da kasuwancin su tare da kafa misali da finafinan Hausa da waƙoƙi.
A cikin watan azumi na Ramadan da ya gabata, ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa, MOPPAN, reshen Jihar Kano, ta shirya taron shan ruwa da buɗa baki, inda mashahurin malamin nan, Malam Ibrahim Khalil, wanda shi ne shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, ya gabatar da lacca mai taken “Mahangar Addinin Musulunci a kan Fim: Tasirin sa a Rayuwar Ɗan’adam”. A laccar, Malam ya ambaci irin alheran da ke cikin sana’ar fim, kuma ya bayyana yadda ya kamata a gudanar da sana’ar daidai da tsarin zamantakewa da koyarwar addini. Bugu da ƙari, ya yi yabo da jinjina a kan wasu ayyukan Kannywood, wanda hakan ya ba wa masu shirya finafinai ƙwarin gwiwa su kawo gyara da samar da finafinai masu inganci da tasiri mai kyau a rayuwar ɗan’adam.
Na so a ce Malam Asadussunnah ya kira ƙasidar sa da taken “Illar Finafinan Hausa ko Tasirin su”. Hakan zai ba shi damar faɗin alheri ko sharrin da ke cikin sana’ar.
A ƙarshe, ina roƙon Sheikh Assadussunnah da ya yi mana adalci wurin kawo alherin Kannywood ko da kuwa bai taka kara ya karya ba tare da bada shawara a kan hanyoyin da za a bi a kawo gyara da cigaba wurin samar da finafinan da za su yi daidai da addinin Musulunci da ɗabi’ar Hausawa. Allah ya sa mu dace.
* TY Shaban sanannen jarumi ne, mawaƙi kuma furodusa a Kannywood